16/05/2023
BORNO: Sojoji Sun sake ceto ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok Bayan shekaru 9 a hannun Boko Haram
Kwamandan shirin Operation Hadin Kai Manjo Janar Ibrahim Ali, ya ce an yi ƙubutar da wata ƴar makarantar Chibok.
Sojojin ƙasa ne su ka ceto Saratu Dauda mai shekaru 25 a ranar 6 ga Mayu, 2023 a maɓoyar ƴan ta’adda a yankin Ukuba a dajin Sambisa, dake jihar Borno.
Da yake miƙa Saratu ga Kwamishiniyar Harkokin Mata da Cigaban Jama’a, Hajiya Zuwaira Gambo, a Maiduguri, Manjo Ali ya bayyana cewa: “Kafin a cece ta bayan ta tsere, Saratu ta auri Abu Yusuf, wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram."
Janar Ali ya bayyana cewa, Saratu ta bar ƴaƴanta uku tare da mijinta da aka tilasta mata aurensa, sannan ta tsare daga dajin Sambisa. Ƴa ƙara da cewa "ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran yaran da ke hannun mijin Abu Yusuf".
A halin yanzu dai tuni Saratu ta samu kulawar likitoci a asibitin sojoji dake barikin Maimalari; kafin mika daga bisani ya miƙata ga gwamnatin jihar.