Tauraruwa Hausa News

  • Home
  • Tauraruwa Hausa News

Tauraruwa Hausa News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tauraruwa Hausa News, Media/News Company, .

Yau Shahararren Mawakin Yabon Annabi (SAW), Fadar Bege Ya Cika Shekaru Goma Da Rasuwa.Allah yajikanshi mu Kuma yasa muci...
01/07/2023

Yau Shahararren Mawakin Yabon Annabi (SAW), Fadar Bege Ya Cika Shekaru Goma Da Rasuwa.
Allah yajikanshi mu Kuma yasa mucika da Imani.

Meye sunan wannan saurayin? Akwai tukuici ga wanda ya faɗa.~Tauraruwa Hausa News ✅
30/06/2023

Meye sunan wannan saurayin? Akwai tukuici ga wanda ya faɗa.
~Tauraruwa Hausa News ✅

SHIRYE SHIRYEN BUKIN BABBAR SALLAH YA KAN K**A.Ko yauma k**ar kowace shekara Mutanen Sokoto sun dukufa wajen Sayen Dabbo...
27/06/2023

SHIRYE SHIRYEN BUKIN BABBAR SALLAH YA KAN K**A.

Ko yauma k**ar kowace shekara Mutanen Sokoto sun dukufa wajen Sayen Dabbobin layya Domin gudanar da ibadar Sallah..

Allah ya amsar Muna.

Kamfanin ne s**a dauki Nauyin kawo muku wadannan hotunan.

DA DUMI-DUMI: Bankin Duniya ya amince da Bashin Dala Miliyan 500 da Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ta nema. G...
27/06/2023

DA DUMI-DUMI: Bankin Duniya ya amince da Bashin Dala Miliyan 500 da Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ta nema.

Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta Samu amincewar bankin Duniya a Bashin Dala Miliyan 500 da ta nema.

Bankin Duniya ya ce ya lamuncewa Gwamnatin Tinubu cin wannan bashi ne domin tallafawa 'yan Najeriyaa shirinta na inganta rayuwar Mata Kuma wannan shine bashi na biyu da bankin ke amincewa sabuwar Gwamnatin.

Ana ran wannan shiri zai taimaka Wajan samawa Mata damammaki masu inganci a bangaren lilimi, Tattalin Arziki, kiwon lafiya da sauran su.

Musulmai fiye da Miliyan daya sun hau dutsen Arfa a wani mataki na cika daya daga cikin shika-shikan aikin Hajjin bana.
27/06/2023

Musulmai fiye da Miliyan daya sun hau dutsen Arfa a wani mataki na cika daya daga cikin shika-shikan aikin Hajjin bana.

Filin idi Aiki ba dare ba ranaGwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf. Abba gida-gida
27/06/2023

Filin idi Aiki ba dare ba rana
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf. Abba gida-gida

YANZU-YANZU: Mataimakin shugaban majalisar dattijai sanata barau Jibrin Maliya ya rabawa Alumma Naira Miliyan Dari da Ha...
27/06/2023

YANZU-YANZU: Mataimakin shugaban majalisar dattijai sanata barau Jibrin Maliya ya rabawa Alumma Naira Miliyan Dari da Hamsin da takwas da dari bakwai da arba'in da biyar( #158,745,000) don gabatar da hidimar sallah.

HOTO: 📸 Abubakar Ja'afar mai Hoton Barau Jibrin

ALLAHU AKBAR: Khuɗubar Annabi S.A.W Ta Ƙarshe Da Yayi Wa Al-Ummarsa A Ranar Arafat 9 Ga Watan Zul-HijjaDaga Zaharaddeen ...
27/06/2023

ALLAHU AKBAR:

Khuɗubar Annabi S.A.W Ta Ƙarshe Da Yayi Wa Al-Ummarsa A Ranar Arafat 9 Ga Watan Zul-Hijja

Daga Zaharaddeen Gandu

Annabi Muhammad S.A.W yayi khuɗubar ta ƙarshe ga al-ummarsa a ranar Arafat 9 ga watan Zhul-Hijja, yayi khuɗubar a shekara 10 bayan Hijrarsa daga Makkah zuwa Madina.

