Standard Radio and Television-SRTV

  • Home
  • Standard Radio and Television-SRTV

Standard Radio and Television-SRTV SRTV - The Voice of the Voiceless

02/03/2022

Special interview

Cike da kima, izza, girmamawa da karamci, an birne mace ta farko matukiyar jirgin yaki a Najeriya, Tolulope Arotile.
23/07/2020

Cike da kima, izza, girmamawa da karamci, an birne mace ta farko matukiyar jirgin yaki a Najeriya, Tolulope Arotile.

Gwamna Masari ya fasa kwai, ya bayyana masu daukar nauyin 'yan bindiga.Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari.Gwamnan jihar K...
22/07/2020

Gwamna Masari ya fasa kwai, ya bayyana masu daukar nauyin 'yan bindiga.

Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya danganta hauhawar miyagun ayyukan 'yan bindiga da gagarar 'yan ta'addan Boko Haram da ke addabar arewa da 'yan siyasa masu son takara a 2023.

Wannan na zuwa ne bayan da 'yan bindiga a jihar Zamfara s**a mika bindigogi 50 a makon da ya gabata don amincewa da karbar shanu biyu da gwamnan ya ce zai bada ga duk wanda ya kawo bindiga daya.

Gwamnan ya ce, wadannan 'yan siyasar sun yadda cewa ta hanyar daukar nauyin 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda ne kawai za su iya bata wa mulkin Buhari suna don samun damar mulkar kasar nan a gaba.

Masari, wanda ya yi wannan jawabin a jiya tare da shugabannin guduma da kananan hukumomi na APC, ya ce da yawa daga cikin 'yan bindigar da 'yan Boko Haram da ke kai hari a kasar nan na bin umarnin wasu 'yan siyasa ne.

"Da yawa daga cikin hare-haren 'yan bindiga da Boko Haram da yankin arewaci ke fuskanta, duk wasu 'yan siyasa kuma makiyan gwamnatin APC suke daukar nauyi a matakin tarayya da jiha.

"A zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ana samun tashin bama-bamai a Maiduguri, Kano da Abuja.

Akwai lokacin da bam ya tashi a Kano inda ya kashe fiye da mutum 500. Masallatai, majami'u da tituna duk an rufesu saboda rashin tsaro. Amma yanzu, Ubangiji ya tsaremu daga irin wannan rashin tsaron amma duk mun manta.

"A yau, 'yan siyasar da ke da burin tsayawa takara ne ke daukar nauyin 'yan bindiga. Daga yadda s**a kware a amfani da bindiga da kuma yadda suke kaiwa sojoji hari, za mu gane cewa akwai wata a kasa.

"Suna cewa mun kori PDP saboda rashin tsaro, a don haka ne suke son yin amfani da rashin tsaron don korar APC. Saboda haka ne yak**ata mu APC mu bude idanunmu," yace.

Ya yi bayanin cewa dakarun sojin da sauran jami'an tsaro suna matukar kokari wurin ganin bayan ta'addanci. Ya ce babbar matsalar shine yadda sauran masu ruwa da tsaki s**a kasa basu tallafi don yakar al'amarin.

Ya ce idan sauran masu ruwa da tsaki za su yi rabin kokarin da dakarun soji ke yi, tabbas Najeriya za ta yi nasarar kawo karshen ta'addanci.

JIGAWA GOVT HAS BEGAN THE DISTRIBUTION OF GRAINS ACROSS THE STATE Jigawa state government has received one hundred and t...
22/07/2020

JIGAWA GOVT HAS BEGAN THE DISTRIBUTION OF GRAINS ACROSS THE STATE

Jigawa state government has received one hundred and ten Trucks of Grains out of the one hundred and fifty allocated to the state as covid-19 palliative by the federal government.

Governor Muhammad Badaru Abubakar announced this today while briefing newsmen at the government House Dutse.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar explained that each poling unit will receive one ton of the commodity for onward distribution to the people.

The governor further said government has already received an alert of one billion naira as part of the federal government palliative donation.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar announced that, another consignment of grains was also received from coalition of private sector to lessen the effects of the pandemic against covid-19.

Governor Muhammad Badaru thanks Almighty Allah and other stakeholders for witnessing a decline in covid-19 active cases in the state.

He therefore expressed appreciation to the people of the state for embracing covid-19 protocols and hoped to maintain the tempo.

