Madugu TV

Madugu TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Madugu TV, .

15/09/2023

Inda akaci Karo da wani baban al'ari. Wani malami mai ikirarin yana addini yayi hakika da kare a jahar kaduna, karamar hukumar chukun

13/09/2023

Orientation from mass comm kaduna polytechnic

13/09/2023

MSSN ORIENTATION FROM MASS COMM DEPARTMENT KADPOLY

13/09/2023
Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un.Allah ya jikan ...
06/09/2023

Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un.

Allah ya jikan malan da Rahama. Allah ya amsa bakuncin Ameen.

04/09/2023

Maganar gsky yan kasuwa kuji tsoran Allah.

Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un wannan yaro antsince shi ne a karkashin gadah bridge dake makarfi road  kaduna. Alamu...
02/09/2023

Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un wannan yaro antsince shi ne a karkashin gadah bridge dake makarfi road kaduna. Alamu sun nuna cewa ancire wani bangare na jikin shi.

Allah ya jikan shi da Rahama Ameen.

A safiyar yau Asabar.

02/09/2023

Atiku ya shawarci ECOWAS, AU su tattauna da sojoji Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne a lokacin Obasanjo, ya...
31/08/2023

Atiku ya shawarci ECOWAS, AU su tattauna da sojoji Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne a lokacin Obasanjo, ya bukaci ECOWAS da Tarayyar Afrika (AU), da su tattauna da sojojin juyin mulki cikin lumana domin ganin sun koma bariki.

SUBHANALLÀH: Mijiń Da Zai Aurèta Ya Fasa Saboda Comment Din Ta A Facebook Wani saurayin da aka samusu rana da wacce zai ...
30/08/2023

SUBHANALLÀH: Mijiń Da Zai Aurèta Ya Fasa Saboda Comment Din Ta A Facebook

Wani saurayin da aka samusu rana da wacce zai aura. Ya fasa auren mako guda a daura musu auren saboda sharhin data yi a shafin Facebook.

Budurwar tasa ta shiga wani shafi ne da aka nemi jin ra'ayin mata ko zasu iya cin amanar mazansu akan naira miliyan 1? A yayin ta rubuta koment tace," Sosai kuwa zan iya cin amanar mijina. Miliyan 1 na naira fa ba karamin kudi bane".

Wannan ra'ayin nata ya jawò mata bakin cikin dana sani bayan wani da yasanta yake abota da wanda zai aureta yayi tagging dinsa a kòment din nata. Wanda hakan ya kawo karshen shirinsa na aurenta.

Wannan lamarin daya dace mata su dauki darasi akansa na yadda suke kuskuren wajen rubuta wasu abubuwan da zai iya jawo musu yin da sun sani.

Mè zakù cè?

Da sanyin safiyar yau mutanen kasar Gabon sun fito suna murna tare da yabawa sojojin kasar da s**a yi juyin mulki a kasa...
30/08/2023

Da sanyin safiyar yau mutanen kasar Gabon sun fito suna murna tare da yabawa sojojin kasar da s**a yi juyin mulki a kasar.

The military has announced a coup in Gabon, deposing President Ali Bongo, who was declared winner of Saturday’s election...
30/08/2023

The military has announced a coup in Gabon, deposing President Ali Bongo, who was declared winner of Saturday’s election.

Bongo, who came to power after the death of his father in 2009, won a third term in an election which opposition argued was heavily disputed.

According to Reuters, tensions were running high amid fears of unrest after Saturday’s presidential, parliamentary, and legislative vote, which saw Bongo seeking to extend his family’s 56-year grip on power while the opposition pushed for change in the oil and cocoa-rich but poverty-stricken nation.

A lack of international observers, the suspension of some foreign broadcasts, and the authorities’ decision to cut internet service and impose a night-time curfew nationwide after the poll raised concerns about the transparency of the electoral process.

The BBC quoted soldiers to have appeared on Gabonese national television in Gabon to say they had taken power and annulled Saturday’s election.