Ya gudanar da Khuɗubar a saman Dutsen Arafat, wadda wannan khuɗubar ta kasance khuɗubar ƙarshe ta Manzon Allah S.A.W, inda Fiyayyen Hallita ya cigaba da khuɗubantar ga al-ummarsa cewa;

“Ya ku mutane! Ku bani hankalinku domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka! ku saurari abin da nake gaya maku da kyau kuma ku isar da abin da zan gaya maku ga waɗanda basa wannan wuri a yau”.

“Ya ku Mutane! k**ar yadda kuka riƙi wannan Wata na Aikin Hajji da wannan rana ta Arfa, da kuma wannan gari na Makka da girma kuma abin tsarewa, to haka kuma ku riƙi ran Musulmi da dukiyoyinsu da girma abin karewa".

“Ku maida wa Mutane kayan da s**a baku Amana, kar ku cuci kowa, kar ku yi zalunci, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, haƙika Allah zai yi sakayya a kan ayukakanku, Allah (SWT) ya hana cin riba, (wato kuɗin ruwa) saboda haka duk abin da aka ƙulla ta kuɗin ruwa sai an warware shi”.

“Ku yi hattara da Shaiɗan domin kiyaye Addininku yanzu kan ya fidda ran ɓatar da ku a kan manyan abubuwa na saɓo, saboda haka ku guji bin shi a kan ƙanana”.

“Ya ku jama'a haƙiƙa kuna da haƙƙi bisa matayenku amma suma suna da haƙƙi bisa kanku, to haƙƙinsu ne a kanku da kuciyar da su sannan ku tufatar da su a kan jin ƙai. Ku bi da su kyakkyawar biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majiɓintan al-amurran ku ne kuma mataimakan ku, hakki ne a kansu da kar su yi abota da duk wanda ba ku so kuma su nisanci zina”.

“Ya ku jama'a ku yi kyakkyawan bauta ga Allah (SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, ku azumci watan Ramadan, ku bada Zakka, ku aikata Aikin Hajji in har kun sami damar yi”.

“Ku sani fa, ko wanne musulmi ɗan uwan Musulmi ne, dukkan ku dai-dai kuke da juna

Naji ɗadin sauƙata a Yola gabannin shagulgulan Sallah.Cewar tsohon mataimakin shugaban Ƙasar Najeriya. Atiku Abubakar 📸
26/06/2023

Naji ɗadin sauƙata a Yola gabannin shagulgulan Sallah.
Cewar tsohon mataimakin shugaban Ƙasar Najeriya. Atiku Abubakar 📸

Kakakin Majalisar Tarayya, Honarabul Tajudeen Abbas Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Ƙasa A Masaukinsa Dake Birnin London Na Ƙ...
26/06/2023

Kakakin Majalisar Tarayya, Honarabul Tajudeen Abbas Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Ƙasa A Masaukinsa Dake Birnin London Na Ƙasar Burtaniya

2023 Hajji: Babban malamin Addinin Musulunci As-sheikh Malam Bello Yabo a filin MinnaWane fata kuke Masa?
26/06/2023

2023 Hajji: Babban malamin Addinin Musulunci As-sheikh Malam Bello Yabo a filin Minna

Wane fata kuke Masa?

DA DUMI-DUMI: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya aminta da Sanya sunan Sheikh Usmanu Danfidiyo a filin jirgin saman kasa...
26/06/2023

DA DUMI-DUMI: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya aminta da Sanya sunan Sheikh Usmanu Danfidiyo a filin jirgin saman kasa da kasa dake Jihar Nasarawa.

Tsohuwar Ajiya: idan aka cire shekarun da wannan kuɗin yayi a duniya, shekaru nawa zai rage a cikin shekarun ka.
26/06/2023

Tsohuwar Ajiya: idan aka cire shekarun da wannan kuɗin yayi a duniya, shekaru nawa zai rage a cikin shekarun ka.

ZARGIN BATANCI GA FIYAYYEN HALITTA (SAW)Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto yayi kira ga jama'ar jihar nan da su zama mas...
26/06/2023

ZARGIN BATANCI GA FIYAYYEN HALITTA (SAW)

Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto yayi kira ga jama'ar jihar nan da su zama masu bin doka da Kuma son zaman lafiya.

Gwamnan jihar Sokoto Dr Ahmed Aliyu Sokoto yayi kira ga jama'ar jihar nan dasu ci ga gaba da zaman lafiya tare Kuma da kiyayewa da bin doka da oda.

