31/07/2023
A hanya na, zuwa Lagos yau da safe nan.
Azman air s**ayi delaying jirgin da zamu hau zuwa 9:30am, Instead of 7:30am.
A lokacin da muke zaman Jira sai na hango wani saurayi da wayoyi uku a hannu sa, yana sarrafa su one after the other.
A damar shi iPhone 13 ce yar ₦930,000,
Acinyoyinsa kuma wayoyi ne biyu, Samsung Z-Fold 4 ce mai 512 memory kuɗin sabuwarta is ₦1,300,000+, sai kuma iPhone 14 Pro max yar ₦1,150,000.
In total wayoyin hanunsa, banda smart watch ɗinsa sun haura million uku da dubu dari uku ₦3,380,000. (Kuyi mun uzuri, na san kuɗin waya da kwamfuta k**ar hauka, abu na farko da ke zuwa kai na duk na ga devices ɗin da ya ban sha'awa, shine kuɗinsa..)
A wanan lokaci In my head, na ce definitely this guy works virtually, kuma aikin nasa is one of these;
Ko Social media management,
Digital marketing (sales da sauran niche ɗin),
Virtual Assistant,
Executive customer service representative ne,
Ko kuma high-earning freelance writer or editor ne shi,
Ko Online seller or someone that manages eCommerce business,
Or Online marketer researcher/Online personal shopper ne.
Da kuzari na, na matsa kusa dashi, nace dashi nayi la'akari da wayoyin hanunka, sunyi attracting ɗina sosai. So sai nayi introducing kaina.
(Ina murmushi) nace dashi ahaka kake yawo dasu maigida, baka tsoro oga!
Ko dai sauri ne yasa baka samu business class ba ?.
Yace wallahi a'a k**awa tayi, zanyi wani update.
Normally sai ina cikin gida ko cikin mota nake fiddo su haka, idan fita zanyi, i have an iPad with a remote access to all the phones.
Kuma wanan dan naga airport ne, akwai security insha'Allaahu.
Sai na ce dashi haka ne kam. Da kace update, me kake nufi sir ?
Karkayi fushi dani, I'm only curious dan ina da yaƙini digital skills ya baka wanan dama, Nima ina .....anan na echoing my tech abilities.
Yace masha'Allaah, sunana Adam kuma gaskiya social media manager ne ni, I'm managing a federal agency accounts, kuma duk su s**a sayi wanan wayoyi dan aikin da za'ana musu.
Da hira dai tayi hira, bayan mun shiga jirgi, da na kalli kujerar gefensa empty seat sanda jirgi ya tashi, kawai sai na canza seat abina.
Anan nake tambayar sa, me ya karanta ? kuma ya yasamu wanan aiki ?
Yace yawwa, wallahi gara fa muyi hirar nan, yafi...idan ba haka ba wallahi duk rikicewa nake a cikin jirgi.
Mukayi dariya, ya ɗora da wallahi geography na karanta a university of abuja, yayata yar kasuwa ce tun 2014 sai nake managing mata social mediyarta.
Ta samu alheri, kuma ta shahara a Instagram, a wanan lokaci ina yawan taya ƙawayanta da sauran jama'arta, wajan basu strategy wato tsari wajan inganta tasu online presence.
Gaskiya a wanan lokacin abinda ya taimaka mun shine kyauta na dinga yi musu shi, hakan ya bani damar samun experience sosai da kuma samun strong connections.
Ahaka na dinga koyon skills din, ana hakan last two years ɗaya daga cikin matan da na wa managing social media ta kira ta haɗani da mijinta wanda yayi sanadin samun wanan aiki nawa.
Wallahi a lokacin ko naira bata bani, sai ɗan ihsanin yau da gobe ka gane ?
A harkar nan ta tech akwai alheri, amma kada ka yaudari kanka da naiman kuɗi dashi wurjanjan, zaka samu kuɗi amma sai ka dage ka zama kwaro mai tarin experiences first.
Dage ka zama gwani a fannin da kake Kai, idan ta k**a ka bada service ɗinka kyauta ga waɗanda s**a cancanta. Hakan zai sa ka ƙwarewa da samun connections.
Shi bada service a yayin da kake koyo kyauta, na sa ka ƙware sosai ka san duk wani sirrin abun, wani brand ɗin ma zaiyi girman da idan kayi citing ɗinshi a portfolio ɗinka ba karamun alheri zaka samu ba.
Kuma ga connections da zaka haɗa ta wanan hanya, ba daidai bane baka ƙware a kan wani ilimi ba, kawai ka dage wai dole kai sai ka samu kuɗi dashi, wallahi son kuɗin nan ba zai baka damar ƙwarewa ba.
Wanan shawara ce da sabon abokina Adam yace na isar gareku.
Adam zai je Lagos ne yin wani masters class a, Ni kam shikenan zan maƙale masa na kwashi ilimi.
Ina miƙa godiyata ga waɗanda s**a mun fatan alheri a jiya, Alhamdulilaahi mun isa gida Lafiya.
Amma fah, nan zafi akeyi.
IBrahim BaBa