27/08/2021
Aji Kima Hadejia
Fassarar Jawabin Mai Girma Gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar kan bikin cikar jihar Jigawa shekaru 30 da kirkirowa.
Auzu billahi Minasshadinin Rajim
Bismillahi Rahmani Raheem,
Ya Yan Uwana al,ummar Jihar Jigawa
yau Juma-a 27 ga watan Agusta 2021 rana ce da tayi daidai da cikar jihar Jigawa shekaru talatin da aka kirkiro ta a shekarar 1991.
Zanyi amfani da wannan dama in sake yiwa al,ummar wannan jiha jawabi na taya murna a daidai lokacin da tarihi ya maimaita kansa na kirkiro wannan jiha tamu,
Idan muka duba baya na doguwar tafiyar da aka yi wacce ta fara daga ranar 27 ga watan Agusta 1991, ina jan hankali tare da kira da mu chigaba da godewa Allah SWT akan irin ni,imar da albarkar da yayi mana a wannan jiha
sannan mu sake jaddada hadin kanmu da yan uwantaka da sadaukar da kai wadda hakan ne ya kawo mana cigaban da jihar nan ta samu.
Ina sake yin amfani da wannan dama na sake yiwa Allah madaukakin sarki godiya da mutanen Jigawa masu karamci, wadanda kowa ke bada tasa gudunmawar domin cigaba da zaman lafiyar da jinjina ga shugabannin jihar na baya kafin zuwana, tindaga kantoman soji na farko Marigayi Brigadier Gneral Olayinka Sule da gwamna Ali Saad Birnin Kudu da marigayi Brigadier General Ibrahim Aliyu ,da Kanal Rasheed Shekoni Mai Ritaya da laftanal Kanal Abubakar Maimalari Mai ritaya da Mai girma Gwamna Ibrahim Saminu Turaki da kuma wadda na karbi mulki a hannunsa Mai girma Gwamna Sule Lamido
Dukkannin wadannan jagorori ba wadda na ware ya yi matukar kokari na tabbatarda cigaba da yadda jihar Jigawa take a yau, tare da yin Addua Allah SWT ya gafartawa wadanda s**a rigamu gidan gaskya a cikinsu, Allah ya kuma kara koshin lafiya ga wadanda suke raye domin suci gaba da bada gudunmawarsu ga cigaba da zaman lafiyar jihar mu.
Ina kuma sake mika godiyata da girmamawa ga iyayen kasa Sarakunan da s**a hadar da mai martaba Sarkin Hadejia kuma shugaban majalissar Sarakunan jihar nan da Mai Martaba Sarkin Kazaure da Mai Martaba Sarkin Gumel da Mai Martaba Sarkin Ringim da kuma mai Martaba Sarkin Dutse
Wadannan iyayen kasa ne guda biyar dake wannan jiha wadda daga garesu ne kowanne Kantoma na soja ko Gwamnan farar hula ya samu shawarwarin da s**a amfane shi ya sami nasarar mulkinsa.
Bawai ina zuga kai ba, irin zaman lafiya da kwanciyar hankali da Allah yabamu a jiharmu a cikin Al,umman mu, mafi yawan kokarin haka yana ga gudunmawar da irin shawarwari da iyayen kasar ke ba kowanne Gwamna a lokacin mulkinsa.
Wadanda Sarakuna suna da cikakken sanin kowacce gwamnati data zo har ya zuwa tafiyarta.
A nan ina kira ga kowa da kowa ya taya ni adduar Allah ya karawa masu Martaba lafiya, ya albarkacesu a aikin da suke mana cikin nutsuwa don cigaban jihar mu tare da Dattawanmu da Malumanmu.
Tarihin jiharmu ba zai cika ba batare da na tabo ma,aikatan gwamnati ba da wadanda muka nada su taimakamana,da wadanda s**a reni sabuwar jihar Jigawa duk da matsaloli da s**a fuskanta na karancin gidajen kwana suke jeka ka dawo da aiki a karkashin yanayi maras dadi saboda karancin ofisoshi da kayan aiki kalilan.
Ina mai farin cikin cewa a yan shekarun nan, munyi kokarin ganin cewa dukkanin bukatun ma,aikata da wadanda muka nada su taimaka mana harma da maaikata da s**a yi ritaya mun sauke nauyin hakkinsu dake kanmu wadda haka yasa muke gudanarda gwamnati ma,abociyar kungiyar kwadago ta kasa wanda a dai dai lokacin da nake wannan jawabin mune a kan gaba kasar nan a fannin dangantaka mai kyau da maaikata.
A yau zamu iya bugun kirji cewa mun bada gudunmawar gaske na gina gawurtacciyar jihar Jigawa data zama mabudin kwaikwayo a samarda ayyukan raya kasa kuma take kan gaba a Nigeria a fannonin wasu aikace aikace da s**a hadar da kiwon lafiya da samarda ruwansha mai tsafta da gina hanyoyi da noman shinkafa da Ridi da bunkasar harkokin kasuwanci da sauransu.
Ina sake kira a garemu duka mu cigaba da sanya Jigawa a gaba da kasarmu baki daya a adduoin da muke na kawo karshen kalubalen tsaro da kasar mu ke fuskanta a yanzu da kuma bunkasar tattalin arziki wadda shima bai tsira ba sakamakon annobar cutar
covid 19.
Samin zaman lafiyar da muke ba zai sa mu shagala ba akan batun tsaro domin idan makwabtanmu basu zauna lafiya ba bamu da tabbacin cewa mun tsira daga barazana amma muna fata da addua wannan yanayi da muka samu kanmu na barazanar tsaro zai zo karshe nan bada dadewa ba da ikon Allah.
Muna adduar Allah use albarkacemu mu Yan Jigawa da ma Nigeria baki daya , ina sake taya mu murnar wannan rana ta cikar jiharmu shekaru talatin da kirkirowa.
Allah ya daukaka jihar CP Jigawa
Allah ya Daukaka jamhuriyar Tarayyar Nigeria
Nagode
27/08/2021