Min of Lands and Survey Ktn State

  • Home
  • Min of Lands and Survey Ktn State

Min of Lands and Survey Ktn State Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Min of Lands and Survey Ktn State, Media, .

16/09/2023

MLPP

16/09/2023

Press Release

Stakeholders Consultation Meeting on Preparation of Strategic Regional Development Plan for the North West Geo-political Zone has been held in Katsina.

The Meeting which was organised by Pragmatic Solutions Consult was participated by MDA's and other stakeholders in Lands and town planning among others.

The National Coordinator Pragmatic Solutions Consult Limited Tpl. Kabir Yari who presented a preliminary findings of the Master Plan of the North West Geo-political Zone said the essence of meeting is to discuss with the the stakeholders on area of priority in the State

Tpl. Kabir Yari who said the Regional Development Plan will cover all Seven North Western State,said at the end of the meeting, the submission of the stakeholders will be properly considered in the Plan.

The State Commissioner Ministry of Lands and Physical Planning,Dr.faisal Umar Kaita said the move by Federal government is in-line with Governor Dikko Radda's led government efforts in ensuring Regional integration for peaceful coexistence and economic development.

Dr.faisal Umar Kaita pointed out that, the State government is determined to update it Regional and State Master Plan to serve as guide in Physical development.

The Land's Commissioner confirmed that the Ministry will budget 2024 fiscal year for the development of Master Plan of Katsina, Funtua and Daura and to revive the department of Urban and Regional Planning of the Ministry proper implementation of the issues regarding Town Planning in the State.

He emphasised that,the Ministry would use its on Staff to work out the development plan to ensure ownership of the data collected.

The Commissioner further revealed that, with the enactment of the law for the establishment of Katsina Geographic Information Services, issues regarding improper planning will be addressed in Katsina State.

Dr.faisal Umar who appreciated Governor Dikko Radda for his political will in Lands administration in the state.

29/04/2023

WASIKA ZUWA GA KWAMITIN LAFIYA NA GWAMNA MAI JIRAN GADO A JAHAR KATSINA

Assalam alaikum wa Rahmatullah....

Dubun gaisuwa da girmamawa ga dukkan illahirin Membobin wannan kwamiti a karkashin jagorancin Halliru Lawal Dutsinma.

Da farko ina taya ku murna da Allah ya zabe ku daga cikin al'ummar Jahar Katsina kusan mutum miliyan shida da doriya,aka daura maku alhakin kawo mafita ga al'ammuran kiwon lafiya da gwamnati mai jiran gado a Jahar Katsina ta kudiri aniyar yi.A hannu daya kuma kuna bukatar addu'ar Allah ya sa maku hannu,don samun nasara ko akasi, da ba a fata ya dogara kacokam kan aikin wannan kwamiti naku.

Ba karamin hangen nesa bane Gwamna mai jiran gado ya yi ba, na bude kofar samun shawarwari, ba ga bangaren kiwon lafiya ba,har da sauran bangarori. Fatar duk wani dan Jahar Katsina ita ce,wadannan kwamitoci su zamo silar samun SABUWAR JAHAR KATSINA da iznin Allah, wanda shi ne taken gwamnatin Dikko/Jobe a yayin yakin neman zabe.

Dalili na na yanke shawarar rubuta wannan wasika da za ta kunshi wasu shawarwari ga kwamitin kiwon Lafiya shi ne, ina da abinda zan iya bayarda gudummuwa, don akwai abinda nike ganin madamar zai ci gaba da tafiya a haka da k**ar wuya a iya samun mafitar da duk wata gwamnati take ta hankilon samu,tun bayan da Nijeriya ta samu 'yancin kanta.

Domin a Jaha irinta Katsina mutum zai yi mamakin yarda harkokin kiwon lafiya ke tafiya rai-kwakwai-mutu-kwakwai duk da kokarin da gwamnatoci da daidaikun jama'a suke yi bakin gwargwado na samarda gine-ginen Asibitoci,Kayan aiki,Likitoci,Malaman jinya da sauran abubuwan da zasu inganta bangaren, amman har haka marasa lafiya, musamman masu karamin karfi dake zuwa cibiyoyin kiwon lafiya,har da ni mai rubutun bamu samun biyan bukatu daidaida yarda tsarin da doka ta tanada.