The development comes amid the move to resolve the crisis in Niger Republic following the removal of democratically elected President Mohamed Bazoum.

Both the Economic Community of West African States (ECOWAS) and African Union (AU), which have rejected the coup in Niger, are yet to react to the situation in Gabon as of the time of filing this report as developments are still unfolding.

Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Shugaba Ali Bongo Na Kasar Gabon.
30/08/2023

Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Shugaba Ali Bongo Na Kasar Gabon.

Tsohon sanatan Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan salon mulkin Tinubu Ya ce idan Tinubu ya yi da kyau, jama'a z...
27/08/2023

Tsohon sanatan Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan salon mulkin Tinubu Ya ce idan Tinubu ya yi da kyau, jama'a za su yabe shi, akasin haka kuma su caccake shi Sai dai Shehu Sani ya bayyana cewa wasu daga cikin tsoffin gwamnonin da ya ba muƙamai, ƙarin nauyi ne ga gwamnatinsa

Labari ya bazu cewa an yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar Saliyo, yayin da ECOWAS ke tattauna batun juyin mulkin Nijar An s...
27/08/2023

Labari ya bazu cewa an yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar Saliyo, yayin da ECOWAS ke tattauna batun juyin mulkin Nijar An samu fargaba a ƙasar ta Saliyo biyo bayan sak**akon zaɓen shugaban ƙasar da ya gudana a watan Yuni Jami'an 'yan sandan ƙasar sun tabbatar da k**a wasu sojoji da wasu jami'an 'yan sanda dangane da batun.

25/08/2023

Karatu daga masallacin Khalid bin Waleed kagoro by pass kaduna. illar shaye shaye

25/08/2023

Karatu daga masallacin Khalid bin Waleed kagoro by pass kaduna

25/08/2023

Karatu daga masallacin Khalid bin Waleed kagoro by pass kaduna.

Some residents of Abuja are currently trapped in the rubble of a two-storey building that collapsed in the nation’s capi...
24/08/2023

Some residents of Abuja are currently trapped in the rubble of a two-storey building that collapsed in the nation’s capital.

The incident happened at Lagos Street, Garki village area of Garki, in the late hours of Wednesday.

Rescue operation is ongoing and 37 persons have so far been evacuated to Hospital, according to a social media post by Ikharo Attah, an aide to former Minister of the Federal Capital Territory (FCT), Mohammed Bello.

Atah, who also posted a video of the tragic incident, said two persons have been confirmed dead.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bankaɗo wasu matsaloli da s**a dabaibaye ɓangaren ilimi a jihar Kano Kwamishinan ilimi, Um...
23/08/2023

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bankaɗo wasu matsaloli da s**a dabaibaye ɓangaren ilimi a jihar Kano Kwamishinan ilimi, Umar Haruna Doguwa, ya ce an gano makaranta mai ɗalibai 5,000 amma babu aji ko banɗaki Ya roki majalisar Burtaniya ta kawo ɗauki domin farfaɗo da harkokin ilimi domin gyara goben matasa.

Naja’atu Muhammad ba ta cikin wadanda hankalinsu ya kwanta da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu Tun a lokacin kamfe, ‘yar siya...
23/08/2023

Naja’atu Muhammad ba ta cikin wadanda hankalinsu ya kwanta da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu Tun a lokacin kamfe, ‘yar siyasar ta ce ‘dan takaran na jam’iyyar APC bai da wata manufa domin Arewa Ganin yadda aka tattago yaki da makwabta a Nijar, Naja’atu ta ce hakan ya nuna kiyayya ga Arewa.

Kungiyar COSEY ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dawo da tallafin mai don rage wa jama'a radadin da suke ciki Shugaban kung...
23/08/2023

Kungiyar COSEY ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dawo da tallafin mai don rage wa jama'a radadin da suke ciki Shugaban kungiyar, Goodluck Ibem shi ya bayyana haka inda ya ce Tinubu ba shi da tausayi ko kadan Ya ce Shugaba Tinubu na yaudarar 'yan Najeriya da kudaden tallafi don tilasta musu amincewa da karin kudin mai.

