AREWA YOUTH FORUM

  • Home
  • AREWA YOUTH FORUM

AREWA YOUTH FORUM Mun kirkiro wannan shafin ne domin mutanen Arewa

Democracy Day StatementZulum: Defying Boko Haram For 13 Years Makes Northeast Hero of 23-Year Democracy The people of th...
12/06/2022

Democracy Day Statement

Zulum: Defying Boko Haram For 13 Years Makes Northeast Hero of 23-Year Democracy

The people of the northeast, particularly those in Borno State, have spent more than half of Nigeria’s 23 years of uninterrupted democracy, showing “incredible resilience” against vicious attempts by Boko Haram insurgents to undermine democratic institutions, Governor Babagana Umara Zulum said on Sunday.

Zulum described the people of Borno State and rest of the northeast as deserving of being amongst heroes of Nigeria’s 23 years of sustained democracy.

Zulum, who is Chairman of the Northeast Governors’ Forum, conveyed these in his democracy day message, made public by his spokesman, Malam Isa Gusau.

Below is Zulum’s message:

1. It is now 23 uninterrupted years since Nigeria returned to democratic rule back in 1999. In those 23 years, societies across the country have witnessed different levels of progress and challenges.

2. In those 23 years, the people of Borno State and other parts of the northeast, have since July 2009, ceaselessly resisted groups of extremely violent insurgents with the determination to wreck massive havoc on communities, pursuing the ultimate objective of bringing down democratic institutions in Nigeria, and replacing them with violent sovereign doctrines.

3. From 2009 to date, which is about 13 years, thousands of our youthful fellow citizens, amongst them women and even old men, have devoted their lives to supporting armed forces in fighting Boko Haram and stopping the insurgents from undermining Nigeria’s sovereignty and our democracy.

4. In these 13 years, countless number of these citizens as members of ‘Civilian JTF, hunters and vigilantes, have made sacrifices including giving their lives at battle fronts, to protect fellow citizens and to preserve our nation’s sovereignty and democracy.

5. These fallen volunteers alongside those currently in front lines and all citizens of the northeast eminently qualify to be named amongst the heroes of Nigeria’s 23 years of uninterrupted democracy.

6. We will forever be grateful to the volunteers for their sacrifices just as we should regularly remember them in our prayers as we seek end to the insurgency that is now on comparative decline.

7. Survivors of our fallen volunteers have earned our help as a matter of obligation to them.

8. We should also sustain our demonstration of love and support to fellow citizens who are still displaced even as government remains committed to safe and dignified resettlement that is ongoing.

9. For our armed forces whose gallantry inspired our volunteers in the first place, we remain forever in their debts and we will continue to support them in any way that we can. We must also keep them in our prayers for their victory means our continued existence.

10. We are grateful to Mr. President, Commander in Chief, Muhammadu Buhari for his sincere and undivided commitment in the fight against Boko Haram in Borno and rest of the northeast. The successes recorded are evident in our ongoing safe rebuilding of communities and safe resettlement of over 20 communities so far in Borno State, and I believe, in other parts of the northeast.

May God bless the Federal Republic of Nigeria and may our democracy be of endless benefit to all Nigerians.

Gwabna Bala Muhammad (Ƙauran Bauchi) Gwabna ne a Jahar Bauchi, ɗaya daga cikin Jahohi 6 da s**a haɗa yankin Arewa maso g...
29/05/2022

Gwabna Bala Muhammad (Ƙauran Bauchi) Gwabna ne a Jahar Bauchi, ɗaya daga cikin Jahohi 6 da s**a haɗa yankin Arewa maso gabas. Ya tsaya takara tare da Atiku, kuma dukkannin Delegates ɗin Jaharsa ta Bauchi shi s**a zaɓa su 20. Wannan kai tsaye na nuni da cewa zai so Atiku ya faɗi shi ya samu nasara.

Amma a hakan, wasu daga cikin al'ummar yankin Arewa maso gabas ɗin basa kallon shi a matsayin maƙiyin Atiku, ko kuma maƙiyin yankinsu sai Kwankwaso da ba Jam'iyarsu ɗaya ba.

Sai dai ban sani ba ko haramun ne wani yayi takara da ɗan yankin nasu oho?

