Jibwis WASE

Jibwis  WASE Truth is like a lion release it , he will defend himself.

Official letter from the Vice Chancellor of National Open University of Nigeria (NOUN), to  Rt. Hon. Ahmed Idris Wase in...
19/05/2024

Official letter from the Vice Chancellor of National Open University of Nigeria (NOUN), to Rt. Hon. Ahmed Idris Wase informing him about the forthcoming commissioning of the NOUN STUDY CENTRE WASE, following the completion of construction work at the site.

Date: Friday, 24th May, 2024
Time: 10:00 am
Venue: NOUN STUDY CENTRE, WASE.

Congratulations, Wase Federal Constituency and Thank you Hon. Ahmed Idris Wase for your service and dedication.

Adamu Adamu
18th May, 2024.

22/11/2021

MUN GAMA SALLAH, ASHE LIMAN YA MANTA BASHI DA TSARKI?

Tambaya
Asl mal mune mukayi sallah muna karewa liman yace yamanta baida tsarki yayi fitsari baiyi tsarki ba. zamu maida wata sallah ne kota limance kawai babu tunda mu da tsarkinmu ko har tashi tayi daidai?

Amsa
To dan'uwa sallar liman ta baci, kuma dole ya sake, amma ku sallarku ta inganta, a zance mafi inganci, saboda dalilai kamar haka:

1. An rawaito daga Umar- Allah ya yarda da shi cewa : ya taba yiwa mutane limancin sallar asuba, bayan an gama sallah, sai ya ga maniyyin mafarki a jikin tufansa, sai ya sake sallah, amma mamun ba su sake ba.

2. Sayyidina Aliyu yana cewa: "Idan mai janaba ya yiwa mutane limanci, zan umarce shi ya yi wanka, ya sake sallah, amma ba zan ce da mamun su sake ba.

3. Abdullahi dan Umar - Allah ya yarda da shi- ya taba yiwa mutane sallar asuba, sai ya tuna ba shi da alwala, sai ya sake amma mamu bas u sake ba.

Abin da ya gabata aikin sahabbai ne, aikin sahabi hujja ne, in ba'a samu wani sahabin ya saba masa ba.

Don neman Karin bayani duba: Almugni 1\419.

Allah ne mafi sani.

27\4\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNWith rudest shock but with total submission to the supreme will of Allah, I regret to ...
10/07/2021

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

With rudest shock but with total submission to the supreme will of Allah, I regret to announce the demise of our Sheikh, Imam Abubakar Salihu Bidazum Dengi which occurred this night at ATBU Teaching Hospital Bauchi.

Funeral prayer will take place tomorrow morning by 9:0am in Bauchi Insha Allah.

May Allah forgive his shortcomings and grant his soul eternal rest.

06/07/2021

HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)

Tambaya:*
Shin ko akwai dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu tazarar haihuwa?

Amsa:
To dan uwa amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu:

1. Ya zama zai hana daukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya sabawa manufar shari'a na yawaita al'uma, kuma 'ya'yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.

2. Ya zama an tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna azalu a zamanin Annabi ﷺ don kar matansu su dauki ciki, kuma ba'a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.

Abin da ake nufi da azalu shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai fito sai ya fitar da azzakarinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.

Duba Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.

13/7/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

17/06/2021

SHAYAR DA MUTANE RUWA YANA DAGA CIKIN MUHIMMAN ABUBUWA MASU TARUN LADA

✍️Rubutawar
Sheikh Aliyu Said Gamawa

A lokacin da mahaifiyar Sa'ad bin Ubada (RH) ta rasu sai yace: Ya manzon Allah (saw) mahaifiyata ta rasu, shin zan iya mata sadaka?

Sai manzon Allah yace "Eh" sai Sa'ad yace, wacce sadaka ce tafi falala?

Sai Manzon Allah (saw) yace "Shayar da ruwa"

A nan ana nuna mana cewa sadaka mafi samar lada shine ka shayar da mutane ruwa

Shayarwa ta hanyar tona rijiya ko borehole, ko samar da ruwa a masallaci ko wani wuri da mutane ke taruwa don su sha ko suyi ibada.

Hakika duk dabba ko tsutsa, ko bishiya ko kwaro ko bil Adam ko aljani daya amfana da ruwan daka samar ana baka lada, haka in aka samar a matsayin sadakatul-jariya ga mahaifa ana kai masu ladan

Allah ya bada iko ya kar6a mana aiyukan mu na alheri, amin

21/05/2021
20/05/2021

Akwai Abin mamaki Cikin wannan labarin. Wanda galibin masu sauraron BBC Hausa sun San shi mai amsa Tambayoyi akan kiwon lafiya. An taba Tambaya shi akan Family Flannning Ga Tambayar Da Dan Jarida ya masa

Tambaya : Dakta wasu Na kokawa akan Family Flannning wani shawara zaka basu akan haka ?

