Mafarauta da Maharba

  • Home
  • Mafarauta da Maharba

Mafarauta da Maharba Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mafarauta da Maharba, Video Creator, .

Dawa dai Dungun mutanen Kebbi. Kowa ya bar hali ba nasa bane.
23/05/2024

Dawa dai Dungun mutanen Kebbi. Kowa ya bar hali ba nasa bane.

Gado girman Ɗa, kowa ya raina gado ba nashi bane.
21/05/2024

Gado girman Ɗa, kowa ya raina gado ba nashi bane.

Ganga ta koma gombe. Gombawa diban fari.
19/05/2024

Ganga ta koma gombe. Gombawa diban fari.

Madugun mutanen birni Idan kana Neman gaskia a farauta kaje wajen shehu idan kana Neman Wanda baya manta amana kaje waje...
19/05/2024

Madugun mutanen birni
Idan kana Neman gaskia a farauta kaje wajen shehu idan kana Neman Wanda baya manta amana kaje wajen shehu
Shafiu yayi masa kida
Yace shi Karen baba Sa,adu
Shi Karen audun mama
Shi Karen audun kanti
Shi amanar Dan baba
Da amadudu

Kada a karya karafa Tambarin gidansu Nasiru Sarkin Yaki Rano
17/05/2024

Kada a karya karafa
Tambarin gidansu Nasiru Sarkin Yaki Rano

Goje rabin gari. Alhaji Sulemanu Gagarawa
16/05/2024

Goje rabin gari. Alhaji Sulemanu Gagarawa

SIYASAR HARKAR FARAUTA 10DAGA MUNIR A IKARA  Umaru Dan Baffa ya nuna shifa yanzu a zazzau yake ba a kano ba,sulhu Kuma a...
22/07/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 10
DAGA MUNIR A IKARA
Umaru Dan Baffa ya nuna shifa yanzu a zazzau yake ba a kano ba,sulhu Kuma a kano akayi,manyan mafarauta da s**ayi sulhu s**a ci gaba da tarurruka da mabiyansu suna hada Kan mafarauta a zauna lfy, Allah ya gafartama Dan Asaben dodo akwai wani kokari da Dan Asaben dodo s**ayi Wanda ba kowa bane hankalinshi yakai Kan wannan alherin na su Dan Asaben dodo,abinda s**ayi shine tunda an fara kawo maganar cewa kano ne akayi sulhu Banda zazzau, sai Dan Asabe s**a shigo zazzau din da maganar sulhu,a maganar fadan gaba a zazzau idan sarkin dawa kalu Dan duna da kaura tsaibu s**ace a zauna lfy anyima fadan farauta rauni a zazzau,kalu Dan duna da kaura tsaibu gidan guna abokaine sosai sabani ya shiga s**a bata fadan shine ya rikide ya koma yadakwari da kura a yankin ikaran zazzau sunyi fadan gaba sosai tsakaninsu k**ar fadan dutsen bauna dutsen bori dajin kalu,kalu Dan duna tare yake da mutanen yadakwari dasu yake tafiya,kalu ba sa o in su Dan asabe bane gaba yake dasu sosai wasu sunce zai girmi wayya ko suzo sa o i' Amma Yana son Dan Asaben dodo duk abinda Dan asaben dodo yake so kalu zai mishi in kanajin kirarin kalu sai ka dauk**a yaron Dan Asabe ne,shi Kuma kaura tsaibu gidan guna tare yake da mutanen kura dasu yake tafiya kaura tsaibu uban gidan umaru Dan Baffa ne idan anama kaura tsaibu kida umaru Dan Baffa ne yake mikewa ya karbi kaura tsaibu sak**akon tsaibu baya kirari sabida fadan dake tsakanin kaura tsaibu da kalu tasa umaru Dan Baffa ya tare a gidan guna,to kunga idan kaura tsaibu da kalu s**ace a zauna lfy adaina fada ko ba a daina gaba daya a zazzau ba anci karfin fadan gaban wannan dalilin ne yasa su Dan Asaben dodo s**a shigo yankin zazzau har s**aci galaba aka hadu ga sarkin dawa kalu Dan duna ga kaura tsaibu aka yafema juna aka shirya akayi koke koke tsohuwar abota ta dawo sabuwa har s**a bar duniya wannan zaije gidan wannan wannan zaije gidan wannan za aje wasa tare banmantawa anyi biki agidanmu, akwai ci gaba

