Hausa Trust News

  • Home
  • Hausa Trust News

Hausa Trust News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa Trust News, TV Channel, .

Wace Kujera Ku Ke Ganin Malam Nasir El-Rufai Ya Kamata Ya Nema A Zaben Shekarar 2027 Idan Allah Ya Kaimu?
22/03/2024

Wace Kujera Ku Ke Ganin Malam Nasir El-Rufai Ya Kamata Ya Nema A Zaben Shekarar 2027 Idan Allah Ya Kaimu?

Tinubu’s plan is to create 384,000 jobs in 4 years – aide  Senior Special Assistant to the President on Job Creation and...
24/02/2024

Tinubu’s plan is to create 384,000 jobs in 4 years – aide

Senior Special Assistant to the President on Job Creation and Micro Small And Medium Enterprises (MSMEs), Temitola Adekunle-Johnson, on Thursday disclosed that the administration of President Bola Tinubu will create at least, 384,000 jobs in the next four years.

Adekunle-Johnson stated this at a Communications Forum organized by his office on Job creation and MSMEs.

He said about 100,000 jobs will be created by the end of May, 2024 by the administration as it was the desire of the present government to focus on jobs creation.

“We are saying that by the end of May 29, we will create at least 100,000 jobs. The target is to create 384,000 jobs in four years,” the presidenrial aide noted.

According to him, the initiative would be a partnership between the Federal Government and Access Bank.

He said. “Today’s programme is to announce our partnership with the Access Bank, how the bank is trying to support the government with regards to access to funding for MSMEs. Right now, the interest rate for loans is between 27 and 29 per cent, but Access bank is giving us at the rate of 15 percent.”

The Presidential aide therefore thanked Access Bank for supporting businesses to thrive in the country.

Also speaking at the event, Head, non-financial Services and Emerging Businesses at Access Bank, Mrs. Chioma Ogwo said: “We are giving them affordable loans at 15 percent and free grants to deserving SMEs who have done very well.

“We have a business exchange programme for the beneficiaries that would enable the SMEs to go and exchange ideas with their counterparts in other countries. We will then learn the best from the best and come back to replicate it in Nigeria.

The Deputy Chief of Staff to the president, Ibrahim Hassan Hadejia, in his remark said MSMEs provide resilience and agility to any economy.

Also present at the event were the Minister of Communications, Innovation and Digital Economy, Mr Bosun Tijjani; the SSA to the President on Digital Media and Emergency Management, Hon. Ahmed Ningi; DG of SMEDAN, Mr Charles Odii; the DG of VON, Mallam Jibrin Ndace who represented the Minister of Information, and the representative of the Registrar General of the CAC, among others.

Dan Shugaba Tinubu, Sheyi Kenan A Yayin Da Yake Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Mabukata Da Kansa
24/02/2024

Dan Shugaba Tinubu, Sheyi Kenan A Yayin Da Yake Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Mabukata Da Kansa

Da Dumi-dumi: Gwamnan Katsina Dikko Radda ya kafa dokar hana boye kayan abinci a jiharMai Girma Gwamnan jihar Katsina Ma...
16/02/2024

Da Dumi-dumi: Gwamnan Katsina Dikko Radda ya kafa dokar hana boye kayan abinci a jihar

Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya saka hannu kan dokar da za ta hana mutane boye kayan abinci.

Kafa wannan doka na nufin hana wasu 'yan kasuwa da ake zargi da boye kayan abinci a rumbuna daban-daban don kayan abincin su yi tsada.

Kazalika Gwamnan ya kafa wani kwamiti na musamman da za a dora wa alhakin bi lungu da sako na jihar don zakulo mutanen da suke boye kayan abinci.

Dokar ta haramta duk wani yunkuri na boye kayan abinci a duk fadin jihar. Kazalika, dokar ta lissafta kayan abinci da s**a hada da shinkafa, masara, gero, dawa, waken suya, gyada da ma duk wani nau'in kayan abincin da karancinsa zai jefa al'ummar jihar Katsina cikin halin ha'ula'i.

Bugu da kari, wannan doka ta fayyace karara cewa duk mutumi ko kamfanin da aka samu da laifin boye kayan masarufi, to ya saba dokar da za a iya hukunta shi karkashin sashe na 114 a kundin penal code.

Sannan hatta wurin da aka k**a cewa ana boye wadannan kayan abinci, za a barke shi a fitar da abincin don sayar wa al'umma a farashin da ya dace.