******************************************

JIGAWA GOVT HAS BEGAN THE DISTRIBUTION OF GRAINS ACROSS THE STATE

Gwamnatin jihar jigawa ta karbi kayan abinci tirela dari da goma daga cikin tirela dari da hamsin da gwamnatin tarayya ta bayar gudummawa domin rage radadin cutar corona virus.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka lokacin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati.
Wakilinmu na gidan gwamnati, Sani Muhammad Gumel nada cigaban wannan rahoto.

Ya ce tuni aka fara kai kayan akwatunan zabe, inda kowace akwati zata sami tan daya da za a raba ga mutane dari.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya ce mutane dubu dari uku da hamsin da takwas ne zasu amfana da tallafin a fadin jihar nan.

Daga nan ya yi bayanin cewa akwai wasu karin kayayyakin masarufi da kungiyar manyan yan kasuwa ta kasa ta bayar gudummawa wanda shima za a yi amfani da tsarin akwatuna wajen raba shi bayan sun kaddamar, kafin karshen wannan watan.

Auwal D Sankara (F**A)
Senior Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media (Babban Mataimaki na Musamman Ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafan sadarwa)

20/07/2020

Hon Hamidu Sajo Lekki mai wakiltar mazabar yola ta arewa a jihar adamawa
- ke jawabin ayyukan cigaba daa samar a mazabarsa k**a daga lokacin da ya shigo office izuwa yau.

Allah jikan Alhaji Adamu Muazu Modibbo, fitaccen Dan Siyaya a Adamawa. "Indeed, death is inevitable to every mortal".
19/07/2020

Allah jikan Alhaji Adamu Muazu Modibbo, fitaccen Dan Siyaya a Adamawa. "Indeed, death is inevitable to every mortal".

Mahaifin da yayiwa 'yar sa ciki a Yobe yace,yayi hakan ne sabi da, tanason bibiyar maza
18/07/2020

Mahaifin da yayiwa 'yar sa ciki a Yobe yace,yayi hakan ne sabi da, tanason bibiyar maza

14/07/2020

14, July 2020.

13, Yuli 2020Gwamnatin jihar Jigawa karkashin gwamna Badaru Abubakar, ta bayyana kudirinta na shuka bishoyoyi miliyan 2....
14/07/2020

13, Yuli 2020

Gwamnatin jihar Jigawa karkashin gwamna Badaru Abubakar, ta bayyana kudirinta na shuka bishoyoyi miliyan 2.5 a fadin jihar.

13th Yuli, 2020Gwamnatin Zamfara ta baiwa JIBWIS gudunmawar naira miliyan 100 domin gina jami'a a shinkafi. Daga Ibrahim...
14/07/2020

13th Yuli, 2020

Gwamnatin Zamfara ta baiwa JIBWIS gudunmawar naira miliyan 100 domin gina jami'a a shinkafi.

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun, ya baiwa kungiyar JIBWIS gudunmawar Naira miliyan Dari (₦100,000,000.00) domin fara gudanar da jami'ar musulunci da kungiyar take shirin gudanarwa a garin shinkafin jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle yace "wannan jami'a da kungiyar JIBWIS take shirin farawa a jihar mu namu ne gaba daya, kuma zamuyi iya yinmu domin ganin harkar ilimi ya farfado, musamman a jihar Zamfara"
Gwamnan a cewarsa, wannan gudunmawa da ya bada, somin tabi ne, zai kuma kara badawa nan gaba domin ganin jami'ar ta tsaya akan kafafuwan ta.

Tun farko a bayanansa, Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yace mun shigo jihar Zamfara ne domin nunawa majalisar koli ta JIBWIS makarantar, wanda tsohon gwamnan Jihar Sokoto ya bamu, tare da kokarin kammala ta a cikin watanni shida, daga nan kuma muka wuce Gusau domin mu shaidawa gwamnan cewa zamu yi jami'a a jihar sa, wanda hakan ya bashi sha'awa har ya bada wannan gudunmawar nan take.

Allah ya bada ikon kammalawa.
....Babu shakka wannan lamari daga Allah ne.

Update
13/07/2020

Update

13/07/2020

Sakon so!!

Update on covid19 13th July 2020.
13/07/2020

Update on covid19 13th July 2020.

13/07/2020

Sambisa!!

13/07/2020
The Voice of the Voiceless!!!
13/07/2020

The Voice of the Voiceless!!!

Address


Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 06:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Standard Radio and Television-SRTV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Standard Radio and Television-SRTV:

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Opening Hours
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share