SIYASAR HARKAR FARAUTA 9DAGA MUNIR A IKARA Da su iro baban kwari duk sani gwani shine ja gaba Dan haka idan sani gwani y...
15/07/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 9
DAGA MUNIR A IKARA
Da su iro baban kwari duk sani gwani shine ja gaba Dan haka idan sani gwani yayi sulhu ko kayi fadan fadan bazai maka dadi ba,a garin mlm ga adahama shikadai in yayi sulhu ba sauran fada a garin mlm,to an lura da jigo a ko wane ban gare Kuma sun ansa Kira yadakwari Dan Asaben dodo ya ansa Kira a kura sani gwani ya ansa Kira a garun mlm Adahama ya ansa Kira abirni su Dan Asabe bawan sarki su Dan juma su Miko duna su bature da sauransu suna da yawa sosai basai an fadi sunan kowa ba, mafarauta da yawa sunyi murna da wannan sulhu wa yanda akeganin k**ar bazasu karba ba k**ar Dan Inna na gargai sai gashi ya karbi abin hannu biyu biyu,ko wane jigo yayi tarurruka da mabiyanshi kafin azauna da mahunkunta haka Kuma s**a hadu a gaban mahunkunta aka yafi juna akayi sulhu,duk da abangarorin biyu an Sami yar tirjiya daga wajen masu dawan a Yan cikin garin kura wandara jikan ladi da kaura diraman su kaura manyal da wasunsu zunyi tirjiya sun nuna su Basu yarda da wannan sulhun ba basa ciki,anyi kokari sosai wajen aga anfahimtar dasu Amma abin yaci tura Amma tunda sani gwani da iro baban kwari sun ansa to zaka iya cewa gaba daya kura tayi sulhu,a cikin garin yadakwari tunda su Dan Asaben dodo s**a karba su duguja babu Dan cikin yadakwari da ya kawo tirjiya saidai wasu dake cikin birni k**ar Aminu baban jaba Amma Dan Asaben dodo yashawo kanshi ya karba ,k**ar kaura gundu a yaryasa Shima ya kowo tirjiya amma ya karba,duk wa yanda s**a ki karba acikin yan kura bai Hana aje gaban mahukunta ayi sulhunba sabida duk wani jigo a kano ya karba,umaru Dan baffa asalinshi bakano ne ya dawo yankin zazzau da Zama a wani gari kafin Allah gaba,kafin Allah gaba wani kauye ne a Ikara local government shi ba Dan cikin garin kura bane Amma madugu ne babba a kafar kura Yan kura suna tak**a dashi da maganar sulhu ta taso Shima yayi tirjiya yafi kowa nuna tirjiyarshi a fili,ya nuna wannan sulhun da akayi akano a kano kawai akayi Banda zazzau, akwai ci gaba