AMSA : Toh Da Farko dai Bada tazara ga mace mai larura mai Dauke Da wani Rashin lafiya Abu Ne mai kyau. Amma ga mace da lafiyanta lau wannan ba Dabi'a ce mai kyau ba. Yace barin baku misali akaina. Mahaifin mu ya Haife mu a Gidan mu. Mu talatin da biyar. Kaf cikin mu talatin da biyar Dinnan nine Dan Autansu kuma nine Wanda Allah Ya Daukaka Yanzu Haka Ina cikin likitocin Duniya Wanda ake tunkaho dasu a Duniya kenan da ace Mahaifiyata da ace tayi Family Flannning dina da Yanzu ban Rayu na taimaki Alumma Duniya ba.

Allahu akbar kalubalenku Yan Boko AQEEDA masu Ganin cewa yawan haiyayyafa shike kawo Talauci wallahi ba haka bane..Allah ya riga Ya Rubutawa kowa Arzikinsa. Allah ka bamu Daman kara Yarda da kaddaranka Ameen Thummah Ameen
Copy from Barrah Almadany!!

JIBWIS TACKLES CAN ON PALESTINE - ISREAL CONFLICT* Calls Nigerian Government not to support IsrealThe Jama'atu Izalatil ...
19/05/2021

JIBWIS TACKLES CAN ON PALESTINE - ISREAL CONFLICT

* Calls Nigerian Government not to support Isreal

The Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'iqamatis Sunnah, JIBWIS-Nigeria, under the leadership of Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau, have strongly warned the Christian Association of Nigeria, CAN, against making inciting statements about the continuing brutal attacks on palestinians in Gaza.

In their statement released, Monday, where CAN urged the Federal Government to end it's support for Palestinians and warned President Buhari against siding with the Palestinians.

The Isreali forces attacks resulted in the death of of over 190 Palestinians, including 58 children and 34 women as well as about 1,235 persons that are suffering varying degrees of injuries.And about ten people killed in Isreal that includes two children.

Despite widespread condemnation of these brutal attacks by the Isreali forces on Palestinians and their places of worship, why is CAN preventing President Muhammadu Buhari from joining other world leaders in condemning a clear violation of Palestinians rights that are as well human beings? Why is CAN calling the Nigerian government to lend it's support on the brutal Isreali attacks on the Palestinians in Gaza.

We therefore called on the Christian Association of Nigeria, CAN, to refrain from such inciting statements that may lead to unnecessary religious crisis in this period when the country is being faced with security challenges, which our security agencies are already working so diligently to curtail.

Article 3 of the Universal Declaration on Human rights states that everyone has a right to life, liberty and security.

Palestinians are no exception. Their rights, liberty and security must be protected without bias.

JIBWIS, however, called on the International community to come together and bring an end to this deadly bombardment on Gaza by the Isreali forces and the unlawful occupation of Palestinian territory, as it's a clear violation of their fundamental human rights.

Therefore, there's nothing wrong for Nigeria to stand against the brutal attacks on the Palestinians as it's a clear violation of their fundamental human rights which article 3 of the Universal Declaration on Human rights seeks to protect.

JIBWIS NIGERIA

SHEIKH ABDULRAZAQ YAHAYA HEIPAN YA GINA MAKARNTA DON KOYAR DA MARAYU HADDAN ALQUR'ANI MAI GIRMA!!!Babban malamin addinin...
19/05/2021

SHEIKH ABDULRAZAQ YAHAYA HEIPAN YA GINA MAKARNTA DON KOYAR DA MARAYU HADDAN ALQUR'ANI MAI GIRMA!!!

Babban malamin addinin muslunci Sheikh Abdurrazaq Yahaya Haifan. Ya ginawa Al'ummar Musulmai da marayu makarantar Haddar AlQurani a Gwagwalada Abuja.

Wannan shine bambamcin malaman Sunnah da malaman Bidi'a. Bayan sun karantar da al'ummmar musulmai Addini, sannan suyi amfani da dukiyarsu wajen gina addinin.

Muna Addua Allah SWT ya sakawa Malam da mafificin alkairi, yasa wannan makaranta ta zama sanadiyar shigarsa aljannah. Ameen thumma Ameen.
🙏🙏🙏

Babangida Mu'azu Isah Fago

KADUNA/KWADAGO-HAWA TEBURIN SULHU SHI NE ZABI MAFI A'ALA-SHEIKH BALA LAUShugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala L...
18/05/2021

KADUNA/KWADAGO-HAWA TEBURIN SULHU SHI NE ZABI MAFI A'ALA-SHEIKH BALA LAU

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce za a iya warware rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar 'yan kwadago cikin lumana ta hanyar hawa teburin shawara tsakanin sassan biyu.