Gwaman yayi wannan Kiran ne a wata sanarwa da Mai magana da yawun sa Abubakar Bawa ya fitar akan hari da aka Kai akan wani Usman Buda Mai Hanji da ake zargin yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.a babbar Mahautar Sokoto da safiyar Lahadi.

Gwamnan yayi kashedi ga jama'ar jihar nan akan yin duk wani yunkuri ko kalami da zai iya taba qima da darajar manzon Allah SAW, musamman ma dai a gari irin Sokoto wanda gari ne kaco kam na musulmi.

Dr Ahmed Aliyu ya Kara da cewa mutanen Sokoto nada matukar soyayya da kauna ga Annabin Rahama ta yadda ba zasu Yi wasa da taba shi ba ,akan haka ya bukaci alumma dasu mutunta manzon Allah SAW.

"Ina kira ga alummar jihar nan da mu kaucewa daukar doka a hannu,a maimakon haka s**ai rahoton duk wani laifi ko zargin batanci ga hukumomi don yin abinda ya dace"

" Addinin mu bai lamunta da mu dau doka a hannu ba don haka mu kasance masu bin koyarwar addinin "inji gwamnan.

Gwamnan ya Kuma Kara da cewa Gwamnatin sa ba zata taba daukar batun yin batanci ga fiyayyen halitta da sassauci ba,Yana Mai cewa zata tabbata an hukunta duk Wanda aka k**a da yin batanci ga fiyayyen halitta a bisa ga tanadin shara'ar musulunci.

Haka ma gwamnan ya bada tabbaci cewa a shirye gwamnatin sa take don ganin ta kare rayuka da dukiyoyin alummar ta na gari.

Gwamnan ya Kuma ja kunnen masu nemen tada zaune tsaye dasu daina Yana Mai cewa jihar Sokoto a yanzu ba wurin da za'a yiwa doka karan tsaye bane a kwashe lafiya.

Abubakar Bawa
Mai.magana da yawun gwamnan jihar Sokoto
25/06/2023

Ko Gidanmu Abba Ya Rushe Bazaimin Laifi baLaifi 1 Zemin Ya Bijirewa Umarnin Kwankwaso.~ Cewar Rabiu Nasiru Lilili Tofa
26/06/2023

Ko Gidanmu Abba Ya Rushe Bazaimin Laifi ba

Laifi 1 Zemin Ya Bijirewa Umarnin Kwankwaso.

~ Cewar Rabiu Nasiru Lilili Tofa

Gaskiyar abinda ya faru game da wannan matashin da aka kashe yau a Sokoto da sunan ya zagi fiyayyan halitta Annabi SAW.G...
26/06/2023

Gaskiyar abinda ya faru game da wannan matashin da aka kashe yau a Sokoto da sunan ya zagi fiyayyan halitta Annabi SAW.

Gardamar Aqidah ce ta kaure a tsakaninsu, sunan mutumin da aka ka*she Mal Usman, Gardama ce ta kaure a tsakaninsu akan nema ko rashin neman taimakon Annabi Muhammad (SAW). Suna cikin gardamar sai wani yace masa kada ya sake fadin ba'a neman taimako a wurin Annabi SAW sai shi kuma ya sake fadi, nan take s**a fara mishi ihun ya zagi fiyayyan halitta, duka da sauran su wanda hakan ya zamo sanadin rayuwarshi.

Wannan shine zancen gaskiya da aka mini bayani ta bangarori da dama. A lokacin da ka*she matashin duk Duniya ta dauka cewa lallai ya aikata hakan sai daga baya aka bayyana ainahin gaskiyar abunda ya faru, rikici ne na Aqidah, hisabi kuma sai a wurin Ubangiji.

Rikicin Aqidah babu irin abunda bai jawowa, har fadan kasa da kasa yana hadawa, yana daga cikin dalilan da yasa duk wani abu da ya shafi Aqidah ban cewa komai, domin ni ba malami bane ni dalibine.

Allah muna rokonka da ka kara hada kawunanmu wuri guda, ka bamu ikon bin gaskiya komin dacinta, Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

✍️ Comr Abba Sani Pantami.

