08/02/2023
NAZARI: Yadda Ayyukan Tinubu A Matsayin Gwamnan Jihar Legas Za Su Iya Kai Shi Ya Hau Kujerar Shugaban Ƙasa A 2023
Kimanin shekaru 24 da su ka wuce, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a Isolo, ƙaramar hukumar Oshodi domin jagorantar yaƙin neman zaɓensa na gwamnan Jihar Legas.
Ya tsaya a gaban al'umma sama da mutum 20,000 a tsohon babban birnin tarayya inda ya taɓa zama Sanata. A wannan lokaci Tinubu ya saki shiri da tsarinsa akan zaɓen 1999, matsalolin da ya ke son magancewa da kuma manufa da burinsa akan Jihar Legas.
"Na zo ne domin na kawo sauyi, za mu bunƙasa Ilimi, lafiya, tsaro, gami da gina rayuwar mata da matasa su zamto masu dogaro da kai Jihar Legas ta zamto abin alfaharinmu gabaɗaya".
Bayan watanni 5 da wannan jawabi, kusan mutum miliyan ɗaya ne su ka sanya hannu akan zaɓen Tinubu domin gina Jihar Legas. Aiki tare, ƴan kasuwa, shugabannin al'umma, masu sana'ar tuƙa ababen hawa, da ma'aikatan gwamnati sun yi ƙulli sun gina alaƙa mai ƙarfi da ta ratsa dukkan ƙananan hukumomi ta haifar da nasarar zaɓar Tinubu a matsayin gwamnan Jihar Legas da gagarumin rinjayen da babu wani gwamna da ya taɓa samu a tarihin Jihar Legas.
Farkon labari shi ne "Tarihi ko labarin Asiwajuna" ( ), yanzu zai ba da labari kan Tinubu da Jihar Legas da kuma abin da zai cigaba da haifar da tattaunawa mai ma'ana a daidai lokacin da Nageriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar (2023).,
Mai ya haifar da haka ?
A matsayin hukunci kan wa'adin mulkinsa, abubuwan da su ka biyo baya sun fi ƙayatarwa. Dayawan tsofin muƙarraban gwamnati, abokan aiki, ɗalibai, matasa, ƴan kasuwa, da masu ƙaramin ƙarfi da su ka amfana da gwamnatinsa sun yaba. Sun je sun yi aiki a gwamnati ko sun kafa kasuwanci ko shiga kamfanoni, ko gano hanyoyin yi wa al'ummarsu hidima. Da dama su na tunowa abubuwan da su ka faru a baya a matsayin shaida tagari akan abin da za mu riƙa idan mu na fatan zaɓar shugabanni masu nagarta.
A bayyane, wannan zai zama daban a farfajiyar yaƙin neman zaɓe. Shaida