Shehun malamin ya ce za a iya samun maslaha kan shirin gwamnatin jihar Kaduna ta Malam Nasiru Elrufai na rage yawan ma'aikata; ta hanyar zama waje daya tsakanin wakilan gwamnati da na kwadago da tsoma bakin dattawa, kwararru da shugabannin jama'a.

Ba za a bar jihar Kaduna a matsayin helkwatar arewa ta zama a cikin irin wannan rudanin ba don hakan ka iya fadada ya shiga wasu sassa ko jihohi.

Don haka Imam Bala Lau ya bukaci gwamnati da 'yan kwadago su maida zuciya nesa ta hanyar warware takaddamar ta hanyar tattaunawa.

"ba za mu koma gefe mu na gani birnin mu mai daraja ya kasance cikin yanayin rudani ba. Don haka mu hadu don gano bakin zaren warware wannan takaddama ta hanyar da kowane bangare zai samu gamsuwa."

Yayin da malamin ke lura da yanda jihar Kaduna da makwabta ke gwagwarmayar magance kalubalen 'yan bindiga; ba daidai ne masu ruwa da tsaki su bari wata sabuwar kura ta taso ba.

A nan shugaban na Izala ya yi addua'ar neman taimakon Allah madaukakin sarki ga samun zaman lafiya mai dorewa, hadin kai, fahimtar juna da kwanciyar hankali a jihar Kaduna, yankin arewa da Najeriya gaba daya.

JIBWIS NIGERIA

09/05/2021

GARKUWAN MARAYUN NIGERIA

Inka tambayeni waye Garkuwan Marayun Nigeria, bazanyi kasa a gwuiya ba wajen ce maka Sheikh Kabiru Gombe ne.

Allah yayi amfani da wannan bawan Allahn ya ciyar da marayu kuma ya tufatar dasu. Daga fara Tafsirin bana 2021 zuwa jiya da aka rufe, sun tara gudunmawan kudi Naira Miliyan Talatin da Dubu Chasa'in da Daya (N30,091,000).

Duka wannan jimillar kudi da kaya an taimakawa Marayun da s**a kai (dubu 70) wannan banda gudunmawan kayayyaki sawa da na abinci.

Fatan Allah ya sakawa Mallam, dukkan 'yan kwamitin da wadanda s**a taimaka da mafificin alkhairi...🤲🤲

ALLAH KASA MUN DACE!!
07/05/2021

ALLAH KASA MUN DACE!!

05/05/2021
05/05/2021

ALAMOMI GUDA SHIDA-(6) NA DAREN LAILATUL QADRI

Lailatul qadr na da alamomi da ake gane shi da su,Wadannan alamomi s**an kasance ne cikin daren kansa:

1-Dare Ne Matsakaici,Babu Zafi sosai Ko Sanyi sosai A Cikinsa

An karbo daga Jabir Dan Abdullahi Allah ya yarda da shi ya ce,
“Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri,sannan an mantar da ni shi,yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa a cikinsa
Khuzaima ne ya rawaito shi.

2-Rana Tana Fitowa Da Safiyar Daren Fara Tas Ba Haske Tare Da Ita.

Yayin da aka tambayi Ubayyu Dan Ka’abu bAllah ya yarda da shi a kan alamomin daren Lailatul Qadri, sai ya ce, (Alamar da Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ya ba mu labari ita ce, rana tana vullowa a wannan rana babu haske tare da ita)
ne ya rawaito shi.

3-Yanayi zai canza ya zama mai dadi,Za a ji iska mai dadi, natsattsiya.
Khuzaima da Dayalisi

4-Samun Natsuwar zuciya da kimtsuwa,Farin ciki cikin zuciya da samun jin dadin ibada.

5-Za ka iya ganinshi (Lailatul Qadr) a mafarki kamar Yadda sahabbai s**a gani
wai za ai mafarkin wani tsunburkai ba ne a a za a iya yin mafarkin ga shi ana ibada a cikin daren za ji karsashi wajen yin ibadarsa

6-Rana zata fito ba zafi (in lokacin zafi ne)


Wadannan su ne alamomin da ake gane daren lailatul qadr. Amma da ake cewa itatuwa zasu fadi su yi sujada,zaka ga rana a kasa, karnuka za su daina kuka,za a ga taurari a kasa,wannan qage-qage da tatsuniya aka qaga a cikin addini wanda kuma ba gaskiya ba ne.

Allah ne mafi sani

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ
“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa fa’afu anni”

28/04/2021

PANTAMI OF ALL PEOPLE

The Saudis expelled Usama Bin Laden because of his terrorism tendencies, the same Saudis employed Pantami to lecture in its University because they know that Pantami does not have terrorism tendencies.

