30/10/2023
DAGA SHAFIN Hon Galadima abba itas
TSOKACI AKAN WANDA AKA RIƘE MUSU ALBASHI A ITAS/GADAU KUMA NA BAMA LAUYOYINA UMARNIN SANAR DA OF ƊAUKAR MATAKIN SHARI'A DON NEMAN HAKKIN MA'AIKATA
Mu shuwagabannin a karamar hukumar Itas/Gaɗau muji tsoron Allah, mu sani kafin zamanin mu wasu sunyi zamani ya shuɗe
Yau ace a ITAS/GADAU shugabane da yake shugabantar Al'ummar daga zaɓaɓɓe zuwa wanda aka naɗa ko stakeholder sune suke bada umarnin a riƙe Albashin mutum a wannan lokacin saboda banbancin akida ta jam'iyya ko siyasa a matsayin horo
Tun lokacin da akayi zaɓe aka riƙe albashin wasu daga cikin ma'aikatan karamar hukumar Itas/Gaɗau har yanzu ba'a basu ba , wallahi wannan zaluncine zaluncine
Kafin wannan rubutun nawa, sati 3 da ya wuce nayi magana da shugaban ƙaramar hukumar ITAS/GADAU nace masa idan kaine kariƙe musu Albashin nan kayi hakuri ka basu kayansu yace shi umarni Hon Maiyadi da Hon Hajara s**a bashi a rike, Na kira chairman party na PDP Hon Sule boss a matsayin sa na shugaban Kuma stakeholder yace shi wallahi baisan wanene yasa aka rike albashin nan ba
Kwamiti ɗan uwana Abdurrahman da kungiyar NULGE da sauransu sunje sun zauna da Hon Hajara ( commissioner )da Hon Maiyadi Member State Assembly na Itas/gadau kuma sun dauki waɗanda aka rike musu Albashi domin su basu hakuri, amma da Hajara da Maiyadi su kace su babu hannunsu chairman na karamar hukuma ne ya rike musu albashi babu ruwansu
Nayi magana da Ministry of Local Government and chieftain Affairs sun tabbatar mu babu hannunsu a cikin wannan riƙon Albashin
Jama'a yanzu mai imani wanda yake da iyaye,ƴan'uwa mata,yara kuma shugaba idan zaici abinci tare dasu Yakamata ya tuna ya hana iyalan wasu hakkinsu? Kana shugaba kana biyan kuɗin makarantar yaranka shin baka tunawa wanda kuka rike musu albashi sun cire yaransu a makaranta wata biyar daya wuce,
Wai yau irin wannan shugabanci muke yi a matsayinmu na shuwagabannin wanda matasa zasuyi koyi damu a yau a karama