SIYASAR HARKAR FARAUTA 8DAGA MUNIR A IKARAA ci gaba da kokarin kawo zaman lfy tsakanin mafarauta shine Mai martaba sarki...
08/07/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 8
DAGA MUNIR A IKARA
A ci gaba da kokarin kawo zaman lfy tsakanin mafarauta shine Mai martaba sarkin kano Alhaji Ado Bayero ya fara ma lifidin kano maganar zaman lfy tsakanin mafarauta, Usman Wanda akafi sani da Dan Asabe bawan sarki na gaje shine lifidin sarkin kano sarauta ce da s**a gada kasancewar kakanninsu mayaka tun abaya k**ar yadda naji a wata majiyar,Kuma Dan Asabe bawan sarki ya kasance jigo ne babba a harkar farauta Mai tarin magoya baya acikin birnin kano gashi Yana da matsayi acikin fada,dole duk abinda ya taso ta fada dangane da harkar jeji ya fara ta Kan Dan Asabe sannan a wata majiyar Dan Asabe yasha suyi magana da sarki game da yadda ake fada tsakanin mafarauta tunda fadan ya ishi kowa,tunda sarki ya bada umarni dole Dan Asabe zai bada hadin Kai shine dalilin da Dan Asabe ya fara tattaro Kan mafarauta manya abokan tafiyarshi akan wannan sulhu da ake so ya kasance Kuma s**a bashi hadin kai,irin su Dan wali nagindin dala su Dan juma sharada da sauran manya da suke tare aka gangaro har wa yanda ba kafarsu daya ba mutanen yadakwari Dan Asaben dodo su duguja barau na umma da sauran mutanen yadakwari Kuma Allah ya sama abin albarka s**a yadda,(a gurguje mukeyi basai an fayyace duk abinda akayi ba ana fadin kadan daga ciki ne) haka mutanen kura sun ansa Kira k**ar sani gwani Dan yarinya da iro baban kwari da sauran mabiyansu sun karbi maganar sulhu dari bisa dari,wani abin lura game da manyan da s**a fara karbar sulhu shine wa yanda s**a fara karbar sulhu kowa jigo ne a bangarenshi,misali Dan Asabe bawan sarki da su Dan juma sharada acikin birni su kadai idan s**a karbi sulhu a kafar kura to an Sami tasgaro duk Wanda yace zaiyi fada to fadan bazai mishi dadi ba,hakanan a ban garan yadakwari acikin birni akwai su bature mlm sani su shehu zaiti da sauran su s**adai in s**ayi sulhu yadakwari ta Sami tasgaro in ka koma cikin kura sani gwani shine babban jigo shi yake Jan su wandara da kaura diraman da sauran mafarauta na kura,akwai ci gaba

SIYASAR HARKAR FARAUTA 7DAGA MUNIR A IKARAGomnan kano Dr rabi u'musa kwankwaso da sarkin kano Alhaji Ado Bayero sune s**...
01/07/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 7
DAGA MUNIR A IKARA
Gomnan kano Dr rabi u'musa kwankwaso da sarkin kano Alhaji Ado Bayero sune s**ayi Kira sune s**a hadu s**a tattauna maganar sulhun mafarauta dubi ga yadda rashin Zama lfy yake dada karfi tsakanin mafarauta, sannan babban dalilin da yasa hankalin mahukunta ya karkato akan yadda za ayi ayi sulhu adaina fada shine yaduwar Yan daba da suke addabar mutanen birni da kwace da harkar miyagun kwayoyi da sace sace da zidda jinin juna dililin fadan daba daba da sukeyi,abin haushin sai s**a jingina kansu da harkar farauta zaka dinga ganinsu da karnuka da mak**ai Amma ba ya zuwa farauta shine kullum jin kidan bishi,in Banda harkar siyar da miyagun kwayoyi ba abinda yakeyi da wannan kwacen da sauransu,sabida haka tunda an Saba ganinshi da Kare to duk inda s**aje s**ayi fada duk Wanda ya gansu kawai abin da zai dauka kawai da mafarauta akeyin fadan in yaje gaba zai bada labari abinda zaice shine yaga mafarauta suna fada,awannan lokacin anyi daba kala kala abirni Kuma har wasu garuwan makotan kano wannan harkar dabar da ta taso daga kano duk sun yadu a wa yannan garuruwan,a kano aka Sami Yan kazagi Bala wai kawai da Dan daba yaga latsi sai yacema Kai ka zagi Bala na Yan kura?da katsaya tambayar wane balan?kawai sai azare karfe a karbi abinda ke hannunka amaka kwace kiri kiri ba yadda ka iya,a Zaria Kuma akayi ya'yan mage suma haka s**a dinga rashin mutunci akwai wa yanda har amarya s**a taba tare hanya s**a karbe amaryar s**a tafi da ita,hakanan cikin kaduna nanma abin ya qazanta sosai Dan haka dole ne yasa hankalin mahukunta sai ya dawo Kan harkar farauta,k**ar yadda na fada indai kano ta daina fadan gaba to duk Wanda sukeyin fadan gaba sai ya daina tunda dama duk Wanda yayi fadan gabar su ya Taya,dama ko ka taya yadakwari ne ko kura Kuma duka suna karkashin mulkin gomna rabi u'musa kwankwaso ne da Alhaji Ado Bayero ne,wa yannan da kuke gani ahoto wasu kadan ne da s**ayi asalin fadan gaba Kuma masu biyayya ne ga sarkinsu dole su ansa kiranshi,kubiyoni