The US and UK did not see the Pantami as a threat when he studied there and even became an instructor in the prestigious HARVARD UNIVERSITY. Those two countries would not allow someone to ask them to enlist him in their watch list. Yet Pantami was cleared to study there.

The DSS did their thorough investigation before they cleared Pantami to head NITDA and Ministry of Communication and Digital Economy.

Those calling and linking Pantami with terrorism are basically Yahoo boys whose criminality would be hampered after the success of NIN/SIM registration of the Ministry of Communication headed by Pantami.

Those calling for Pantami's resignation are treading the same path of Abubakar Shekau, the leader of Boko Haram, who wants him killed because he brings to bear NIN/SIM registration that would drastically curtail the terror of Boko Haram.

Pantami is never accused of under performance and misconduct in the Ministry he heads.

Those trailing Pantami were well with him when he was DG NITDA because his work did not trail them, but they want him out because his performance is trailing their criminalities.. They also want kidnappers to continue their onslaughts on Nigerians.

Pantami's performance brought the Ministry of Communication to limelight. He was one of the Ministers that were appointed on merit, given his sterling performance at NITDA.

If other Ministers of Nigeria are as performing as Pantami, Nigeria would uptimally changed to the better.

Pantami should not succumb to the cheap blackmail to resign. He should redouble his performance for the betterment of the Ministry of Communication and Digital Economy.

26/04/2021

MU NE MATSALAR KASARMU

"Malam ka dubi yanda kasarmu ta lalace, idan wani abu ya faru, sai aje a nemo wani mai fashin baki a gidan radio yazo yayi fashin baki, sai kaga inda matsalar kasar tayi daban, inda fashin bakinsa yayi daban, shima wanda yake fashin bakin yana bukatar ayi masa fashin baki"
✓Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum

21/04/2021

KALUBALEN MU 'YAN-AREWA Daga bakin Sheikh Dr NAZEEF YUNUS JOS!

07/04/2021

SUNAYEN MALAMAI DA ALARAMOMI DA JIBWIS TA KASA TA TURA TAFSIRI RAMADAN NA 1442/2021 A JAHOHIN NAJERIYA
1-Shaikh Dr. Abdullahi Bala Lau da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu, Jimeta Adamawa

2-Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo da Alaramma Mustapha Jalingo, Jalingo Taraba

3-Sheikh Usman Isa Taliyawa da Alaramma Abubakar Muhd Gombe, Gombe.

4-Sheikh Abbas Jega da Alaramma Abubakar Adam. B/Kebbi, Kebbi.

5-Shaikh Ibrahim Sabiu Jibiya da Alaramma Aminu Salisu Jibiya, Masjid Hamza Jibiya, katsina.

6-Sheikh Yakubu Musa Hassan da Alaramma Usman Birnin Kebbi, Masjid Kandahar Katsina

7-Sheikh Pro. Abdullahi Saleh P**istan da Alaramma Abbas Iliyasu Kano, Tudun Martala, Kano.

8-Sheikh Dr, Muh’d Kabir haruna Gombe da Alaramma Ahmad Sulaiman, T/Wada/Malali, Kaduna.

9-Sheikh Abubakar Giro Argungu da Alaramma Saifullahi Musa Makera, Kwantagora, Niger.

10-Sheikh Aliyu Abdullahi Telex da Alaramma Muhsin Ishaq, Aleiru, Kebbi

11-Sheikh Surajo Muhammad Gusau da Alaramma Jamilu Muhammed Dan Magi, Gusau, Zamfara

12-Sheikh Mas’ud Ibrahim Offa Offa, Kwara

13-Dr. Muhammad sani Umar R/lemo da Alaramma Abubakar Muhammad Rariya, Masjid Gwallaga, Bauchi

14-Sheikh Sani Yakubu da Alaramma Ridwan Kaduna, Zariya Kaduna

15-Sheikh Dr. Ismail Kumo Basirka da Alaramma Abdulrashid Sulaiman Jega, Minna, Niger

16-Sheikh Ahmad Muhammad Boyi da Alaramma Muhammad Aliyu Babangida, Masjid Finance Jalingo, Taraba

17-Dr. Ibrahim Abdullahi R/Lemo Alaramma Abdullahi Salisu, Western by Pass, Kano

18-Prof. Umar Labdo da Alaramma Aliyu P**i Abuja, Berger Masjid Abuja

19-Mal. Imam Aliyu bunza da Alaramma Sulaiman Adamu, Argungu Kebbi

20-Sheikh Gambo Kyari Maiduguri da Alaramma Adam Alhaji Allawan, Masjid Tashihul Aqida, Dikwa Low cost Borno

21-Sheikh Modibbo Muctar Gaundare da Alaramma Dahiru Musa Jega, Gire Adamawa

22-Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale da Alaramma Saifullahi Kira, Area 11, Abuja

23-Dr. Zakariya Idris da Alaramma Usman Ya’u Gido, Gumel, Jigawa

24-Dr. Bishir Iman, Masjid Amd. Yola, Adamawa

25-Dr. Sadau Salihu, Yola Adamawa

26-Dr. Magaji Zarewa da Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi, Lagos Lagos.