ƴar talla

Bari na yi wa Atiku adalci.Duk da mutanen Atiku basu da wanda ya tsaya musu a rai a takarar nan kamar Baba Madugu raskwa...
29/05/2022

Bari na yi wa Atiku adalci.

Duk da mutanen Atiku basu da wanda ya tsaya musu a rai a takarar nan kamar Baba Madugu raskwanan siyasa zamu fadi magana ta adalci a kan Atiku. Zabi ya ragewa masu zabe.

Ko shakka babu idan Atiku ya yi nasarar cin mulkin Najeriya zaa saci kudi a mulkinsa kamar yadda ake sata a wannan zamanin ko ma fiye da haka. Yaki da rashawa ba ya daga cikin Agenda din Atiku.

Ko shakka babu idan Kwankwaso ya hau mulki matsalar satar kudin gwamnati zata ragu sosai saboda yawan sa ido da yake yi akan shige-da ficen kudade.

Atiku dan kasuwa ne saboda haka zai sanya tsaruka da zasu inganta harkokin kasuwanci. Radadi da azabar rayuwa da wannan almurar gwamnatin ta saka mutane a ciki zasu iya raguwa. Wannan zai iya faruwa ne idan lafiyar jikinsa ta bar shi duba da tsufansa. A inda gizo yake sakar shine Atiku zai iya ci gaba da sanya dokokin kasuwanci da zasu ci gaba da kassara yan kasuwan Arewa suna inganta rayuwar yan kasuwan kudu, kamar yadda s**a yi a zamanin mulkinsa da Obasanjo.

Kamar yadda Atiku zai iya inganta tattalin arzikin kasa ta hanyar inganta kasuwanci, Kwankwaso ma ko shakka gwamnatinsa zata inganta harkokin kasuwanci . Amma ko da wasa Kwankwaso ba zai yarda da dokokin da zasu kassara kasuwanci a Arewa ba.

Atiku zai yi mulkin wa ka sani wa ya sanka kamar yadda muka saba gani a Najeriya. Kwankwaso zai yi mulkin me ka iya menene kwarewarka. Maana dai cancanta zata rinjayi alfarma a mulkin Kwankwaso.

Matsalar ilimi ita ta fi komai ci mana tuwo a kwarya. Atiku zai iya inganta ilimi amma kuma in dai Atikun da na sani ne toh wajibi kudin yin karatu ya kara gagarar talaka a zamanin mulkinsa. Da wahala ba a yi provatizing din harkar ilimin jami'a an mayar da shi hannun yan kasuwa ba.

Kwankwaso kuma zai mayar da hankali ne akan inganta ilimin malam talaka. Talakawa wadanda basu da hanya ko ta kusa ko ta nesa zamu samu damarmaki na inganta iliminsu.

Kusan komai da ka sani mallakin gwamnati ne kamar ilimi, kiwon lafiya da sauransu, Atiku zai yi gwanjonsa ya sayarwa da danginsa da abokansa. Hakan zai sanya kiwon lafiya ya gagari talaka, ilimi ya gagari talaka, kusan komai ma ya gagari talaka. Amma kuma hakan zai iya jawowa a samu inganci a kiwon lafiya a su wadannan bangarori, kawai matsalar dai shine ingancin ba zai amfani talaka ba saboda sun fi karfinsa.

A bangaren tsaro, Atiku ba shi da wani tsayayyen tanadi akan inganta tsaro, amma dai zan tsammanci cewa gwamnatinsa zata iya yin sulhu da yan taadda yayin da kuma zata ci gaba da kara kaimi akan fatattakarsu, abinda ake kira carrot and stick approach. Idan lafiyarsa ta bar shi, bana tsammanin zai zama lusari kamar wannan gwamnatin.

Kwankwaso bana tsammanin zai yi wani sulhu da yan taadda. Zai tabbatar da cewa ya ragargaje su har wurin buyarsu, amma zai dauki matakan inganta rayuwa da ilimin makiyaya. Wannan zai sanya shiga harkar taaddancin ma gaba daya ya zama ba abinda su makiyayan zasu yi shaawa ba. Zai kuma kawo maslaha ta dindindin a wannan lamari.