Matar Aure Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Kwana 4 A Duniya A
22/08/2023

Matar Aure Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Kwana 4 A Duniya A

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i, ya gargadi kungiyar ECOWAS da ta dakatar da shirin amfani da karfin ...
22/08/2023

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i, ya gargadi kungiyar ECOWAS da ta dakatar da shirin amfani da karfin soji kan sojojin da s**a yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Jami'an Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) sun ce hafsoshin tsaron ƙungiyar sun yanke shaw...
18/08/2023

Jami'an Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) sun ce hafsoshin tsaron ƙungiyar sun yanke shawara a kan ranar da za su tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Nijar, bayan wani taron kwana biyu da s**a yi a Accra, babban birnin Ghana.

"Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni".

A cewar jami'an, Ecowas ta cimma wannan matsayi ne bayan abin da s**a bayyana da kafiya ko taurin kan shugabannin mulkin soja da kuma tarnaƙin da suke ta kawowa a hanyar cimma sulhu game da wannan rikici.

Da yake jawabi ga kafofin yaɗa labarai bayan taron manyan hafsoshin, kwamishinan Ecowas kan harkokin siyasa, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ce ba za su bayyana ranar da s**a sanya ba, saboda dalilai na dabarun aikin soja.

Sai dai ya ce duk mambobin ƙungiyar tara da s**a halarci taron za su ba da gudunmawar dakaru da kayan aikin don shiga Nijar.

Ya jaddada cewa ‘matakin zai kasance irin na gamo da kasawa; kuma zai kasance taƙaitacce don ganin an dawo da tsarin mulki' a Nijar.

Haka zalika sun yi la'akari da illolin tsaro da na jin ƙan ɗan'adan waɗanda mai yiwuwa matakin amfani da ƙarfin sojan zai janyo.

Sai dai, Ecowas ta ce har yanzu ƙofar tattaunawa a buɗe take don warware rikicin ta hanyar lumana kuma za ta aika wani ayarin shiga tsakani zuwa Nijar nan da 'yan kwanaki.

Lamarin dai ya harzuƙa ƙungiyar Ecowas, wadda ta ba da umarnin cewa rundunarta ta ko-ta-kwana ta ɗaura ɗamarar yaƙi.

Manyan hafsoshin tsaron dai sun kuma ƙi yin bayani kan yadda za su tura dakarun da kuma sauran muhimman bayanai game da tsare-tsaren matakin sojin.

Ƙungiyar Ecowas dai na neman lallai a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar da iyalinsa da kuma jami'an gwamnatinsa.

Janar Abdourahamane Tchiani ya ƙwace iko ne cikin watan jiya a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba.

Nijar, ƙasa mai arziƙin yuraniyam, na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya kuma tana fama da wani mummunan rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun soki matakin gwamnatin tarayya na bayar da naira biliyan 180 ga jihohi domin raba wa j...
18/08/2023

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun soki matakin gwamnatin tarayya na bayar da naira biliyan 180 ga jihohi domin raba wa jama'a a matsayin rage raɗaɗin cire tallafin mai.

Haɗakar ƙungiyoyin ƙwadagon NLC da TUC ta ce a yanayin yadda al'amura ke tafiya a Najeriya, ‘yan siyasa ne za su ci gajiyar tallafin na naira biliyan biyar da za a bai wa kowacce jiha, amma ba talakawan da aka fitar da kuɗaɗen domin su ba.

A ranar Alhamis ne, gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya sanar da shirin gwamnatin na bai wa kowacce jiha naira biliyan biyar da tirelolin shinkafa 180 domin rage wa jama’a zafin cire tallafin.

Matakin ya zo ne bayan wani taron Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima a Abuja.

Yaran nan da yazo daga jihar Bauchí domin ganin Jarumar Kannywood Aisha Humaira sai a hankali domin halin da yake ciki z...
18/08/2023

Yaran nan da yazo daga jihar Bauchí domin ganin Jarumar Kannywood Aisha Humaira sai a hankali domin halin da yake ciki zai iya rasa ransa kuma kowa ya kasa taba shi sai an jira yan sanda sun zo.