27-Dr. Abubakar Ali Bama, Karem Lamido, Taraba

28-Dr. Abdulrahaman Sani Yakubu da Alaramma Hudu Usman Ashiru, Juwa Emirate Council, Abuja

29-Mal. Usman AbdulHamid, Numan, Adamawa

30-Dr. Ibrahim Adam Umar Disina, Masjid Rahama, Bauchi

31-Sheikh Prof. Mansur Ibrahim sokoto da Alaramma Abubakr Gani, Masjid Abu Huraira, Sokoto

32-Dr. Muhammad Rabi’u Collage da Alaramma Sidi Ali, Gashua, Yobe

33-Mal. Hussaini Isa Abubakar da Alaramma Salihu Mukhtar, Makurdi, Benue

34-Mal. Muhammad Dawud Damaturu, Damaturu Yobe

35-Mal. Abdulbasir U/Maikawo da Alaramma Sani Malumfashi, Wukari Taraba

36-Mal. Ali Aliyu Jos da Alaramma Baba Abubakar Tambuwal, Tambuwal Sokoto

37-Mal. Umar Mai Damma da Alaramma Auwal Adam Sokoto, Masj Shk Ab Gumi Sokoto

38-Mal. Abubakar ladan Mai Idigami da Alaramma Muhamma Auwal Sokoto, Masj Lokoja Road Sokoto

39-Mal. Abdurrahman sani Mai Tawul da Alaramma Hassanu Abubakar Umar, Sultan Ibrahim Dasuki

40-Dr. Abubakar Usman Ribah da Alaramma Muhammad Bunza Borgu, Niger

41-Mal. Saifuddeen Yakubu musa, Masjid kandahar Katsina (Tafsirin Mata)

42-Dr. Nazifi Yunus Jos da Alaramma Faruq Jada Tambuwal, Jos plateau

43-Mal. Abdulwahid Abubakar Sulaiman da Alaramma Umar Ibrahim, Villa A Abuja

44-Dr. Ali Yunus, Usman Bn Affan Gado Kaya Kano

45-Dr. Sani Suleiman Jibia Da Alaramma Ahmad sani Sulaiman Masjid Mamman Barda, katsina

46-Dr. Uthman Sani Haruna da Alaramma Yusuf Ibrahim Jalo, Lafiya, Nasarawa

47-Dr. Zubairu Madaki da Alaramma Kabir Abdullahi Bauchi Masjid Umar bn Al khattab, Kofar Wambai, Bauchi

48-Dr. Adam Usman Nengere da Alaramma Usman Barikin Ladi, Jumeta, Adamawa

49-Mal. Abdulrahman Muhammad, Kano state University Wudil, Kano

50-Mal. Abdul Razak Yahaya Haifan da Alaramma Kabir Hussaini Daura, Gwagwalada, Abuja

51-Mal Abdullahi Umar Zaria da Alaramma Mustapha Shuaibu Garki Village, Abuja

52-Mal. Moh'd Auwal Abubakar (M/gaskiya) da Alaramma Aliyu Ibrahim P**i, Fed. Min. of Works Abuja

53-Mal. Abdullahi Karshi da Alaramma Salihu Gumi, Villa B Abuja

54-Mal. Adam Isah Sahibul Kuwa, Dakkwa Abuja

55-Mall. Aliyu Ladan da Alaramma Tukur Jakada, Life Camp Abuja

56-Mal. Umar Sadiq Jega da Alaramma Yusuf Suru, Kamba Kebbi

57-Dr. Abdallah Umar Gadon Kaya da Alaramma Baba Lawal, kanbarikin,(Water Board ) Kumo, Gombe

58-Mal Abdulrahman Alzamfari da Alaramma Muhammad Kabir Yunus/Abdulbasid Surajo Gusau, Masjid Muhajirun Wal-ansar Dutsen Alhaji, Abuja

59-Mal. Tajuddeen Imam da Alaramma Murtala Muhammad Prince & Princes, Abuja

60-Mal. Aliyu Saeed Gamawa da Alaramma Saeed Adamu, People Bank Masjid Gamawa, Bauchi

61-Mall. Ibrahim Idris Zakariyya da Alaramma Mujtapa Shuaibu Yusuf, Tirden Fulani, Bauchi

62-Mal. Nazifi Hashim da Alaramma Dauda Alkasim Wukari, Alkaleri Bauchi

63-Shk. Ahmad Tijjani Yusuf Guruntun da Alaramma Mahmud Zaharaddin, Masj S19 Dutsen Tenshe Bauchi

