
02/06/2025
Ziyara Ta Biyu
Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jahar Kano Ya Kara Kai Ziyara Ta Musamman Asibitin Murtala Dake Kano Domin Ganin Halin Da Matasa Maza Da Mata Yan Asalin Kano Wadanda Sukayi Hadari Akan Hanyar Dawowar Kano Daga Jahar Ogun Suke Ciki Tare Da Tabbatar Musu Da Aniyar Gwamnatin Jahar Kano Kar Kashin Jagorancin Alhaji ABBA K YUSUF Ta Ganin Sun Sami Lafiya Bayan Haka Nan Take Aka Bawa Kowannan Su Kudi Naira Dubu Dari Biyar Domin Cigaba Da Jinya Duk Da Cewa Gwamnatin Jahar Ta Dauki Dukkan Kudin Maganin Sa Sauran Abubuwana Yau Da Kullin .
Mai Girma Mataimakin Gwamna Yana Tare Da Mai Girma Sakataran Gwamnatin Jahar Kano Da Kuma Shugaban Ma’aikatan Jahar Kano Malam Abdullahi Musa Da Sauran Yan Tawagar Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jahar Kano
Hon Hamza Ahmad Telan Mata
PA Photography To The Deputy Governor Kano.