Ta bangaren kwamitin karta-kwana na task force da Gwamnan ya kafa kan wannan batu kuwa, an dora masa alhakin zakulo masu boye kayan masarufin a cikin jihar.

Bugu da kari, an kwamitin zai hada da jami'an tsaro don su kamo tare da gurfanar da wadanda aka samu da laifin. Kazalika, kwamitin zai gana da masu ruwa da tsaki kan harkar kayan masarufi a jihar don gudun kitso da kwarkwata.

Sannan wannan kwamitin zai rika kula da yadda ake safarar kayan abincin, daga sassan jihar daban-daban da ma tsallakawa da shi kasashen waje.

Ana kyautata zaton kwamitin zai kunshi shugaba da karin mambobi 10 da za su gudanar da wannan aiki.

Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD ya rarraba hannu kan wannan doka a ranar Juma'ar nan 16 ga watan Fabrairun, 2024.

Isah Miqdad
SSA Digital Media for Chief Press Secretary
16/2/2024

LABARI: Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya gwangwaje Ma'aikaciyar sa Aisha Humaira D...
16/02/2024

LABARI: Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya gwangwaje Ma'aikaciyar sa Aisha Humaira Da Kyautar Dalleliyar mota.

Masu karatu mai zaku ce?

Da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Ƙara Kuɗin Man Fetur Na Yi Murna, Ko Dan Masu Kawo Man Ziyara A Daura Za Su Ragu, Amma D...
01/01/2024

Da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Ƙara Kuɗin Man Fetur Na Yi Murna, Ko Dan Masu Kawo Man Ziyara A Daura Za Su Ragu, Amma Duk Da Haka Sai Su Haɗa Kuɗin Mota Su Zo, Cewar Tsohan Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari

DA ƊUMI-ƊUMI: Manyan Alarammomi sun taru a Kano don roƙa wa Nasiru Gawuna nasara a Kotun Koli. Mene ne ra'ayoyinku?
27/12/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Manyan Alarammomi sun taru a Kano don roƙa wa Nasiru Gawuna nasara a Kotun Koli.

Mene ne ra'ayoyinku?

Jagoran Jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Tare Da Wasu Daga Cikin Ƴaƴansa
26/12/2023

Jagoran Jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Tare Da Wasu Daga Cikin Ƴaƴansa

RAININ WAYO: Ba Wai Sace Ta Na Yi Ba, Na Je Gwada Lafiyarta Ne Daga Abuja Zuwa Delta, Cewar Matashin Da Aka Zarga Da Sac...
22/07/2023

RAININ WAYO: Ba Wai Sace Ta Na Yi Ba, Na Je Gwada Lafiyarta Ne Daga Abuja Zuwa Delta, Cewar Matashin Da Aka Zarga Da Sace Wata Mota Ta Kimanin Naira Milyan 55 A Abuja

YANZU YANZU : Majalissar Wakilan Najeriya ta Amince da Batuñ karin kudin Man Fetur .
19/07/2023

YANZU YANZU : Majalissar Wakilan Najeriya ta Amince da Batuñ karin kudin Man Fetur .

Gwamnatin Kano ta Nada Abba El-mustapha Shugaban Hukumar tace Fina-finan Kannywood .Wane Fata zaku masa ?
19/07/2023

Gwamnatin Kano ta Nada Abba El-mustapha Shugaban Hukumar tace Fina-finan Kannywood .

Wane Fata zaku masa ?

Ba Mu Da Hannu A Kara Farashin Man Fetur, 'Yan Kasuwa Ne S**a Kara Daga Naira 540 Zuwa 617, Cewar Kamfanin NNPC, Ta Baki...
18/07/2023

Ba Mu Da Hannu A Kara Farashin Man Fetur, 'Yan Kasuwa Ne S**a Kara Daga Naira 540 Zuwa 617, Cewar Kamfanin NNPC, Ta Bakin Mele Kyari

Uwar Gidan  Gwamnan Jahar Katsina Dr. Zulaiha Dikko Umar Radda, First Lady tasamu halarta taro da akai yau tareda matar ...
18/07/2023

Uwar Gidan Gwamnan Jahar Katsina Dr. Zulaiha Dikko Umar Radda, First Lady tasamu halarta taro da akai yau tareda matar Shugaban kasar Nigeria Sen Oluremi Tinubu da Nana Kashim Shettima matar mataimakin Shugaban kasar Nigeria da sauran matan gwamnoni, wajen taron National women Development Center da kaddamar da hotan matar Shugaban kasa a hukumar ta mata da chigabansu ta kasa dake Birnin Tarayya Abuja .