64-Barr. Sheikh Garba Hassan Alaramma Abduljalal Usman, Masjid Abu Huraira New GRA Bauchi

65-Sheikh Sulaiman Yusuf Bashir da Alaramma Abubakar Usman T/former, Masallacin Adamu Jumba Housing Estate, Bauchi

66-Sheikh Babangida Sulaiman da Alaramma Adam Adam Muhammad, Masallacin Juma'a na Gwallga (Karatun Safe) Bauchi

67-Sheikh Kabiru Ahmed Azare da Alaramma Sulaiman Abdullahi, Masjidus Sunnah Sardauna Road Azare, Bauchi

68-Imam Muhammad Manga Abba Zadawa da Alaramma Idris Ibrahim Kolo, Masallacin Jibwis Zadawa Misau, Bauchi

69-Alkali Ridwan Abubakar Alaramma Yahaya Tudun Maliki, Masallacin Jibwis Fed. Lowcost Misau, Bauchi

70-Imam Magaji Bappa Sulaiman da Alaramma Aliyu Ahmad, Masallacin Ali bin Abi-Talib gandum Wambai A. Bauchi

71-Imam Ibrahim Adam Narabi, Masallacin Jibwis Magam Gumau, Bauchi

72-Sheikh Ibrahim Haruna Dambam da Alaramma Aliyu Ahmad, Masallacin Jibwis Dambam, Bauchi

73-Sheikh Yakubu Isma'il da Alaramma Ibrahim Musa, Masallacin Jibwis Dass, Bauchi

74 Sheik Haruna Musa Riban Garmu da Alaramma Sani ishaq, Masallacin Jibwis Kirfi, Bauchi

75-Sheikh Yunusa Abubakar, Masallacin Haudah Jibwis Jama'are, Bauchi

76-Sheikh Musa Yakubu da Alaramma Rufa'I Abdulqadir, Masallacin Jibwis Kafin Madaki Ganjuwa, Bauchi

77-Imam Habibu Garba Baima da Alaramma Abdulkarim Muhammad Baima, Masallacin Jibwis Warji Bauchi

78-Sheikh Sadisu Yusuf Konkiyal da Alaramma Mal. Yakubu Sabo, Masallacin Jibwis Darazo, Bauchi

79-Sheikh Muhammad Albashir Ningi da Alaramma Sulaiman Muhammad, Masallcin College of Health and Tech Ningi, Bauchi

80-Imam Abdurrahman Ibrahim idris da Alaramma Huzaifa Yakubu Sambo, Masjidus Sahaba New GRA Bauchi

81-Sheikh Dalhatu Babaji Mball da Alaramma Yusha'u Adam, Masallacin Jibwis Burga Tafawa Balewa, Bauchi

82-Sheikh Salisu Isa Saidu Kurgui da Alaramma Sale Abdussalam, Masallacin Jibwis Sabon Kaura, Bauchi

83-Sheikh Mahmud Ibrahim Shira, Masallacin Jibwis Ibrahim Bako, Bauchi

84-Sheikh Umar Baba Hanafari da Alaramma Yahuza Aliyu, Masjid Abubakar Gumi, Bauchi

85-Dr. Abdullahi Jaji da Alaramma Hussaini Alhaji Bauchi, Masjid Usman Bn Affan, Bauchi

86-Mal. Anas Adamu da Alaramma Faisal Abdulmumin, Masjid Umar Bn Alkattab, Bauchi

87-Mal. Tanimu Tahir da Alaramma Tahir Ahmed Alkaleri, Masjid Jibwis Alkaleri, Bauchi

88-Mal. Aliyu Yau Assurubun da Alaramma Dauda Ibrahim Katagum, Masallacin Jibwis Zaki, Bauchi

89-Sheikh Muhammad Bukar Albagawy da Alaram Bako Bello, Ningi Bauchi

90-Mal. Yaqub Isah da Alaramma Adam Muhammad, Kwaya kusar, Borno

91-Mal. Abba Musa da Alaramma Aminu Ibrahim Potiskum, Maiduguri, Borno

92-Shk. Muhammad Abubakar Kachalla da Alaramma Ahmad Isma’il, Maiduguri Borno

93-Mal. Zainu Usman Baban Tine, NNPC Kaduna

94-Prof. Ahmad Jafar Abdulmalik da Alaramma Tajuddeen Muhammad, Masallacin Jumaa na Sheikh Jaafar U/Dosa, Kaduna

95-Imam Saidu haruna Kankiya, Masallacin Jumaa na Kabala Costing, Kaduna

96-Ustaz Nura Mujahid da Alaramma Sulaiman Musa, Masallacin Jumaa na kwaru, Kaduna

97-Dr. Tukur Adam Almannar, Masallacin Juma'a na Almannar, Kaduna

98-Imam Ishaq Ibrahim da Alaramma usman Yusuf, Sa'ad Bin Abi Waqqas hayin banki, Kaduna

