01/09/2022
Za Mu Taimaka Wa PDP Ta Fadi Zaben 2023 – Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar taimaka wa wajen kayar da jam’iyyarsu ta PDP a zaben Shugaban Kasa na 2023 mai zuwa.
Wike, wanda yake wani yakin cacar baki da Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da wata sabuwar hanya a yankin Omerelu da ke karamar hukumar Ikwerre, ranar Alhamis.
Yana tsokacin ne kan kalaman Ayu, wanda ya ce masu neman ya sauka daga mukaminsa na fama da kuruciya, inda ya ce bai saba kowacce irin doka ba, saboda zabarsa aka yi.
Sai dai a martaninsa, Gwamna Wike, ya bayyana Shugaban na PDP a matsayin mai hadama da ke duba bukatar kansa kawai.
Ya ce bisa ga dukkan alamu Ayun na son PDP ta fadi zaben ne, kuma a shirye yake ya taimaka masa yin hakan.
“Ina mamakin yadda mutane ke zama masu hadama, marasa godiya. Na dauka a matsayinka na shugaban jam’iyyar da ke son lashe zabe, babban burinka shi ne yadda za ka dinke barakarta, ka hada kan ’yan jam’iyya, ba wargaza ta ba.
“Wadannan yaran da kake magana a kansu, su ne s**a kawo ka daga cikin kwata zuwa shugabancin jam’iyyar. Ya ce mu yara ne, a bayyane yake karara ba ya son jam’iyyar ta lashe zaben, za mu taimaka masa.
“Ayu, ka cika bakin cewa ku ne kuka kafa jam’iyyar nan, amma a 2007 ka fice daga cikinta. Idan ka kafa kamfani amma daga baya ka bar shi, wasu s**a raine shi har ya zama abin da ya zama, kana da bakin da zaka zo ka ce naka ne bayan ka sayar da hannun jarinka a ciki?” inji Gwamna Wike.
Takun-sakar ta fara ne tun bayan da dan takarar Shugaban Kasa na jami’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ki daukar Wiken a matsayin Mataimakinsa, inda ya dauki Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.
Wiken dai na neman Ayu ya sauka daga Shugabancin PDP ne saboda a cewarsa, bai k**ata da shu da dan takarar Shugaban Kasa su fito daga Arewacin Najeriya.