Mal Abdul Danja

Kyari Ya Maye Gurbin Adamu A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC Na KasaMataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa shiyyar Ar...
17/07/2023

Kyari Ya Maye Gurbin Adamu A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya zama shugaban rikon jam’iyyar APC na kasa.

Hakan ya biyo bayan murabus din da Sanata Abdullahi Adamu ya yi a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada, idan shugaban jam’iyyar na kasa ya yi murabus, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga shiyya ne zai karbi ragamar mulki.

Kyari ya jagoranci wasu mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) zuwa wani taro da ke gudanarwa a halin yanzu a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja cikin tsauraran matakan tsaro.

Wadanda s**a shiga taron da Kyari sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa Jam’iyyar daga yankin Kudu, Emma Enukwu da takwaransa na yankin Arewa Maso Yamma, Salihu Lukman da Kuma Mataimakin Shugaban Kasa na shiyyar Arewa Maso Gabas, Salihu Mustapha da takwaransa na Arewa Ta Tsakiya, Muazu BawaBawa da Mataimakin shugaban na Kudu maso Yamma, Issacs Kekemeke da Mataimakin shugaban na kudu maso gabas , Ejoroma Arodiogu da mataimakin sakataren Jam’iyyar na kasa, Barr. Festus Fuanter.

Gwàmnañ Jàhar Borno zulum Ya rabawa Mutane samà dà Dubu 13 kàyàñ Abinci domiñ Ràge Radadi a karamar hukumàr Goza.Wañe Fà...
17/07/2023

Gwàmnañ Jàhar Borno zulum Ya rabawa Mutane samà dà Dubu 13 kàyàñ Abinci domiñ Ràge Radadi a karamar hukumàr Goza.

Wañe Fàta kuke Masà ?

Mark Zuckerberg Na Ci Gaba Da Ɗaukar Horo A Wajen Israel Adesanya Don Fafata Dambe Da Mamallakin Twitter, Elon Musk.Ya K...
16/07/2023

Mark Zuckerberg Na Ci Gaba Da Ɗaukar Horo A Wajen Israel Adesanya Don Fafata Dambe Da Mamallakin Twitter, Elon Musk.

Ya Ku Ke Ganin Damben Na Su Zai Kasance?

Duk Cin kaina Na hadu dà Babànà inji Shagiri Girbau Lokacin daya Hadu da Ale Rufa'i Mai Kudin Duniya .
16/07/2023

Duk Cin kaina Na hadu dà Babànà inji Shagiri Girbau Lokacin daya Hadu da Ale Rufa'i Mai Kudin Duniya .

Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'uunYanzu-Yanzun nan, Allah ya yiwa Matar Alhaji Dahiru Mangal Hajiya Aisha rasuwa .Ta ra...
15/07/2023

Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'uun

Yanzu-Yanzun nan, Allah ya yiwa Matar Alhaji Dahiru Mangal Hajiya Aisha rasuwa .

Ta rasu ne a Abuja, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Za'a yi jana'izar ta idan Allah ya kaimu gobe da misalin ƙarfe 11am na safe.

Allah yajikan ta, ya gafarta mata, yasa Aljanna ce makomar ta. Ameen

Yadda Babban Attajirin Nan Ale Rufa'i Yake Sharholiya da Lemun kwalba kirar Coca-Kola Bayan Ya Sayi Jahar Kano da Jahar ...
15/07/2023

Yadda Babban Attajirin Nan Ale Rufa'i Yake Sharholiya da Lemun kwalba kirar Coca-Kola Bayan Ya Sayi Jahar Kano da Jahar Kaduna ..

Me zakuce ?

Shahàrarren Malamin Addini kuma Babban Limamin Masallacin Abuja Farfesa Shaick Maqari a Harabar Masallacin Manzon Allah ...
14/07/2023

Shahàrarren Malamin Addini kuma Babban Limamin Masallacin Abuja Farfesa Shaick Maqari a Harabar Masallacin Manzon Allah S.A.W .

Wane Fata Kuke Masa?

Yadda Wani matashi Dan Jahar Born0 Ya kera Jirgin sama , Motoci.  Masallacin Ka'aba  , Plaza da Sauran Ababen More Rayuw...
12/07/2023

Yadda Wani matashi Dan Jahar Born0 Ya kera Jirgin sama , Motoci. Masallacin Ka'aba , Plaza da Sauran Ababen More Rayuwa .

