21/10/2023
هنا العلم والحكمة
Dr Muh'd Sabi'u Sulaiman
Game da ta'addancin Yahudawa kan musulmai falasɗinawa:
1. Wajibi ne muji damuwa da baƙin cikin abinda ke faruwa da yan-uwanmu musulmai na kisan zalumci da ake musu, da ragargaza gidajensu a kansu.
Mumini yana damuwa da damuwar ɗan uwansa musulmi, wani lokacin har damuwar takan iya damautarwa, zuciya takan tafasa da kunci k**ar zata fashe, ɗanɗanon bacci ya gushe, wannan shine wajibin yan-uwantakar musulunci.
Kuma Wajibi ne muyi abinda zamu iya wajen kawar da wannan zalumcin da akeyi kan raunanan yan-uwanu, kowa gwargwadon abinda zai iya, cikin iyakokin shari'a.
Mafi kyawun abinda zamuyi shine komawa ga addininmu ginshiƙin samun ƙarfinmu, muyi ruƙo dashi mu ɗaukaka shi, muyi watsi da maƙiyanmu da tafarkinsu da ɗabi'usu, Yahudawa ne ko Amerika ce ko sauran kasashen yamma ne, adawarsu ta riga ta bayyana garemu da makircinsu, ko basu hallaka ka da makami ba sun ɗanɗana maka baƙin ciki da damuwa.
Haƙiƙa idan zaka cigaba da ruɗuwa dasu da goyan bayan siyasarsu kode ƙarya kake kai ba mai son Addini bane ko kuma bakasan abinda kakeyi ba..!!
2. Sa'annan abinda ya gabata bazai saka mu kawar da kai daga ɓatan ikwanul Muslimeen da reshensu Hamas ba, matsayar mu game da su, matsaya ce ta Shari'a, ba ta Aɗhifa ba:
A. Dukkansu biyu ba kan tafarkin dai-dai suke ba, haƙiƙa dukkansu ma'abota saɓawa sunnah ne, Kada a ruɗu da maganar maha'incin addini wanda yake tsarkake tafarkinsu.
B. Al'ummar musulmi a yau al'umma ce mai rauni ta kowacce fuska, rauni mafi muni, wajibine falasɗinawa a game da hamas a keɓance su zama masu hangen nesa, Kada su riƙa afkawa tarkon maƙiya, ta yadda zasu riƙa tunzuruwa idan an tinzirasu, haƙiƙa halinsu k**ar wanda yake kurkuku ne, maƙiyinsu yana neman duk wani sababi ne na kashe adadi mafi yawa da zai iya, babu shakka biye masa a wannan yanayi na rauni rashin hangen nesa ne, wajibinsu shine ƙoƙarin samun karfi da cin gashin kai a rayuwa, sannan tanadin abinda zasu tinkari maƙiyanmu, muma wajibine mu taimaka musu kan haka.
Mafi girman abinda zai lamunta mana nasara mu dasu baki ɗaya komawa ga Allah da hukunta addininsa a cikin komai namu, da nisantar duk abinda zai saɓa masa, da nisantar shirkoki da bidi'o'i da saɓon Allah waɗannan sune sababin ƙasƙancinmu da rauninmu.
3. Wasu Suna amfani da wannan hali na damuwa da ya taɗa hankulan musulmai, waje yaɗa aƙidarsu da tafarkinsu na ikwanul Muslimeen da dayawan musulmai s**a gane ɓatansa da ɓarnarsa a fili, musamman bayan bore da s**ayi a kasashen musulmi da ya haifar da asarar rayukan miliyoyin musulmai da ƙarin raunin al'umma.
ɓidi'arsu ta bore da ta saɓawa ɗaruruwan hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, da ƙarya, da yaudara, da hauragiya, da har gamagarin musulmai duk sun gane, amma a yau wasu na ƙoƙarin yayyafawa wannan manhaji na ɓarna ruwa, ta hanyar ribatar adhifar musulmi a wannan yanayin, waɗannan su sani Ahlusunnah suna dakonsu!!!
A wani bangare kuma wasu guguwar Aɗhifa da damuwa tasa sunyi sulu cikin taɓo na saɓawa shari'a.
A. Wani yana wuce iyaka wajen ƙyamatar bidi'ar ikwan, har ya zama yana suranta k**ar sune duk wani sababin ta'addanci la'annanun Yahudawa, su Yahudawan barrantattu ne!
B. Wasu kuma da sunan goyon bayan musulmi kan kafirai, sun wayi gari suna tallata ɓarna, suna kare ɓata, suna sauya haƙiƙa.
Abinda yake wajibi lokacin damuwa idan mutum bazai iya dabaibaituwa da Shari'a ba yayi shiru, Kada yayi ta kutsawa cikin ɓarna ba tare da tabbatuwa ba, dayawa sun samu zamiya da karkacewa ne saboda kajerun hakuri lokacin fitina da damuwa irin wannan, wani ya koma ɗan koran arna, wani ya zama barafide ɗan shi'a, wani ya zama bakwarije, mutun yayi ƙoƙarin danne zuciyarsa ya yawaita addu'a Allah ya tabbatar da zuciyarsa, yayiwa dukkan musulmai fatan Allah ya gyra sha'aninsu, haƙiƙa shiriya da tattabatuwa na hanun Allah, kuma sune mafi ƙarfin makamin cin nasara....