04/06/2023
LABARIN WADANSU MADINKA GUDA UKU
Daga littafin Magana Jari Ce 2
Na Alhaji Abubakar Imam
A wata kasa an yi wadansu madinka guda uku, ba a taba ganin inda s**a sayi zawwatin da su ke dinkawa ba, har mutane suna zaton sautu su ke yi a wata kasa ana kawo masu. Wadansu s**a ce watakila aljannu ke gare su masu ba su zawwati.
Ashe duk ba haka ba ne. Su yadda su ke yi, kullum da tsakad dare sai su gamu, su dauki hanyoyi su nufi hurumin garin, watau inda a ke rufe mutane, su yi ta hake sababbin kaburbura suna zare likkafanin daga jikin matattu, sai su zo gida su rika dinka 'yan taguwoyi da wanduna suna sayarwa.
Al'adar kasan nan kuwa, idan mai zarafi ya mutu sai su sa masa kayansa duk, su haka babban rami su sa shi a ciki, su dauko dutse mai girma su rufe bakin.
Ana nan sai Wazirin garin ya mutu, aka tafi hurumi aka haka masa katon kabari, aka shimfide wurin da kilisai da barguna da katifai. Da aka gama aka dauko Waziri, aka sa masa kufta da jabba da wando mai zina, aka yafa masa alkyabba. Da ka gan shi sai ka yi zaton in an ce masa, "Ranka ya dade" zai ce "Mhm." Aka kawo wani zobe na zinariya aka sa masa a hannu, aka kai shi kabarin nan aka ajiye, aka nemo wani jibgegen dutse aka rufe bakin.
Kafa na daukewa sai madinkan nan su uku s**a taho wurin kabarin, don su sace abin da ke ciki. Amma su duk abin da s**a fi bukata cikin kayan nan shi ne zoben nan na zinariya, don ko shi kadai ma ya iya sayen duk abin da ke cikin kabarin.
Da zuwansu s**a yi dako-dako a bakin ramin, suna shawarar wanda zai shiga ya miko kayan. Kowa aka lalabo sai ya ki, ya ce dan uwan ya shiga. Babbansu ya ce karamin ya k**ata ya shiga. Karamin ya ce, "A'a, ai wannan irin wuri sai ku manya."
S**a yi ta jayayya haka, har dai karamin ya yi ta maza ya ce ya shiga, a bude, ai mai rabon ganin badi sai ya gani. Da s**a bude zai shiga sai mabi masa ya ce, "In ka dauko zoben nan fa ka lura kada ya sumbule maka." Ya juyo, ya ce, "Ina ruwanka, ko ya sumbule mini, ko kada ya sumbule mini, kai dai ba tsoro