18/08/2023

Wannan shine halinda yan kasa Nigeria suke ciki musamman arewancin Nigeria. Allah ya kawo mana mafuta Ameen.

innalillahi Wa'ainna Ilaihi 😭 INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN. Yanzu haka mun samu labarin cewa wani Mutum Ya Rataye ...
18/08/2023

innalillahi Wa'ainna Ilaihi 😭
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN.
Yanzu haka mun samu labarin cewa wani Mutum Ya Rataye kasan Har lahira sak**akon kunci Rayuwa Daga ƙauyen Dungun Tantama Yankin Ruba A Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa, Jihar Jigawa,

Allah yasa muyi kyakyawa karshe

17/08/2023

Wannan shine halinda mutanan mu na baya shuka shiga lokacin mulkin mallaka.... ......

Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar dawo da bayar da tallafin man fetur na dan wucin gadi biyo bayan matsin rayuwa da ak...
16/08/2023

Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar dawo da bayar da tallafin man fetur na dan wucin gadi biyo bayan matsin rayuwa da aka shiga da kuma yadda farashin Dalar Amurka ke ta hauhawa tun bayan cire tallafin a watan Mayu, Inji jaridar TheCable



Har yanzu dai shugaban bai tabbatar da wannan kuduri ba amma takardar shawarar tana kan teburinsa, k**ar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa TheCable.

Tuni dai kungiyoyin kwadago s**a yi barazanar shiga yajin aiki na sai Baba-ta-gani idan farashin man fetur ya kara hauhawa.

Manyan hafsoshin tsaron (ECOWAS) za su sake yin wata ganawa ta musamman a kasar Ghana don ci gaba da tattauna yiwuwar am...
16/08/2023

Manyan hafsoshin tsaron (ECOWAS) za su sake yin wata ganawa ta musamman a kasar Ghana don ci gaba da tattauna yiwuwar amfani da karfin soja, a kan sojojin Nijar, musamman a yanzu da suke barzanar hallakar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Tun farko dai an shirya wannan taro ne a ranar Asabar din da ta gabata, amma aka dage shi bayan da shugabannin kungiyar s**a amince da fara aikewa da sojoji Jamhuriyar Nijar don tabbatar da mayar da dimokuradiyya kasar.

Har yanzu dai matsayar da ECOWAS ke dauka na ci gaba da rikitar da mutane, la’akari da yadda ta ke shan alwashin amfani da karfin soji, a wasu lokutan kuma ta ce akwai bukatar a yi amfani da tattaunawar diflomasiyya, k**ar yadda ta fada a taronta na ranar Alhamis din da ta gabata.

Har yanzu dai babu wani tabbas a game da matakin da kungiyar za ta dauka, yayin da gwamnatin sojin Nijar din ke ci gaba da nade-nade da kuma kafa cikakkiyar gwamnati.

A yanzu dai Nijar na karkashin takunkuman ECOWAS da kuma wasu kasashen duniya.

Ƴan kasuwar na cewa lamarin zai iya durkusar da tattalin arziƙin arewacin NajeriyaSa'o'i 7 da s**a wuceWasu 'yan kasuwa ...
14/08/2023

Ƴan kasuwar na cewa lamarin zai iya durkusar da tattalin arziƙin arewacin Najeriya

Sa'o'i 7 da s**a wuce
Wasu 'yan kasuwa sun ce kayan masarufin da suke kasuwancinsu k**ar biskit da ashana, sun fara yanke wa a kasuwa, sanadin datse iyakokin Najeriya da Nijar.

Tun da farko, wata gamayyar 'yan kasuwar arewacin Najeriya mai suna Arewa Economic Forum ta ce rufe iyakokin Najeriya da Nijar, sanadin juyin mulkin sojoji a Niamey, yana matuƙar shafar 'ya'yan ƙungiyar a arewacin Najeriya.