Wane Fata kuke masa ?

Ka Taba Jin Kasar 🇱🇺 Luxembourg?1. Kasa ce karama a tsakiyar turai. Tana gewaye da kasashen 🇫🇷 France, 🇩🇪 Germany da kum...
12/07/2023

Ka Taba Jin Kasar 🇱🇺 Luxembourg?

1. Kasa ce karama a tsakiyar turai. Tana gewaye da kasashen 🇫🇷 France, 🇩🇪 Germany da kuma 🇧🇪 Belgium.

2. Yaren kasar guda 3 ne; German, French da Luxembourgish.

3. Kasa ce yar karama, tana cikin mafi kananan kasashe a duniya. Girman kasar 2,586 Sqkm. Kenan Gombe da Kano sun ninka kasar sau 7.

4. Jami'o'i 2 ne kacal a kasar, daga jami'ar University of Luxembourg sai kuma Sacred Heart University.

5. Taken kasar shi ne "mir wëlle bleiwe wat mir sinn", ma'ana haka mu ke son mu ganmu.

6. Gaba daya mutanen kasar mutum 626,108 ne, babban birnin kasar wato Luxembourg City na dauke da mutane 120,000

7. Saboda daɗaɗɗun abubuwan tarihin kasar, UNESCO ta sanya Luxembourg daya daga cikin guraren ziyara na tarihi a duniya. Akwai samada gidajen sarauta (castle) 100 a kasar, akwai hanyoyin karkashin kasa (underground tunnel) wadanda s**a zamo mafaka a lokacin yakin duniya na 2, wanda zai iya daukan samada mutane 30,000

8. Itace kasar da kadai a duniya wacce ba a karbar kudin abin hawa (transport). Da bus, da jirgin kasa, duk wanda ka hau, za su kaika duk inda ka ke so a kasar a kyauta.

9. Luxembourg ta fi kowace kasa a turai girman mafi karancin albashi. Mafi karancin albashin kasar shi ne yuro £2,141.99 daidai da kudin Nigeria ₦1,859,822.76 (miliyan daya da dubu dari takwas......) a wata.

10. Ita tafi kowace kasa yawan masu motoci. A cikin kowane mutum 1,000, mutum 681 sunada mota a kasar.

11. Itace kasa ta mafi arziki a duniya.

12. Daya daga cikin kasashen da s**a fi ko'ina zaman lafiya. Yan sandan kasar gaba daya su 1,300 ne, gidajen yari kuwa 2 kacal.

13. Kusan kashi 60 cikin 100 na mazauna kasar ba asalin yan kasar ba ne, duk baki ne daga wasu kasashe.

14. Kasa ce mai dauke da duwatsu manya, dazuka (forest) da guraren tarihi da tsofin gidajen sarauta.

✍️ Abu Albani Auwal Ahmad

Jagorañ jam'iyyar Mai Kwando Injiniya Rabi'u Kwankwaso tare da Malam Bello Yabo .Wane Fata Kuke Masu ?
11/07/2023

Jagorañ jam'iyyar Mai Kwando Injiniya Rabi'u Kwankwaso tare da Malam Bello Yabo .

Wane Fata Kuke Masu ?

A bakin Haramin Makka muka taba haduwa da yaronnan Haifaffen Makka ne amma asalinsa daga Sudan suke, Muna magana, naje C...
11/07/2023

A bakin Haramin Makka muka taba haduwa da yaronnan Haifaffen Makka ne amma asalinsa daga Sudan suke, Muna magana, naje Ciro wayata daga Aljihu sai wadannan kudin s**a fado sai yace Menene wanna nace kudin mu ne na Nigeria, sai yace na bashi ya dauke su hoto sun masa kyau, sai nace Idan YA GAMA HOTON YAJE DASU YA AJJIYE DON TARIHI😀

Allah Ka taimaki Nigeria 🇳🇬

~ Ismail Shettima

DA DUMIDUMI: Gwamna Zulum Ya haramta Sana'ar Jari Bola a BornO .Me zaku ce ?
11/07/2023

DA DUMIDUMI: Gwamna Zulum Ya haramta Sana'ar Jari Bola a BornO .

Me zaku ce ?

