17/07/2022
NDLEA ta k**a wata mata za ta yi safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Oman
Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta k**a wata mai suna Opoola Mujidat, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi zuwa Oman, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.
An k**a ta ne bayan hukumar ta k**a wasu fasinjoji biyu da ke tafiya Oman a ranar Litinin, 11 ga Yuli.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce an k**a fasinjojin biyu, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi kafin su hau jirgi.
“Fasinjojin, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi, suna tafiya tare zuwa kasar Oman dake Gabas ta Tsakiya a cikin jirgin kasar Habasha a ranar Litinin 11 ga watan Yulin shekarar na ta 2022 inda jami’an NDLEA s**a tare su a filin jirgin.
"A binciken da aka yi a cikin jakunkunan su, an gano kullin tabar wiwi da aka boye a cikin wata jaka dauke da kayan abinci, wanda Kazeem ke dauke da ita.”
“Nan da nan Kazeem da Omoniyi s**a sanar da jami’an yaki da miyagun kwayoyi cewa Mujidat da ke kusa da wurin ce ta ba su jakar da ke dauke da haramtattun kayan a filin jirgin, nan take kuma aka k**a ta.”
A cewar sanarwar, Mujidat ta yi ikirari cewa ta kawo kayan ne da nufin fasinjojin biyu su bawa mijinta dake can a kasar Oman din.
~Daily Nigerian Hausa