08/11/2023
Kasar Afrika ta Kudu tayi kira da i kotun hukunta laifukan yaki da ta dauki Israila amatsayin wacce ta tafka mummunan laifi ga dan adam a zirin gaza
Kisan gilla ga ƙananan yara da mata da tsofaffi wannan kadai zai sa kotun ta bayar da damar kamo duk wani mai ruwa da tsaki ciki kuwa har da natanyahu, wanda yake shine babban wanda ya taka duk wata doka ta kotun.
Wannan furucin dai ya fito ne daga bakin ministar dangantaka da kasashen waje ta Afrika ta kudu Naledi Pandor lokacin da take bayani ga yan majalisu a Talatar nan.
Haka nan ministar tayi kira da a gaggauta tsayar da wuta a zirin gaza da israila take yi tun 7 ga watan Oktoba
Ta kara da cewa "wannan abu ne da bai kamata a kyale ba irin wannan kisan dabbancin.
Mu 'yan Africa ta kudu dole ne daga murya mu kira a tsagaita wuta sannan a bude hanyoyin kai kayan jin kai don masu bukata su sami