Don haka a wasu bangarori na Jahar Katsina,ba batun rashin Ma'aikatan kiwon lafiya ko kayan aiki ne yake kawo koma baya a cibiyoyin kiwon lafiyar ba,face wadannan dalilai.

Zargin Karacin sa-ido da tsawatawa daga mahukunta,rashin bin diddigin yarda ake tafiyar da ayyuka a Asibitoci gami da tabarbarewar alaka da ake samu a tsakanin Malaman kiwon lafiya da marasa lafiya matsaloli ne da ba zasu taba barin a samu nasarorin da ake bukatar cimmawa ba a kiwon lafiyar al'umma, domin duk Kudaden da gwamnati zata cigaba da zubawa, madamar ba za a shawo kan wannan matsaloli ba masu alaka da da'ar Ma'aikata,to matsalolin mutuwar mata masu juna biyu da yara kanana,musamman ba zasu kare ba,domin tuni Mata sun fara kauracewa Asibitoci saboda halin rashin tabbas da suke tsintar kansu a hannun Ma'aikatan kiwon lafiya

Idan har wannan kwamiti mai albarka ya yi la'akari da wannan matsala,tare da bayarda shawarar daukar mataki na sa-ido ga yarda Asibitoci suke tafiyar da ayyuka da yarda suke hulda da marasa lafiya lallai an cimma wani kaso mai rinjaye ga bukatar da ake son cimmawa na inganta bangaren kiwon lafiya, domin akwai inda tsawatawa kawai gwamnati zatayi, a samu mafita,don nasan shugabanni da dama,sun jaraba kai ziyarar ba zata a Asibitoci kuma sun ci karo da irin wannan matsalar.

Yin wannan maganin matsalolin,kaso ne mai tsoka na matsalolin da ake ganin suna tarnaki ga cimma muradun gwamnati duk tsawon shekarun nan.

Akwai hujjoji da dama na zargin rashin kyakkyawar alaka a tsakanin Malaman kiwon lafiya da marasa lafiya a Asibitoci, wanda ada Asibitocin karkara ne s**a yi kaurin suna,amman yanzu zarge-zargen rashin yin daidai a Asibitocin da ke Jahar nan harda wadanda suke mallakin gwamnatin tarayya ya zamo ruwan dare.

Wannan yasa tuni mata dayawa sun kauracewa Asibitoci musamman a yayin haihuwa saboda yanayin da suke cintar kansu a hannun ungozomomin Asibitoci. Kodayake idan Mace na da yan'uwa a Asibitin takan iya Kiran abokan aikinta ta ce ma ta ga amanar yan'uwata nan.

Bincike na ya tabbatar da cewar idan baka da wani wanda zai yi magana akanka ko dai ba zaka samu kulawar da kake so ba ko kuma ka samu kulawar a lokacin daka galabaita,don har ni wannan matsalar ta faru da ni,a lokacin da na yi hadari aka kaini Asibitn Kashi ta Janaral Amadi Rimi dake nan Katsina,sai da na dauki awoyi jini na zuba daga jiki na,kuma daga karshe ban samu kulawar ba,sai dai wata Asibitin aka ta fi dani, don ceton rayuwata

Irin wannan matsalar bata tsaya ga Asibitoci mallakin gwamnatin jaha ba,domin na ga ma'aikacin Asibitin gwamnatin tarayya ta Katsina ya je ya biya kudinsa a asibiti mai zaman kanta saboda ya kasa samun abinda yake so a Asibitin da yake aiki,saboda shi ba bangaren masu bayarda lafiya ya ke ba.
Idan da wannan kwamiti zai zurfafa bincike zai gano lallai akwai wuraren da rijiya ke ba da guga ya hana,kuma lallai ko nawa gwamnati zata kashe idan ba canza dabi'un Ma'aikatan kiwon lafiya ba sai an rasa masu zuwa Asibiti.

Duk da ba duka s**a taru s**a zama daya ba,amman karuwar da suke yi ita ce abin tsoron, kodayake akwai Asibitin da bincike ya nuna cewar rashin samun walwala da jin dadi daga mahukuntan Asibitocin yake sanya ake huce haushi a kan marasa lafiya.