DA DUMI-DUMI: Wata Babbar Kotun Tarayya Dake Zamanta A Kano ta Hana Gwamnatin Jihar Kano da Jami’anta Ruguza wasu Gine-g...
25/06/2023

DA DUMI-DUMI: Wata Babbar Kotun Tarayya Dake Zamanta A Kano ta Hana Gwamnatin Jihar Kano da Jami’anta Ruguza wasu Gine-gine dake kan Titin BUK.

Me za ku ce?

DA DUMI DUMINSA: Kwankwaso ya tabbatar Abba Kabir Yusuf zai shekara 8 a mulkin Kano
25/06/2023

DA DUMI DUMINSA: Kwankwaso ya tabbatar Abba Kabir Yusuf zai shekara 8 a mulkin Kano

Kuziyarci shafin Tauraruwa Hausa News👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎
25/06/2023

Kuziyarci shafin Tauraruwa Hausa News
👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎

TIRKASHI: Ragon da aka taya Naira miliyan guda, amma mai shi ya ce sai an ba shi Naira miliyan 1 da rabi, ya mutu haka kawai

~Tauraruwa Hausa News

TIRKASHI: Ragon da aka taya Naira miliyan guda, amma mai shi ya ce sai an ba shi Naira miliyan 1 da rabi, ya mutu haka k...
25/06/2023

TIRKASHI: Ragon da aka taya Naira miliyan guda, amma mai shi ya ce sai an ba shi Naira miliyan 1 da rabi, ya mutu haka kawai

~Tauraruwa Hausa News

Fitacciyar Jarumar Nollywood Mercy Argby wacce ta musulunta a kwanakin baya ta gabatar da aikin Hajjinta na farko a Ciki...
25/06/2023

Fitacciyar Jarumar Nollywood Mercy Argby wacce ta musulunta a kwanakin baya ta gabatar da aikin Hajjinta na farko a Cikin Musulunci. Ta zabi aci gaba da kiranta da suna Amina | Allah ya ƙarawa Annabi daraja.

Babbań Burina Shiné Na Auri Mijin Da Zai Karɓé Ni Á Yadda Nake, Nafi Son Wanda Zai So Ni Tsakani Da Allah - Indómie Ina ...
25/06/2023

Babbań Burina Shiné Na Auri Mijin Da Zai Karɓé Ni Á Yadda Nake, Nafi Son Wanda Zai So Ni Tsakani Da Allah - Indómie

Ina son wanda zai ji tausayi na, ya riƙe ni amana, koda kuwa zai min kishiya, bani da matsalar hakan, zan nuna masa soyayya fiye da wacce zai nunan, bazai taɓa yin nadamar Aure na ba, céwar Zainab Indómie.

Wanné fata zaku yi matá ?

Lafiya uwar jiki....Yadda Wani matashi ya aure mata Hudu a Rana daya kuma Suna zaune gida daya babu rikicin komai.Wani f...
25/06/2023

Lafiya uwar jiki....

Yadda Wani matashi ya aure mata Hudu a Rana daya kuma Suna zaune gida daya babu rikicin komai.

Wani fata kuke musu?

YANZU-YANZU: DAGA JIHAR SAKKWATO, GWAMNA AHMAD ALIYU YA AMINTA DA BIYAN ALBASHIN WATAN YUNI GA MA'AIKATAN JIHAR SOKOTO A...
22/06/2023

YANZU-YANZU: DAGA JIHAR SAKKWATO, GWAMNA AHMAD ALIYU YA AMINTA DA BIYAN ALBASHIN WATAN YUNI GA MA'AIKATAN JIHAR SOKOTO

A wani bangare na ganin ya cika alkawuran da yayi na biyan albashin ma'aikata akan Kari,Mai girma Gwamnan jihar Sokoto Dr Ahmed Aliyu Sokoto ya aminta da biyan albashin watan Yuni nan take ga ma'aikatan jiha da kananan hukumomi da Kuma malamai kazalika da Yan fansho.

Wannan na Kunshe ne a wata takardar bayani da sa hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto Malam Abubakar Bawa.

Sanarwar tace wannan yunkurin dai nada manufar ganin ma'aikatan jiha sun samu sukunin gudanar da sallah Babba a cikin walwala.