Fatanmu shine Allah ya Baiwa jagoran Kwankwasiyya nasara ya kuma sanya albarka a mulkinsa. Ya sanya mulkinsan shine mafi alkhairi.

Uncle Abdul.
5/29/2022

18/04/2022

Ashe malam Albaniy zaria shima comrade ne 😂😂

18/04/2022

Ashe malam Bello yabo shima comrade ne 😂

17/04/2022

Wayyo cikina 😂😂😂

17/04/2022

🧐

Karfe 2 na dare a asibitin Monguno, Zulum ya ba likitoci karin kashi 30 cikin 100 na albashinsu a kananan hukumomi 7. Gw...
17/04/2022

Karfe 2 na dare a asibitin Monguno, Zulum ya ba likitoci karin kashi 30 cikin 100 na albashinsu a kananan hukumomi 7.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a wata ziyarar dare a babban asibitin Monguno, a ranar Asabar, ya bayyana amincewa da karin kashi 30% na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai da ke da wasu abubuwan da s**a dace.

Baya ga likitoci, ma’aikatan jinya, ungozoma, kwararrun likitoci, likitoci da sauran ma’aikatan lafiya a kananan hukumomin bakwai za su ci gajiyar karin kashi 20% na albashi da nufin zaburar da su wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya masu inganci da araha.

Kananan Hukumomi bakwai da s**a hada da Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da Banki da ke Bama na daga cikin manyan garuruwan da Boko Haram ta lalata a shekarar 2014, kuma sun kasance ba su mamaye ba har tsawon shekaru takwas har zuwa lokacin da aka sake tsugunar da ‘yan gudun hijira da ‘yan gudun hijira.

Zulum, tare da babban mai shigar da kara na majalisar wakilai, Barr. Mohammed Tahir Monguno, ya ziyarci babban asibitin da misalin karfe 1 dare kuma yana can har karfe biyu na dare.

Babban jami’in kula da lafiya Dr. Solomon Tiza ne ya karbe shi tare da gudanar da shi.

Gwamnan ya ba da umarnin gina karin rukunin ma’aikata da samar da rijiyoyin burtsatse mai zurfi da kuma hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana don inganta ayyuka a wurin.

A watan Janairun 2022, Zulum ya kara albashin dukkan likitocin da ke Borno zuwa matakin da gwamnatin tarayya ta biya don dakatar da yawaitar cutar da likitocin jihohi ke komawa cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya domin samun karin albashi.

A cikin shekaru uku da s**a gabata gwamnan ya amince da daukar jimillar ma’aikatan lafiya 676 da s**a hada da likitoci sama da 40 da ma’aikatan jinya 241 da ungozoma da sauran ma’aikatan lafiya.

Zulum ya shafe daren Alhamis da Juma'a a Monguno da ke arewacin jihar, yana gudanar da ayyukan jin kai da sake ginawa.

Gwamnan ya yi tattaki zuwa Monguno tare da Cif Mohammed Tahir Monguno, kwamishinan sake gine-gine, gyara da sake tsugunarwa, Engr Mustapha Gubio, kwamishinan shari'a na Bar. Kaka Shehu Lawan da tsohon kwamishinan noma, Engr Bukar Talba, da sauran jami’an agaji da na sake gine gine.

Daga shafin Northeast Reporters

Fassara Shuaibu Abubakar

Amurka tayi Juyin Mulki a Pakistan.Jiya Majalisar Dokokin Pakistan ta kada kuri'ar nuna rashin cancanta (vote of no-conf...
10/04/2022

Amurka tayi Juyin Mulki a Pakistan.

Jiya Majalisar Dokokin Pakistan ta kada kuri'ar nuna rashin cancanta (vote of no-confidence) ga Imran Khan a muqaminsa na Fira Mininsta, yan Majalisa 174 daga cikin jumullar 342 ne s**a jefa kuri'ar saukeshi, wanda hakan yake nufin kaso mafi yawa sun rattaba hannu akan hakan.

Menene laifin Imran Khan?