Daga karshe ina fatan wannan kwamiti zai bincika tare da duba irin shawarwarin da za a baiwa gwamnati na kokarin da take yi na samun mafita ta wannan fuska,domin anan Gwamna mai jiran gado ya yi nasa,naku ya rage tare da raka shi da addu'ar yin amfani da shawarwarin da kuka ba da.
Ina rokon Allah ya sa wannan aiki da zaku yi shi ne silar ceto bangaren kiwon lafiya.

Waslam.....

Naku-:Yakubu lawal
Dan Jarida
Jami'in Hulda da Jama'a

25/02/2023
31/12/2022

DA MA NI DAN TAKARA NE!

Ra'ayin Yakubu Lawal

'Daya daga cikin Adiban Marubutan Wakokin Turanci na Nijeriya a salon Pigin EZENWA OHAETO a wakarsa mai taken 'I wan bi President'ya yi irin wannan shaguben da na yi take da shi, wanda nasan hujjoji sune zasu tabbatar da hakan.

Duk da dai masanin mulki da kimiyyar siyasa Nicolas Macvelley yace ga dan siyasa da sandar hannunsa yake rama bugu, wato(Might is his right)salon da yan takara ke amfani da shi da sakon dake kunshe cikinsa bai isa ya sayarda dan takara ba,tare da jan ra'ayin masu zabe, ko dai don al'umma/masu zaben sun gaji da jin irin sakon ko kuma salon aika sakon ya zama tsohon yayi,musamman wannan lokaci da al'umma s**a fi son kwai a baka fiye da kaza a akurki.

Duk da cewar,a kakar zabe ta bana masu takara daga Jam'iyu dabam-daban sun yi kokarin gane cewar zamani ya fara canzawa sun gane ba a cika bin Yarima a sha kida ba,abin nufi kowane dan takara yanzu ya na lika hotonsa da tambarin Jam'iyarsa ne kawai, sabanin abaya da wasu ke hada hotonansu da wasu da suke ganin za su zamar masu albarkacin kaza,kadangare ya sha ruwan kasko,amman sakon iri daya ne da na baya, kodai na yi alkawarin zan yi...
ko kuma zan yi abinda wane ya kasa yi da dai sauransu.

DA MA NI DAN TAKARA NE! To da sai in yi la'akari da abinda na ke jin al'umma/masu zabe na koke da shi game da salon mulkin da ake ciki,in yi kwaskwarima in fiddowa al'umma,tare da yin amfani da shi a duk lokacin da na hau bisa munbarin yakin neman zabe,don kaucewa maimaita abinda a kan kushe.
Alal misali mafi akasarin abinda masu zabe suke koke da zargin mahukunta sune tarayya da'yan hana ruwa gudu,rashin hukunta masu laifi,rashin daukar mataki kan matsaloli a zahiri,rashin bin kadi a kan wadanda s**a daurawa aikin al'umma da sanyawa kowa ido ya yi abinda ya yi masa dadi da mak**antansu, duk da dai zargi ne irin na mai mulki da wanda ake mulka, domin suma masu mulkin suna cewa sunyi abin a yaba da yak**ata.

Kodayake,akwai yiwuwar salon siyasar ne ya nuna, yin alkawarin dorawa daga inda wanda ya rikewa dan takara kan macijin yake wasa da bindin, to amman DA MA NI DAN TAKARA NE,to ba zan yi alkawari ba tunda wuyar cikawa gareshi,sai in cewa al'umma su zabe ni tare da ta ya ni addu'ar samun nasara cikin sauki da sauke nauyin mulkin cikin sauki,in anyi nasara,tunda a fili take, ba tarurun taron yakin zabe ke haifar da mafi rinjayen nasara a zabe ba,don kila duk sojojin baka ne da ake wa kirarin sun fi mai katin kada kuri'a.

To amman wani hanzari ba gudu ba,zan so al'umma su goya mani baya, don ka da su yi ta zundena tare da hadani da wanda ya yi mani hanyar zama dan takarar, ya k**a ni da laifin rashin yin alkawari irin nasa na cewa zan dora daga inda ya tsaya,domin akwai yiwuwar daga inda shi (mai gidan nawa)ya tsaya, watakila ba nan al'umma ke bukatar a fara mulkarsu ba.