Ƙasa Da Kwana 40, Gwamnan Neja Ya Raba Wa Ƴan Sanda Motocin Aiki 20A kokarinsa na daƙile matsalar Tsaro, gwamnan jihar N...
11/07/2023

Ƙasa Da Kwana 40, Gwamnan Neja Ya Raba Wa Ƴan Sanda Motocin Aiki 20

A kokarinsa na daƙile matsalar Tsaro, gwamnan jihar Neja, Alhaji Umaru Muhammadu Bago ya raba wa jami'in yan sandan jihar motocin aiki guda ashirin domin samun sukunin gudanar da aikinsu, musamman yankunan da ake fama da matsalar, jiya Litinin..

Gwamnan Jihar, Honarabul Umaru Muhammadu Bago ya ba da umurni ga duk jami'an tsaro da ke aiki a jihar, da su kakkabe duk wasu ɓata-gari musamman waɗanda dake cikin birnin Minna kuma su rushe duk wani gida ko muɓuyarsu ko wani gini da masu safarar miyagun kwayoyi ke amfani da shi.

Daga Jamilu Dabawa

Jarumar Kannywood , Momee Gombe ta saki zafafan Hotunan Murnar Zagayowar Haihuwarta .Wane Fata zaku Mata ?
11/07/2023

Jarumar Kannywood , Momee Gombe ta saki zafafan Hotunan Murnar Zagayowar Haihuwarta .

Wane Fata zaku Mata ?

Bazan Gudu Ko Ina ba Ina nan zaune Daram a Daura - Inji Tsohon Shugaban kasa Buhari .
10/07/2023

Bazan Gudu Ko Ina ba Ina nan zaune Daram a Daura - Inji Tsohon Shugaban kasa Buhari .

Ni Ba Musulma Ba Ce, Shauƙin Soyayar Da Musulmai Suke Yiwa Annabinsu Ya Birgeni, Shi Yasa Na Rera Masa Waka, Cewar Sarah...
10/07/2023

Ni Ba Musulma Ba Ce, Shauƙin Soyayar Da Musulmai Suke Yiwa Annabinsu Ya Birgeni, Shi Yasa Na Rera Masa Waka, Cewar Sarah Aloysius Ta Cikin Shirin Fim Ɗin Daɗin Kowa

Masu karatu wanne fata kuke da shi ga Sarah da ta rerawa shugaban halitta Annabi Muhammadu S.A.W waƙa, duba da ita ba musulma ba ce?

~ IDON MIKIYA

Yau Shekara 42 Cif Da Kisan Dakta Bala Muhammad A KanoDaga Saliadeen SiceyKisan Dr Bala Muhammad (Mijin Hajiya Naja’atu ...
10/07/2023

Yau Shekara 42 Cif Da Kisan Dakta Bala Muhammad A Kano

Daga Saliadeen Sicey

Kisan Dr Bala Muhammad (Mijin Hajiya Naja’atu Muhammad) Wanda A Ka Kashe A Tarzomar Siyasa a Ranar Juma'a 10 ga Yuli, 1981.

A rana irin ta yau 10 ga watan Yuli 1981 aka kashe Dr Bala Muhammad mai baiwa Gwamna jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi shawara akan harkokin siyasa.

Rikici Tsakanin Marigayi Sarki Ado Bayero da marigayi Gwamna Abubakar Rimi Ya kai ga sanadiyar kisan gillar da aka yiwa Dr. Bala Mohammed, matashin malami, mai kishin kasa, mai hangen nesa, mai bege da buri na samar da al'umma mai adalci da daidaito

Ya rasu yana da shekaru 35 a duniya kuma har zuwa lokacin da aka kashe shi ya kasance mai baiwa marigayi Gwamna Abubakar Rimi shawara kan harkokin siyasa na jihar Kano tsawon watanni tara.

An yi masa kisan gilla da wuta. Yayin da yake cikin aiki a ofishinsa, maharan marasa tsoron Allah sun banka masa wuta Da sauran abubuwan da ke cikin ofishin.

Marigayi Abubakar Rimi ya yi karin haske game da dalilin da ya sa aka kashe Dr Bala. In ji shi: "Abubuwan da s**a faru a ranar Juma'a 10 ga Yuli abin takaici ne k**ar yadda muke bakin ciki.
Amma al’amura ne da ya k**ata a yi tsammani a duk wata fafutuka da za a yi tsakanin dakarun ci gaba da masu mayar da Hannu Agogo Baya a kasar nan da ko’ina.”

A Lokacin Tarzomar ta 10 Ga Watan Yuli 1981 An Kona Majalisar Dokokin Ta Kano A Lokacin ta na hasiya Bayero Dafda kofar kudu, An Kona Gidan Rediyon Kano.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Trust News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share