Laifinsa shine bijirewa umarnin Amurka, tare da ziyartar Shugaban kasar Russia Putin a yakin da yake cigaba da gudana a Ukraine, wannan yasa gwamnatin Amurka ta hannun me baiwa Sakataren Harkokin wajenta shawara-Donald Lu- ya shaidawa Ambassadan Pakistan a Amurka cewa:
Amurka za ta taimakawa yan jam'iyyar hamayya su kayarda gwamnatin Imran Khan, idan ya fadi to shi kenan, idan kuma bai fadi ba to Amurka zata farlantawa Pakistan uqubobi na tattalin arziki, tsaro dss!

Bayan jefa kuri'ar rashin cancanta (vote of no-confidence), kai tsaye, aka bada sanarwar kakabawa Imran Khan da muqarrabansa takukumin haramcin fita daga kasar.

Wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da makociyar kasar, wato India babu abinda ta daina na huldar kasuwanci da Kasar Russia, balma da aka jefa kuri'ar nuna kyama ga yakin Russia a Majalisar dinkin duniya, India tana daga cikin kasashe uku da s**a ki yarda su jefa kuri'ar, s**a kuma bayyana cewa suna tare da Russia.

Amma ita Pakistan, tunda kasar Musulmai ce bata da wannan alfarmar ta cin gashin kanta, dole sai dai ta zama me biyayya ga Amurka a komai.

Baya daga cikin maslahar Amurka mulkin mutane masu nagarta a kasashen Musulmai, don haka, duk wani me nuna kishin kasarsa da addininsa zata yi kutun-kutun wajen ganin ya bar mulki, ta hanyar karnukanta a Majalisa, ko ta hanyar zuga rundunar tsaron kasar domin hambarar da mulkin.

Tun jiya muka ga mutane masu gaba da Musulunci, suna murnar faduwar wannan gwamnati ta Imran Khan irinsu Geert Wilders, dan Majalisar kasar Netherlands.

Abubakar Umar
9/Ramadan/1443AH.

Umar Abubakar

10/04/2022

A kasar masu hankali kamata ya yi Amechi ya baiwa yan kasa hakuri sannan ya sauka daga mukaminsa saboda sakarcin da ma'aikatarsa ta yi dangane da harin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da ya faru da gurbatattun hanyoyi na gwamnatin tarayya da suke hallaka mutane babu dare babu rana.

Amma a maimakon ya yi hakan, tunsa a kasar gaba-gaba ake wai yana da kwarin gwuiwar da zai foto ya ce yana son yan Najeriya su zabe shi a matsayin shugaban kasa.

A haka fa kuma duk APC basu da dan takarar shugaban kasar da ya kai Amechi rangwamen aibi. Su kuwa PDP dama baa magana, kaf yan takararsu babu na zaba sai dai na bari.

Abdulaziz Tijjani

10/04/2022

Daman daga cikin matsalolin Nigeria da s**a fi bani haushi akwai matsalar rashin wuta! Sai yanzu abin ya sake karuwa.

Babu amfani da iron, babu amfani da electric cooker, babu amfani da electric kettle, iya TV, fridge, fanka, sai chajin waya da computer kowane sati ₦1,000 to minimize cost. To yanzu ya dawo kowane sati ₦3,000. Su su dauki ₦2,000 su bamu wutan ₦1,000, kuma dole ka saka daga ₦3,000 ya yi sama.

Idan misali outstanding dinsu za su cire, a matsayin gwamnati na mai samawa al'umma sauki, ina laifin mu biya ₦2,000 su dauki ₦1,000 su bamu wutar ₦1,000? Meye asararsu a hakan tunda dai tun farko ba su ce mana za'a biya wani outstanding ba s**a zo s**a saka mana meter, ana zaune a lokacin da komai ya yi tsada s**a kawo mana wannan zaluncin.

Amma sai mu saka ₦3,000 su dauki ₦2,000 su bamu ₦1,000? Wannan shi ne karshen zalunci da karshen rashin imani da karshen rashin tausayi da rashin amfanin gwamnati ga talaka.

₦12,000 duk wata a iya wutar lantarki kawai nan ma ba ka isa ka yi amfani da iron ba sai dole ka kai wanki da guga, su ma sun kara kudin, babu amfani da electric cooker, dole ka sayi gas, shi ma ya kara kudi, sannan wai mu yi shuru kar muce wannan gwamnatin azzaluma ce! To gwamnati ce mai adalci da tausayi.

Daga shafin Albani

09/04/2022

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA YOUTH FORUM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share