DA MA NI DAN TAKARA NE! Zan yi kokarin al'umma su fahimci manufata kafin manufar iyayen gidana,zan tabbatar na gamsar da wadanda nike tunanin zasu zabe ni,ba ki dayansu ba wadanda na tara a wurin gangamin yakin neman zabe ba kadai,saboda ba kowane mai halartar yakin neman zaben ba ke iya zabe na,sannan zan yi kokarin fahimtar matsalar da wanda nike son in gada ya fuskanta ko da kuwa ba Jam'iyarmu daya ba, don kauce ma ta, daga nan sai in barwa Allah sauran tun da shi ke bayarda mulki ga wanda ya so, a kuma sanda ya so.

Kash!!! Da ma ace shugannin da ke da magada daga cikin Jam'iyunsu za su yi jarunta irinta Gwamnan Jahar Kaduna a lokacin kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Gwamna na Jam'iyarsa?" A inda Gwamnan yace ina kaddamar maku da Malam Uba Sani a matsayin dan takarar Gwamna,ku zabe shi mutanen kirki ne, harma ya fini kirki,kuma karku tuhumeshi a kan kuskuren da na aikata a yayin tafiyar da mulkina. Sai dai ina neman ku yafe mani nima a kan kurakuren da na yi."Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan labari.

Irin wannan salon aika sako,salo da ka iya canza tunanin makiyi ya koma masoyi,kuma sabon salo ne a siyasar Nijeriya.

To tunda yanzu NI BA NI CIKIN 'YAN TAKARA sai mu taru mu fahimci, miye hakkinmu,miye hakkin wadanda zamu zaba,in har matsalolin da muke zargi ba laifinmu bane, don gujewa gudun da babu mafita, wanda karshensa safkon bubukuwa.

Alkalamin Yakubu Lawal
Dan Jarida
Jami'in Hulda da Jama'a

31/12/2022
03/12/2022
11/11/2022

_Ya Allah kaine mafi tausayin masu tausayi, mafi karamcin masu karamci. Ya Allah don sunayen ka tsarkaka, ka kyautata rayuwar mu ta duniya, da lahira ka tsare mu daga zafin fitan rai, azabar qabari, zafin ranar qiyamah ka bamu ikon tsallake siradi sannan kasamu a aljanna ba tare da hisabi ba. Kai mai ikone akan haka Ameen ya Hayyu ya Qayyum._
*Juma'at Mubarak *

23/03/2022

TPL.Usman Nadadq Ngs.Rtp.NATE Kwarya Ce Dai-Dai Gurbinta.......

SHARHI KAN SAMARDA SABON BIRNI DA MA'AIKATAR KASA DA SUFIYO TA JAHAR KATSINA ZA TA YI.

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya bai yi shinge ko iyaka akan cewar sai wanda ya kware a Ma'aikata ko Sashe ake nadawa ba mukami a matsayin Mamba na majalisar zartaswa a matakin Jaha ko Tarayya.

Sai dai idan aka yi gamo-da-katar abin ya fi haifar da mai ido idan aka baiwa mutuminda ya fi kwarewa a Ma'aikata ko Sashe da aka nada shi ya Jagoranta.

Ma'aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina, na daga cikin wuraren da s**a dace da kwararren Jami'in Tsara Birane(Town Planner) da ke shugabantar Ma'aikatar, wato Tpl. Usman Nadada.

Wannan dama da Tpl.Usman Nadada ya samu bayan shekarun da ya dauka yana aiki mai alaka da tsara birane tun bayan kammala karatunsa na digiri na daya da na biyu,wanda har ya kai shi ga rike kujerar Janar Manajan Hukumar Tsara Birane da 'Yankuna na Jahar Katsina na tsawon shekaru ya sanya yake da ra'ayi na ganin cigaban harkokin da s**a jibanci Kasa da Sufiyo.

Kudurori da Manufofin da Tpl.Usman Nadada ya hau mukamin kwamishinan Ma'aikatar da su na tunanin dorawa daga inda wanda ya gada ya tsaya a kan inganta tsarin Kasa sune sirrin nasarorin da ya ke cigaba da samu a Shugabantar Ma'aikatar.

Wannan tsari kuwa shi ne,sarrafa Kasa kai tsaye a maimakon rarrabawa ba tare da sarrafawa ba.

A karkashin wannan tsari ne aka yi tunanin samarda wani sabon birni da zai kunshi kayan more rayuwa dabam-daban da mutanen da za a haifa a sabuwar duniyar za su amfana da su.