SIYASAR HARKAR FARAUTA 6DAGA MUNIR A IKARA  Shiga siyasa da wasu mafarauta s**a shiga ta kawo matsala sosai wasu da hark...
24/06/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 6
DAGA MUNIR A IKARA
Shiga siyasa da wasu mafarauta s**a shiga ta kawo matsala sosai wasu da harkar siyasa akayi anfadani aka kashesu wani a tareshi a hanyar dawowa wajen harkar siyasa akasheshi,wasu Kuma ta kawo musu rabuwar Kai atsakaninsu irin wannan rabuwar Kan ne ya Dan jawo cikas a fadan farauta na gaba awani wajen tunda Kai ya fara rabuwa,wani wajen Kuma ananan dai ana gwabzawa mafarautan da s**a shiga siyasa abin ya zame musu biyu adaji ga fadan gaba a gida Kuma ga harkar siyasa sabida haka fadan ya kara tsamari musamman acikin birni Saida takai kusan kowa ya gaji da fadan,tunda anyi an Kara yi tun kafin azo Kan siyasa anyi kazaman fada a wurare da dama,k**ar dutsen bauna dutsen bori marke gafan runfar kwano kekasa kwazazzabon Yan mata,kadan ne wa yannan akwaisu da yawa to dole kusan kowa ya gaji da fadan wasu wasu Kuma su aransu basuki tsakaninsu da abokin fadansu ayi tayi har abada ba,ana cikin haka ne har Allah ya kawo lokaci 1999 akayi zabe obasanjo ya Zama shugaban kasa Dr rabi u'kwankwaso ya Zama gomnan kano,Mai martaba sarkin kano Ado bayero da gomna s**a tattauna akan halin da harkar farauta tashiga a birni da kauye. Akwai ci gaba
Ina sarki nakala barka da juma a'dafatan zamuyi sallah lfy Allah yasa mugama lfy

SIYASAR HARKAR FARAUTA 5DAGA MUNIR A IKARA   Ahaka aka ci gaba da tafiya kowa naso ya ga bayan kowa alokacin mafarauci z...
17/06/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 5
DAGA MUNIR A IKARA
Ahaka aka ci gaba da tafiya kowa naso ya ga bayan kowa alokacin mafarauci zai taso daga garinsu yazo ya tare agarin abokin tafiyarshi yayi wata da watanni wasu suyi shekaru sunzo Taya abokin tafiyarsu fada saidai azo gida aga iyali akoma,sunyi fada bakin iya iyawarsu an hadu adaji da dama anyi fada, malamai ne kawai suke iya jawo hankali domin azauna lfy Amma abun yaki ci yaki cinyewa lokacin da aka shigo siyasa Yan siyasa sun shiga jikin wasu mafarauta su Kuma s**a shiga harkar siyasa ana daukarsu ana zuwa kanfen dasu,shi yasa gabar ta Kara fasuwa acikin birni so Yan siyasa basa so wutar ta mutu sabida anfanin da suke musu, shi yasa malamai s**ai takira akan adaina fadan Amma abin yaci tura acikin malaman da s**a dinga Kira azauna lfy akwai shehi Nasir kabara yayi kokarin yaga anzauna lfy tsakanin mafarauta Amma Yan siyasa Basu bashi goyon bayaba,tunda kano itace uwa Kuma inda aka fara fadan gabar yankin kano ne sabida haka in s**a zauna lfy kowa zai zauna tunda duk Wanda ya shiga fadan farauta bakano ka taya,ko a zazzau misali ban garanmu na ikara tsakanin kaura tsaibu da sarkin dawa kalu dukkaninsu kanawa ne Dan haka in kano ta zauna lfy a harkar farauta to makotanta sai sun zauna lfy Amma manya sunki bada hadin Kai, akwai ci gaba

