02/01/2020
Salam ya ke muradina,
Da safe na antayo kauna,
Na bayyana sirrikan raina,
Gare ki ina makwancina,
Zo amsa min cikin son rai.
Abar sona abar sona,
Abar kauna abar kauna,
Abar marari a rayina,
Yau ga ni da so cikar kauna,
Cikar buri cikar komai.
Gare ki masoyiya tawa,
Ki ji ni da zantukan baiwa,
Na kaunar nan da ba tsaiwa,
Cikin mararin cikar sowa,
Na bayyana baitukan so dai.
Idan na gane ki don kauna,
Na manta abin da ke raina,
Cikar buri ki zo guna,
Ki amshi bukatuna,
Ki share min duhun komai.
Ranar wanka Bahaushe de,
Ya ce cibi waje bude,
Nufinsa a wangame bude,
Kowa ya gano ido bude,
A san shi a san kalar komai.
Kin san so ba a mai yarfe,
Ba a kyamar tuwon safe,
Zoben so ba a sa karfe,
Burina na tattaro lefe,
Na kai ki garin da ba kome.
Kin san so ba a mai kulle,
Gararinsa yawa na 'yan talle,
Shuhurarsa a zuciya zille,
A ganta a fuska ba kyalle,
A san ya zarce duk komai.
Idan na taho a motata,
Cikin tafiya ta kasaita,
Idan na gane ki 'yar auta,
Kina tafiya ta kasaita,
Na manta batu na tukin dai.
Kalarki daban a mataye,
Sunanki daban na 'yar yaye,
Sautinki daban a Karaye,
A soyayya ana maye,
A sonki ko za na yo komai.
Naman da ake kira soye,
A cakuda kafi zabaye,
A sa naman a sa maye,
A sa gishiri a yo soye,
A so haka duk ake komai.
Maimaita aji fa sai dolo,
A so kam ba a son gwalo,
Ba a kome cikin salo,
Jifa kam sai da dan kwallo,
A so ba a barin komai.
Baitin karshe na ce santsi,
Ya debi mutum ya yo watsi,
Ya farfasa kai ya yo rotsi,
A soyayya a bar kutsi,
Aure a gare ki ne komai.
Ni Nayaya na ce ki dube ni,
Ki min kallon da ba raini,
Da zai mai she ni dan birni,
Na sa kaya na sa rawani,
Na so domin na zam komai.