Wani ɗan kasuwa a Kwanar Singa da ke tsakiyar birnin Kano, ya ce rufe kan iyakar ya janyo datse kayansa da na sauran abokan kasuwancinsa kimanin mota goma a Jibiya, cikin jihar katsina.

A cewar Alhaji Ahmed Ɗayyabu rashin samun kayan da s**a yiwo safara, sun sanya wasu kayayyaki sun fara ƙaranci a wajensu.

"Ka ga yanzu, akwai ashana yanzu kakarta ce, saboda da damuna, ana amfani da ita sosai. Maƙwabtan jihohi duk s**an zo nan su sayi ashana domin ana amfani da ita sosai a irin wannan lokaci." A cewarsa: "To ita ma ta fara yankewa.

Ka ga k**ar abin da ya shafi biskit. Mutane s**an ci shi da damuna sosai. Akan haɗa da lemo a ci haka. Irin 'yan biskit ɗin nan masu sauƙi. Naira hamsin, naira saba'in, naira ɗari. Irinsu ne, kuma duk sun fara yankewa.

Kungiyar raya tattalin arziƙin arewacin Najeriyar ta Arewa Economic Forum ta ce lamarin ya haifar da koma-baya ga ‘yan kasuwa, inda duk mako 'yan kasuwar yankin ke asarar aƙalla naira biliyan 13.

‘Yan kasuwar sun ce matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa ba, lamarin zai iya haifar da nakasu da koma-baya ga tattalin arziƙin yankin baki ɗaya.

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Muhammad Kantoma, wanda ya bayyana irin asarar da ake yi cikin tattaunawarsa da BBC, ya ce takunkumin Ecowas ya sa al'ummar Najeriya da Nijar sun daina amfana da harkokin kasuwancin k**ar yadda s**a saba.

‘’Akwai mutanenmu da ke shigowa da kaya ta iyakokin Nijar daga wasu kasashe tun lokacin da aka rufe boda, akwai aƙalla kwantena 2,000 da wani abu,’’ in ji Kantoma.

"Aƙalla kar

Sojojin sun ce sun tattara bayanan laifukan da Mohamed Bazoum ya yiSa'a 1 da ta wuceSojojin da s**a yi juyin mulki a Nij...
14/08/2023

Sojojin sun ce sun tattara bayanan laifukan da Mohamed Bazoum ya yi

Sa'a 1 da ta wuce
Sojojin da s**a yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara isasshiyar shaidar za a iya gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar ƙasa.

Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen ƙasar, zagon ƙasa.

Kakakin sojin Kanal Amadou Abdramane ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ta tashar talbijin ta ƙasar.

Ana sa rai, ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za ta gudanar da wani taro ranar Litinin ɗin nan don ci gaba da matsa lamba ga sojojin juyin mulki su hau teburin tattaunawa, haka ita ma Majalisar Tsaro da Tabbatar da Zaman Lafiya ta Tarayyar Afirka za ta yi taron don tattaunawa a kan rikicin.

Sojojin na tsare da Bazoum da iyalansa a wani ɗaki na ƙarƙashin ƙasa a fadar gwamnati da ke birnin Yamai, tun bayan hamɓarar da shi a ranar Lahadi 26 ga watan Yulin bana.

Baya ga shugaban sojojin sun kuma k**a wasu daga cikin jiga-jigan gwamnatinsa da ma na jam’iyyarsa ta PNDS Tarayya.

Mai magana da yawun gwamnatin sojin ya ce tuni sun riga ma sun tattara duk wasu bayanai da shaidun da suke buƙata domin gurfanar da Bazoum a gaban shari’a.

Kashi-kashi
End of podcast promotion
A sanarwar, kakakin ya ce, za su gurfanar da Bazoum tare da waɗanda ya kira masu haɗa baki da shi a cikin ƙasar da ma ƙetare a kan laifukan da s**a zayyana, saboda musayar bayanan da ya yi tsakaninsa da wasu ‘yan ƙasashen waje da shugabannin ƙasashe da kuma shugabannin ƙungiyoyin ƙasashen duniya.