SIYASAR HARKAR FARAUTA 4DAGA MUNIR A IKARA  Shi yasa a makotan yankin kano zazzau da wasu sauran garuruwan da suke makot...
10/06/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 4
DAGA MUNIR A IKARA
Shi yasa a makotan yankin kano zazzau da wasu sauran garuruwan da suke makota tsofaffin mafarauta da s**a zauna s**a kafu s**a hada gayyarsu ta farauta s**a zama k**ar dama can agarin aka haifesu Amma in kabi tarihi sai kaji daga kasar kano yayi hijira ya dawo wannan garin Kuma akaci gaba da fadan gaban bawai ankare bane tunda ana haduwa a farauta,in Kuma anajin fadan ana iya sa daji musamman ace in ka Isa kazo daji kaza rana kaza wasu in ansa dajin za suje wasu Kuma bazasu ba,ga Wanda ba bakano ba Yana Kuma makota da kano nasan in ya karanta rubutunnan sai ya tuna wani mafarauci kila agarinsu Wanda hijira yayi ya dawo garin Amma asalinshi bakano ne,acikin wannan yanayin Saida ya kasance fadan da mafarautan sukeyi baso sukeyi ba Amma ya k**a dole sai sunyi tunda in an hadu anyo kanka ba saranda mafarauci zaiyi ba ko gudu ne ko faduwa ko kasha dakyar ko Kai ka koresu,in za ayi wasa sai anyi gayya sosai ba karamin uzuri bane zai Hana mafarauci zuwa wajen wasa ba in Yan kafarsu zasuyi lokacin wasu garuruwan anfi yin wasan dare,za a kunna fitillar ruwa makadi ya tashi kida aci gaba da Kiran maza suna kirari haka za a raba dare ana wasa wani lokacin abokan gaba ana wannan kida za abiyo dare afada wasu su rasa rai wasu su tafi da rauni,dalilin wannan fadan gaba na mafarauta wasu sun rasa iyayensu wasu yayyinsu wasu kannensu wasu abokan tafiya haka akaci gaba kowa Yana so ya dauki fansar abinda aka mishi, akwai ci gaba

SIYASAR HARKAR FARAUTA 3DAGA MUNIR A IKARA   Haka aka ratso cikin wannan yanayin na rashin Zama lfy tsakanin mafarauta d...
03/06/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 3
DAGA MUNIR A IKARA
Haka aka ratso cikin wannan yanayin na rashin Zama lfy tsakanin mafarauta duk inda aka hadu za a iya yin fada,Amma duk da wannan gabar haka ake haduwa adaji ayi farauta tare da abokan gaban ba wani maganar wasan buya,kamin kwace ko ka dake ni haka za a hadu ga Kuma makadi Nan Yana kida a mazubi ga Kuma abukan fada za a Kira wane daga gari kaza makadi ya zuga mutum ya tashi yayi kirari ya fadi inda yasha wuya da inda ya bayar wani Kuma akirashi ya kasa ansa kiran,in anje mashaya duk Wanda ya riga zuwa Shan ruwa in ka sake saidai ku jira su gama in Kuma kunga latsi anan wajen Shan ruwan lbr zai canza,an dibi shekaru a cikin wannan halin lokacin Kuma ba ayi yawa k**ar yanzu ba sarakai sune suke da karfin fadi aji,zaka Sami mafarauci baya rabo da sarakai domin idan s**ayi ta adi sarakan basa musu komai idan suna shiri in Kuma basa shiri ya mikashi,in akayi babban ta adi sai adanyi hijira kafin maganar ta mutu wasu Kuma in s**ayi hijirar sunyi kenan saidai su dawo sugaida dangi su koma,shine zakaji anfadi tarihin mafarauci sai kaji asalinshi hijira yayi ya dawo inda yake da zama,akwai ci gaba