99-Mal. Abubakar Buba Luwa da Alaramma Abubakar Muhammad Rabiu, Sheikh Abubakar Muh'd Gumi Jumaat Masjid Kawo, Kaduna

100 Alkali Tahir Lawal Abubakar.

KU SHIGA WANNAN LINK DOMIN GANIN SAURAN SUNAN MALAMAI NA NAIJERIYA DA KASASHEN AFURKA.

https://jibwisnigeria.org/Tafseer/Applications.html

Domin karin bayani game da shiga website din jibwis ku tuntubi wadannan lambobi.
08025178750
08061330072

Sanarwa daga ofishin sakataren JIBWIS na kasa, Sheikh Dr. Kabiru Gombe, ta ofishin shugaban JIBWIS Social Media na kasa, Alhaji Ibrahim Baba Suleiman.

Jibwis Nigeria Social Media

FALALAN BIYAN BUKATAUN MUTANE DAGA BAKIN ANNABI (SAW).NA FARKO (1)-ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢﻣﻦ ﻳﻜﻦ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺔ ﺃﺧﻴﻪ ﻳ...
05/04/2021

FALALAN BIYAN BUKATAUN MUTANE DAGA BAKIN ANNABI (SAW).
NA FARKO (1)-
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻣﻦ ﻳﻜﻦ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺔ ﺃﺧﻴﻪ ﻳﻜﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ .
( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ )
Manzon Allah (saw) Yace:-
Duk Wanda Ya kasance Cikin Biyan Buqatar Dan Uwansa, Allah Zai Kasance Cikin Biyan Buqatar Sa
NA BIYU (2)-
* ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻮﻥ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﻓﻲ ﻋﻮﻥ ﺃﺧﻴﻪ،
‏( ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ )
Manzon Allah (saw) Yace:
Allah Yana Cikin Taimakon Bãwa, Matuqar Bãwa Yana Taimakon Dan Uwansa
NA UKU (3)-
* ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﻷﻥ ﺃﻣﺸﻲ ﻣﻊ ﺃﺧﻲ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ ، ﺃﺣﺐّ ﺇﻟﻲَّ ﻣﻦ ﺃﻥ ﺃﻋﺘﻜﻒ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺷﻬﺮﺍً،
( ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ )
Manzon Allah (saw) Yace:
Wallahi In Kasance Cikin Biyan Buqatar Dan Uwana Musulmi, Yafi Soyuwa Agareni Akan Inyi E'itikhãfi Na Wata Daya A Masallaci
NA HUDU (4)-
* ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻭﻣﻦ ﻣﺸﻰ ﻣﻊ ﺃﺧﻴﻪ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ ﺣﺘﻰ ﻳﺜﺒﺘﻬﺎ ﻟﻪ، ﺛﺒﺖ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻗﺪﻣﻪ ﻳﻮﻡ ﺗﺰﻝ ﺍﻷﻗﺪﺍﻡ،
( ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ)
Manzon Allah (saw) Yace:
Duk Wanda Ya Tafi Tare da Dan Uwansa Musulmi Cikin Biyan Buqatar Sa, Har ya Tabbatar Masa Da Buqatar Sa, Allah Zai Tabbatar da Diddigen Sa Ranar da Digadigai Zasu Zame (Akan Siradi)
NA BIYAR (5)-
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺃﻥ ﺗﺪﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﺃﺧﻴﻚ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﺳﺮﻭﺭﺍً، ﺃﻭ ﺗﻘﻀﻲ ﻋﻨﻪ ﺩﻳﻨﺎً، ﺃﻭ ﺗﻄﻌﻤﻪ ﺧﺒﺰﺍً،
( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ)
Manzon Allah (saw) Yace:
Mafificin Aiki Acikin Ayyuka Shine: Ka Sanya Farin Ciki ga Dan Uwanka Mumini, Ko Ka Biya Masa Bashin da Ake Binsa, Ko Ka Ciyar dashi Abinci
NA SHIDA (6)-
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻣﻦ ﻳﺴﺮ ﻋﻠﻰ ﻣُﻌﺴﺮ , ﻳﺴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﺍﻵﺧﺮﺓ،
( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ)
Manzon Allah (saw) Yace:
Duk Wanda Ya Sauqaqa Ma Wanda Yake Cikin Qunci, Allah Zai Sauqaqa Masa Acikin Duniya da Lahira
NA BKWAI (7)-
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻣﻦ ﺳﺮﻩ ﺃﻥ ﻳﻨﺠﻴﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﻛﺮﺏ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻠﻴﻨﻔﺲ ﻋﻦ ﻣﻌﺴﺮ،
( ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ)
Manzon Allah (saw) Yace:
Duk Wanda Yake Son Allah Ya Tseratar dashi daga Quncin Ranar Alqiyamah, To ya Yaye Damuwar Wanda Yake Cikin Tsanani.
NA TAKWAS (8)-
IBNUL QAYYIM (RH) YACE:
إن في قضاء حوائج الناس
لذة لا يعرفها ‏إلا من جربها
Lallai Acikin Biyan Buqatun Mutane Akwai Wani Dandano, da Babu Wanda Yasanshi Sai Wanda Ya Jarraba
فافعل الخير مهما استصغرته
فإنك لا تدري أي حسنة تدخلك الجنه
Ka Aikata Alkari ga Mutane Duk Yadda Kake Ganin Qanqantar Sa,
Domin Baka San Wani Aikine Zai Shigar Dakai Aljannah ba.
NA TARA (9)-
قال رسول الله صلى الله عليه وسلام
خير الناس من ينفع الناس [متفق عليه]
Manzon Allah (saw) Yace:
Mafi Alkairi Daga Cikin Mutane, Shine Wanda Mutane Ke Amfanuwa Dashi.
Yaa Allah Kasa Mu Zamto Alkairi ga Mutane, Ba Sharri A Garesu ba.

