16/09/2023
DALILI A BAYYANE DAKE TABBATAR DA YAN TIJJANIYYA SHEHU YAFI ANNABI A WAJANSU.
SHI NE: SALATIN DA ANNABI YA KOYAR DA SALATIN DA SHEHU YA KAWO.
Idan Mukayi Duba da Yanda Sukeyin Raddi akan Salatul Ibrahimiyya, Salatin da ba Ibn Taimiyya ya kawo shi ba, ba Ibn Abdulwahab Ya kawo shi ba, Ba Sheikh Ja'afar Ya kawo shi ba, Amma Sun Dage da Yi ma Salati Raddi akan Sai Sun Tabbatar da Salatin Shehu Yafi na Annabi.
Abarshi akan Cewa Salatul Fati Salatin Gaskene, a Matsayin su na Wa'yanda Suke Ƙaryar Son Annabi, Mi ya hana su Fifita Salatin Da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama Ya Koyar da Lafazin Bakinshi, Sahabbai S**a ji S**a Koyar da Ɗalibansu?
Shin Wa Suke ma Raddi? Miye na Dole sai sun Tauye Salatin Manzon Allah? Idan Shehu Bai Fi Annabi ba a Wurinsu, Miyasa Suke Fifita nashi akan Na Annabin?
Yana Daga Cikin Abinda Shehu Yace: Salatil Fati Yanasa Ka Mutu da Imani, Kuma s**a Yarda. To Salatin Annabi Shi Baisa a Mutu da Imanin ne?
Ku Rabu da Shehu Kubi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, Allah Ya Shiryeku Yasa Ku Gane.