SIYASAR HARKAR FARAUTA 2DAGA MUNIR A IKARA  A wannan lokacin yadakwari ce kawai suke da sarkin dawa tun taletale,shi yas...
27/05/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 2
DAGA MUNIR A IKARA
A wannan lokacin yadakwari ce kawai suke da sarkin dawa tun taletale,shi yasa s**a zama jagorori a harkar daji ana nan ana wannan Zama na zumunci tsakanin yadakwari kura garun mlm da sauran kauyuka sai sabani ya shiga tsakanin shawai da dagajirau shaidan ya shiga s**a bata,sai shedanun mutane s**a shiga s**a Kara Bata al amarin abu k**ar wasa gaba da fada ya fara yaduwa tsakanin mabiya, wasu sunce wannan dalilin ne aka samu kafar yadakwari da garun mlm har ta rikide ta dawo kafar kura da yadakwari Amma lokacin ance zafin gabar yafi da yadakwari da garum mlm,shi Kuma mafarauci Allah ya h**e mishi zumunci zaka Sami mafarauci a awani garin ya shiga fadan,kila Yan yadakwari abokan tafiyarka ne Kai Kuma kana wani garin bakasan me ya hada fadanba dole ka goyi bayan yadakwari inkai mafadaci ne,haka kila garum mlm abokan tafiyarka ne kaima zaka ara ka yafa ka tamamusu,ko Kuma kana can wani garin Kuna fada da wani abokin gabanka shi yasan mutanen kura Kai Kuma kasan mutanen yadakwari,shi kenan sai a dakko waccan gaba da akeyi a tsakanin yadakwari da kura da garun mlm sai a ci gaba, da haka gabar ta dinga yaduwa aka samu kafa kafa mafarauta s**a dinga kashe junansu sunama kansu rauni,kasuwa sai da hargi masallacin juma a'saida hargi har Jana iza zaka iya ganin mafarauci da hargi,in kasa shaya bazaka iya shiga wani garin da ita ba saidai ka jefar da ita a hanya Dan kana tsoron kila garin da zaka ratsa akwai abokan gabarka karsu tareka,akwai cigaba

A wannan zantawa da mukayi da shi, ya lábarta mana yadda kakansa ya jefa gyaɗa sama, ya jefa gabas, yamma, kudu da arewa...
27/05/2023

A wannan zantawa da mukayi da shi, ya lábarta mana yadda kakansa ya jefa gyaɗa sama, ya jefa gabas, yamma, kudu da arewa, yace ayi tafiya. Musabbabin hana faɗan mafarauta da s**a shiryo shi tun a gida. Da sauran abubuwan ban mamaki.

A wannan zantawa da mukayi da shi, ya kabbarta mana yadda kakansa ya jefa gyaɗa sama, ya jefa gabas, yamma, kudu da arewa don hana wani faɗan mafarauta da ak...

A wannan zantawa da mukayi, Alasan ya bamu labarin yadda yake daukan kare a kwangiri ya goya a keke ya tafi farauta, har...
25/05/2023

A wannan zantawa da mukayi, Alasan ya bamu labarin yadda yake daukan kare a kwangiri ya goya a keke ya tafi farauta, har kawo wannan zamanin da ake shiga mota a tafi jejin.

A wannan zantawa da mukayi, Alasan ya bamu labarin yadda yake daukan kare a kwangiri ya goya a keke ya tafi farauta, har kawo wannan zamanin da ake shiga mot...

A wannan hira, zamu ji yadda másu dawa suke daurin jeji. Hakanan zamu ji yadda idan an samu sabani a tsakaninsu suke rab...
23/05/2023

A wannan hira, zamu ji yadda másu dawa suke daurin jeji. Hakanan zamu ji yadda idan an samu sabani a tsakaninsu suke raba raini, har ta kai ga kowa ya wahala, wataran ma saidai a dawo daban-daban.

A wannan hira, zamu ji yadda másu dawa suke daurin jeji. Hakanan zamu ji yadda idan an samu sabani a tsakaninsu suke raba raini, har ta kai ga kowa ya wahala...

A wannan Zantawa, zamu ji yadda ta gam ma su Ade da Su liman a kan wata gada da ba a yiwa shaida ba. Sanadin da ya jawo ...
22/05/2023

A wannan Zantawa, zamu ji yadda ta gam ma su Ade da Su liman a kan wata gada da ba a yiwa shaida ba. Sanadin da ya jawo rasuwar Aden Dakare. Duk daga bakin Baleri Mai kada kwaure.

A wannan Zantawa, zamu ji yadda ta gam ma su Ade da Su liman a kan wata gada da ba a yiwa shaida ba. Sanadin da ya jawo rasuwar Ade. Duk daga bakin Baleri Ma...