05/04/2021

Walkiya:
✍ Prof. Mansur Sokoto, mni.
22 Sha'aban 1442H (05/04/2921)

Hassada
Mahasadi duk tsawon rayuwarsa yana cikin damuwa. Yana kallon arzikin mutane a cikin bakin ciki da bacin rai; shi ba zai iya kwace masu ba, kuma shi ba zai iya samu ba. Daga karshe da bakin ciki yake mutuwa.
Allah ya kiyashe mu daga hasada.

LABARU CIKIN HOTUNA:Kai Tsaye Daga Tafseer Foundation Inda Ake Gudanar Da Taro Akan Cikar Shekaru 30 Da Fara Tafseer Na ...
05/04/2021

LABARU CIKIN HOTUNA:

Kai Tsaye Daga Tafseer Foundation Inda Ake Gudanar Da Taro Akan Cikar Shekaru 30 Da Fara Tafseer Na Jos North Wanda Marigayi Sheikh Ibarhim Bawa Mai Shinkafa Ya Assasa Tareda Karrama Wasu Daidaiku Da S**a Bada Gudunmawa Don Ganin Wannan Tafseer Ya Kawo Ga Yau.

Haka An Kafa Gidauniya Ta Neman Tallafi Domin Gina Masaukin Maluma Masu Zuwa gabatar da Tafseer aJos North, Da Neman Tallafin Mota Ta Zirga Zirga Harma Da Kayan Sauti Na Zamani Domin Cigaba Da Isar Da Sakon Allah.

JIBWIS Social Media Plateau State Directorate...
3/4/2021..

03/04/2021

Forget about HND, BSC, MSC, PhD..if you lack Islamic Knowledge you are still an Illiterate!!

SUNNAH SAK BID'AH SAM!!
01/04/2021

SUNNAH SAK BID'AH SAM!!

Hotuna: Daga As-salam Global University (AGU) Yayin da, Tawagar Jagororin kamfanin T-Grid Ltd" suke kawo ziyarar aiki da...
29/11/2020

Hotuna: Daga As-salam Global University (AGU) Yayin da, Tawagar Jagororin kamfanin T-Grid Ltd" suke kawo ziyarar aiki daga, Babban ofishinsu dake Abuja.

Muna rokon Allah yakara mana nasara Amin.

Daga: Baffa Maina Hadejia

KAI TSAYE DAGA GARIN HADEJIA , JIHAR JIGAWA 2020!Shugaban kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau tareda du...
10/10/2020

KAI TSAYE DAGA GARIN HADEJIA , JIHAR JIGAWA 2020!

Shugaban kungiyar Izala ta Kasa Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau tareda dukkan masu ruwa da tsaki na kungiyar ayau Asabar ya jagoranci bude katafariyar Sakateriya wadda aka ginata akokarin su na assasa Jami'ar "As-salam Global University" dake garin Hadejia a Jihar Jigawa, taron daya fara da ranar yau Asabar 10/10/2020 zaicigaba da wa'azin kasa daren yau kuma agobe Lahadi inshaallah mai alfarma sarkin musulmi zai yagoranci tawagar kungiyar da sauran al'uma musulmai wurin kafa tubalin ginin jami'ar dake da nisan kilomita 7 daga garin na Hadejia kan hanyar kano. Allah ya kara dauka ka Musulunci da musulmai a fadin duniya baki daya.

10/10/2020

INNA LILLAHI WA"INA ILAIHI RAJIUN ALLAH YAYIWA ABDULMALIK JAFAR MAHMOOD ADAM RASUWA YAU A HATSARIN MOTA ALLAH YA GATARTA MASA

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis WASE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share