Bayan karɓe mulki tare da rushe zaɓaɓɓiyar gwamnatin tuni s**a naɗa majalisar ministoci, tare da yin biris da duk wani kira na neman sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya, daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO da sauran ƙasashe da hukumomi masu rajin kare dimokraɗiyya na duniya.

Wannan ya janyo s**a daga ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya.

Biris da halin ko-in-kula tare da ƙara kankane iko da k

Farashin abinci a duniya k**ar su shinkafa da man girki zai yi tashin da bai taɓa yi ba cikin shekara 12.Wannan na cikin...
14/08/2023

Farashin abinci a duniya k**ar su shinkafa da man girki zai yi tashin da bai taɓa yi ba cikin shekara 12.

Wannan na cikin wani rahoto da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a watan Agusta, wanda ta ce hakan ya zo ne bayan ficewar Rasha daga yarjejeniyar fitar da abinci da aka cimma tsakaninta da Ukraine ta ruwa.

FAO ta ce alƙalumanta sun nuna an samu ƙaruwar kashi 12.1 na farashin man girki bayan irin wannan tashin a cikin watanni bakwai a jere.

Farashin shinkafa ma ya tashi da kashi 1.3 a watan Yuli idan aka kwatanta da watan Yuni, k**ar yadda FAO ta bayyana a ranar Juma’a.

An riƙa samun faɗuwar kayayyakin abinci a duniya a bara wayan wani tashin gwauron zabi da abincin ya yi lokacin da ake tsaka da rikicin Rasha.

Ƙara samun katsewar fitar da abinci daga da aka samu a bayan nan bayan ficewar Rasha daga cikin yarjejeniyar fitar da abinci da aka cimma da Ukraine, ya sanya ƙayan abinci tashi a faɗin duniya.

Ƙasashen Rasha da Ukraine ne ke kan gaba wajen noma tare da fitar da alƙama da wasu sauran nau’o’in hatsi da akan iya sarrafawa a fitar da su duniya, musamman zuwa nahiyar Afrika da Gabas ta tsakiya da kuma Asiya inda miliyoyin mutane ke fama yunwa.

“Ƙasashen da s**a dogara da shigo da abinci za su yi matuƙar kaɗuwa ta tashin farashin, saboda zai janyo hauhawar farashin sauran kayayyaki da talauci da matsalar abinci,” in ji rahoton.

Rashin amfani da Baharul Aswad wajen fitar da hatsi ya janyo tashin farashin alƙama da kashi 1.6 a watan Yuli idan aka kwatanta da wata Yuni.

Rahoton hukumar ya ce wani abu da zai ƙara tayar da hankalin duniya shi ne haramcin fitar da shinkafa da India ta yi, wanda ya sanya ‘yan kasuwar ƙasar ɓoye wadda suke da ita a hannu zuwa kasuwannin duniya.

Haramcin fitar da shinkafa daga Indiya da kuma ficewar Rasha daga yarjejeniyarta da Ukraine ya sanya farashin shinkafa ya tashi da kashi 2.8 a watan Yuli, ya kuma ƙaru da kashi 19.7 a wannan shekarar, mafi yawa tun Satumbar 2011, in ji FAO

Wannan lamari sai ya fi shafa

Ina Tausayin Tinubu Saboda Yasa Gaggawa Akan Maganar Nijar, Cewar Manjo Hamza Al-Mustapha"Ba zai yiwu kana maganar diplo...
10/08/2023

Ina Tausayin Tinubu Saboda Yasa Gaggawa Akan Maganar Nijar, Cewar Manjo Hamza Al-Mustapha

"Ba zai yiwu kana maganar diplomasiya amma kuma kana bayar da umarni irin na soja ba, idan anaso dimukuraɗiyya ta ɗore sai da hankali da bin dokoki da girmama juna." Inji Al-Mustapha.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madugu TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share