21/05/2023

Baleri Na rafin Duna, samarin Aden Dakare

SIYASAR HARKAR FARAUTA 1DAGA MUNIR A IKARA   Ina so mataka toyi siyima rubutuna fahimta mai kyau,a can baya mafarauta su...
20/05/2023

SIYASAR HARKAR FARAUTA 1
DAGA MUNIR A IKARA
Ina so mataka toyi siyima rubutuna fahimta mai kyau,a can baya mafarauta suna fitowa daji gaba daya babu wani banbancin kafa babu fadan gaba saidai ka nuna jarumtarka akan Wanda ta k**a ka nuna,in ta fadi in ba zugarku daya ba in kaga latsi ka karba babu gaba saidai gabar nama in ya fadi zaka Sami waccan gayyar da wannan ba ashiri kila wani ya tabama wani kwace Shima Yana so ya dauki fansa Amma babu gabar kafa kafa,mafi yawancin masu dawa gada s**ayi wajen iyayensu haka akai ta tafiya har lokacin shawai baban garba sarkin dawan yadakwari alokacin garum mlm da kura da kauyukansu Kai har lahadin makoli tawagar shawai baban garba ce shine madugu uban tafiya shawai suke bi shine uban kowa adaji iya gagararka in shawai yace kabari sai ka bari,lokacin sarkin kano Abdullahi bayaro shine yaba shawai ankwa duk mafaraucin da yayi ba daidaiba ya Kuma cancanta a kaishi birni to shawai ya kawoshi, alokacin in akayi fada adaji ba shawai Yan doka s**a k**a mafarauci ko mutum ka kashe in shawai yaje sai ya karboka,idan shwai ya fito daji mutane ne iya ganinka, shawai baban garba da dagajirau Mai kidan bishi na garun mlm k**ar oga da yaro ne domin dagajirau makadin shawai ne duk inda shawai yake zaka iya ganin dagajirau duk inda zaije kida shawai zai iya sani, dagajirau shine ya dauki hannun adahama ya hada da na Dan Asaben dodo ya damkawa shawai yace gasunan amana tun suna yara haka s**a taso suna zumunci,ga Wanda ya taba jin wani kida na dagajirau zakaji kankura na mlm Musa Yana kirari Yana cewa ni bakon Dan asabe a yadakwari ni bakon na bawa mai matimi anan zaka gane Ashe dama can abokan juna ne tare suke fada suma wasu kwace babu Wanda baisan gidan kowa ba Kuma babu Wanda baisan jarumtar kowa ba,tun kafin wannan lokacin yadakwari ta kasance anan yankin a harkar farauta itace jagorar ko wane gari a harkar daji tunda sune suke da sarakan dawa tun asali daga wannan sarkin dawan sai wannan sarkin dawa,cigaban rubutuna nanan tafe

Duniya Manya muke tuna tsufa da mutuwa a ko dayaushe,kowa daka gani daga rauni ya fara har karfinshi ya kawo,tafiya na t...
20/05/2023