Wannan sabon birni da za a kafa a Arewacin garin Katsina, a kan hanyar Katsina zuwa Jibia an rada masa suna'KATSINA RACE COURSE VILLAGE'
Idan wannan birni ya kammalu zai kunshi Gidaje, Makarantu,Massallatai gami da Filayen Wasanni dabam-daban, musamman na Wasannin tseren Dawaki da na Kwallon Dawaki.

Shedar yiwuwar wannan aiki tuni Ma'aikatar Kasa ta yi yarjejeniya da wani kamfanin tuntuba na wasu kwararrun masu ilmin tsara birane mai suna'BIN-HAJJ CONSULT' da ya samarda taswira ta zahiri da bayyana kwarangal din birnin baki daya.

Tuni wannan taswira ta samu sambarka da amincewar Maigirma Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari da Maimarbata Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da sauran masu ruwa da tsaki.

Wani abun da ya k**ata mutane su sani shi ne tuni an fara rattabawa takardun yarjejeniyoyi hannu da kamfanonin da ke huldar samar da muhalli(Developers) don cigaba da tabbatuwar samuwar wannan sabon birni.

Irin wannan shirye-shirye wadanda duniyar cigaba s**a yi nisa ga aiwatar da su,a kasashe irin namu na ifrikiyya ba a cika samun aiwatar da su dari bisa dari ba.

Don haka, kaifin basira da hikima ta Kwamishinan Kasa da Sufiyo a Jahar Katsina Tpl.Usman Nadada ya yi amfani da kwarewar da ya ke da ita ta wannan fuska ya hannanta kula da tafiyar ga Kamfanin BIN-HAJJ CONSULT don haka ta cimma ruwa.

Wani sabon salo da Tpl. Usman Nadada ya yi wa wannan aiki tare da shawarar abokan aikinsa da kuma amincewar gwamnati shi ne wannan birni shi zai samarda kansa da kansa.

Yanzu nan da wasu 'yan lokutta da yardar mai duka sabon birni zai wanzu a nan Katsina,sai dai sanin karkashin wace gunduma zai kasance, muna jiran masana tsare-tsaren iyakoki su bayyanas.
Ko ba komai, ajiye kwarya a bisa gurbinta ta kara tabbata a Ma'aikatar Kasa da Sufiyo ta Jahar Katsina

Alkalamin: Yakubu Lawal
Dan Jarida
Jami'in Hulda da Jama'a.

12/02/2022
02/12/2021
Today being 2nd Dec 2021.Ministry of Lands and Survey, Katsina State led by its Commissioner Tpl. Usman Nadada has prese...
02/12/2021

Today being 2nd Dec 2021.
Ministry of Lands and Survey, Katsina State led by its Commissioner Tpl. Usman Nadada has presented its proposal for 2022 fiscal year

07/10/2021

The Board Members and Management of Teachers Service Board have inspected the on-going construction project of their permanent site within Ja Abdulkadir secretariat
The project is being carry out by Green House Company Katsina under Public Private Partnership between the Company and Katsina State government
The T.S.B Chairman Alhaji Umar Audi Kofar Bai who led other Members were conducted round the project by the Project Manager Q.S Kabir Gambo and Engineer Ashahabu Al-qaseem
The Project is a one Storey building consisting of offices attached with Public Conviniences for the Chairman,his board Members, Management staff as well as other staff.
Other facilities nclude Conference Hall, waiting room, reception, parking pavilions,generator room,secret and open registries and land scapping of the premises among others
Briefing the Chairman and other Members on the Project, the Project Manager Q.S Kabir Gambo who said they are determine to ensure good quality work noted that three parking spaces are earmarked for the conviniency of workers
While assuring timely completion,the project Manager said already a borehole was constructed for the supply of water

The Engineer of the Green House Company, Engineer Ashahabu Qaseem who said the project has reached over fourty percent compeletion stage,assured that contractual agreement would be adhere strictly
Responding after the Inspection, the T.S.B Chairman, Alhaji Umar Audi Kofar Bai expressed satisfaction over quality of work of the project
Alhaji Umar Audi described the provision of a permanent and a conducive working place to the Board as commendable
He noted that, the place would be more convinient to the Board, considering the fact that, the present place is not design for their activities and is overtaking by itinerant traders
# # # # # # #
Yakubu Lawal... PRO. MLS

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Min of Lands and Survey Ktn State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share