Gwamnan haka ma ya Kara jaddada aniyar gwamnatin sa na ganin ta kyautatawa ma'aikata tare Kuma da farfadowa da darajar aikin gwamnati.

Haka Kuma, ya bukaci ma'aikatan dasu sakawa wannan yunkurin ta hanyar zamowa masu gaskiya,tsare aiki da Kuma zuwa aiki cikin lokaci.

Alhaji Aliyu ya Kuma roki alummar jihar Sokoto dasu ci gaba da yiwa Gwamnati addua don samun nasarar biyan bukatun jama'a.

Abubakar Bawa
Sakataren Hulda da Yan jarida a fadar gwamnatin jihar Sokoto
22/06/2023

YANZU-YANZU: Anga Jinjirin Watan Babbar Sallah A Kasar Saudiya, Za'a Gudanar Da Hawan Arfah A Ranar Talata 27, Za'a Hau ...
18/06/2023

YANZU-YANZU: Anga Jinjirin Watan Babbar Sallah A Kasar Saudiya, Za'a Gudanar Da Hawan Arfah A Ranar Talata 27, Za'a Hau Idin Babbar Sallah A Ranar Laraba 28 Ga Wannan Watan.

DA DUMI-DUMI: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu yana shirye-shiryen fadar da man fetur ya dawo N100, ko N110 per Litre Kaf...
17/06/2023

DA DUMI-DUMI: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu yana shirye-shiryen fadar da man fetur ya dawo N100, ko N110 per Litre Kafin karshen watan Yuni (June) da muke ciki.

Okoronko ya shedawa Arise News cewa, Tuni Tinubu ya ba CNG Umarnin su fito da wata hanya Wanda zata kada man fetur warwas a Najeriya. Saboda shi bazai iya juran talauci da wahalun da Yan Najeriya ke ciki ba.

Tutar babu...Gwamnoni uku cikin gwamnonin Arewa wadanda sune s**ai ruwa s**ai tsaki wajen tabbatar da samun nasarar Bola...
17/06/2023

Tutar babu...

Gwamnoni uku cikin gwamnonin Arewa wadanda sune s**ai ruwa s**ai tsaki wajen tabbatar da samun nasarar Bola Tunubu,da Alamu za a shanye jar miyar amarya su Suna kofar gidan ango, masana harkokin siyasa sunyi hasashen babu Wani shiri da Gwamnati maici takeyi don ganin Ta Basu wasu manyan muk**ai acikin wannan gwamnatin,

Bayanin sirri da muka Samu dai ya nuna aiki aka Basu kuma abinyasu ladan aikinsu tun kafin suyi aikin, sannan wasu na kallon za ai musu irin abinda Bahaushe kecewa ne, ingiza mai kan turuwa!

~Tauraruwa Hausa News ✍️

DADUMI-DUMI..Young Sheikh Ya kammala Karatun Jami'a a mafi kankantar Shekaru. Fitaccen Karamin Malamin Addinin Musulunci...
17/06/2023

DADUMI-DUMI..Young Sheikh Ya kammala Karatun Jami'a a mafi kankantar Shekaru.

Fitaccen Karamin Malamin Addinin Musuluncin nan Na Afurka Zakeer M.S Ali da aka fi Sani da (Young Sheikh) ya sake kafa wani Sabon Tarihi, inda ya kammala karatu a kan Shari'a yana da karancin Shekarun da basu wuce goma sha 12 ba.

Young Shiekh dai ya Karancin Fannin Shari'a ne a wata Jami'a mai zaman kanta ta kasa da kasa dake Garin Maradin Jamhuriyar Nijar.

Wane Fata zaku masa?

Daga
Saifullahi Lawal Imam Zaria.

Wata sanarwa da ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya dakatar da Bawa ne domin ...
14/06/2023

Wata sanarwa da ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya dakatar da Bawa ne domin bayar da damar yin bincike kan wasu manyan zarge-zargen da ake yi wa shugaban hukumar ta EFCC.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/3X63EL0

LABARI: DA DUMI DUMIGwamnatin tarayya zatafara bayar da tallafin bashi ga yan makaranta acikin watan satamba na wannan s...
14/06/2023

LABARI: DA DUMI DUMI

Gwamnatin tarayya zatafara bayar da tallafin bashi ga yan makaranta acikin watan satamba na wannan shekara.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tauraruwa Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share