Duniya Manya muke tuna tsufa da mutuwa a ko dayaushe,kowa daka gani daga rauni ya fara har karfinshi ya kawo,tafiya na tafiya kuma ya koma k**ar yadda ya taso a mai raunin, to ko ba mutuwa wannan kawai ya Isah abin tunani,Masu dawannan k**ar yadda ka taso amatashinka majiyin karfi mai jin kanshi suma haka s**a taso abun da s**ayi akuruciyarsu ko duniya aka Baka akace kayi bazaka iya ba, AMMA yanzu girma ya hausu wasu ba lfy wasu da lfy AMMA girman ya k**asu basu da buri arayuwarsu saidai fatan gamawa lfy babu mai son tashin hankali ya sameshi, inda rai kaima zaka zo wannan lokacin kayi kokari kabar abun koyi kafin lokacinka yazo, irinsu sunanan burjik sai an fadi sunan wani mai dawan SAI kaji wani yace wai daman yananan?to duniyar kenan,!!!
Kaura gundu wandara jikan ladi Dan kuli Baban duna Sarki najume tanga Baban dudu jangwalo Na Baban yanga sani Dan ilu alhaji wada hotoro SHEHU zaiti sale me jajaye Sarki gyado amadudu mai Dawa hausawa aciman mutanen kura Kaura manyal duguja narabi Bala kuttu sale tifa Baushe mai gida adawanau falalu Na kofar jatau mlm kani uba ranja Sarki rabe barau Na umma ado binge sarki sale Na bawo dahiru tanga Sarki manu sani cilli SA idu Goje makarfi Na bar u arnan sale kogo kawu kawu, suna nan burjik bazasu lissafu ba, wani yafi wani tsufa wani yafi wani lfy amma in ka duba SAI kaga da Wanda yafi tsufan da Wanda akafi duk girman ya k**asu,ka taba jin wani yayi rigima da wani atsakaninsu?duk Neman gamawa lfy sukeyi da wannan duniyar ,in ka tsaya kayi tunani zakaga akwai ragowar Masu irin shekarunsu da yawa,wani in ka ganshi aka Baka labarin lokacin da yayi a wannan harkar sai kace karya ne sabida yadda zamanin yayi dashi, wannan izina ce sosai da zatasa ka zauna da mutane lfy,mudai addu a'ce tsakaninmu daku Allah yasa Ku gama lfy damu Baki daya
Munir A Ikara

A yau zamu fara kawo muku rubutu mai taken Siyasar harkar farauta wanda Munir Abubakar Ikara ya rubuta. Wannan rubutu za...
20/05/2023

A yau zamu fara kawo muku rubutu mai taken Siyasar harkar farauta wanda Munir Abubakar Ikara ya rubuta. Wannan rubutu zai riƙa zuwa muku a duk ranar asabar a wannan shafin da misalin karfe 7 na dare. A karanta lafiya.
PS: Hoton marubucin

Dan kuli baban duna na balaraba Mai sauru ,jaki Sha dukan maxa na kauyan Ali.
19/05/2023

Dan kuli baban duna na balaraba Mai sauru ,jaki Sha dukan maxa na kauyan Ali.

Allah kajiqan sanda jikanmowa natsohuwa mijin gambori maitafiya da matojikan ayya gamji sha saran maza kanin bunkure
19/05/2023

Allah kajiqan sanda jikanmowa natsohuwa mijin gambori maitafiya da matojikan ayya gamji sha saran maza kanin bunkure

Jejin dai maza matsotsa ƙarin kunama
18/05/2023

Jejin dai maza matsotsa ƙarin kunama

Kantafi masomin asara wa ke son ɓari yabaiwa makaho kaya, ku ke sa gani garara garara,  ku ke da  kogin jini idan an nem...
18/05/2023

Kantafi masomin asara wa ke son ɓari yabaiwa makaho kaya, ku ke sa gani garara garara, ku ke da kogin jini idan an nema, lahira uwar cirani SALE TIFA na Malan hari, walakiri yaushe kazo, Allah ka jikan duna na gindin dutse, Allah kajikan lahirar shawai nakande dan mamma cirkwui babban bako amincin Adahama jikan musa dan audu magajin tsoho, Allah ya kyautata makwanci Allah ya kara hada kan mafarauta a duk inda suke.

zamani mai yayi Allah yajikan sarkindawa dan juman sharada aminchinubale nahauwa Allah yatashi kafadarMaza
17/05/2023

zamani mai yayi Allah yajikan sarkin
dawa dan juman sharada aminchin
ubale nahauwa Allah yatashi kafadar
Maza

Ba kisan Gwanki ba a sam maɗauka kayin
17/05/2023

Ba kisan Gwanki ba a sam maɗauka kayin

Sale mai jajayemai guibi da doka Dan saboMai jar miya mijin talatuMai dafa kan mahaukaci yaje yayi sallahAjiyar danju Da...
16/05/2023

Sale mai jajaye
mai guibi da doka Dan sabo
Mai jar miya mijin talatu
Mai dafa kan mahaukaci yaje yayi sallah
Ajiyar danju Dan Bawa
Amincin gazara mazan kibau Dan Garba
Ajiyar kura Na hinde Uban kaka
Allah ƙara lafiya

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mafarauta da Maharba posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share