02/10/2021
Jawabin Mai Girma Firaministan Nageriya Na Farko, Alhaji Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, Wanda Ya Gabatar A Karon Farko A Matsayin Firaminista A Shekarar (1957).
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Cikakken jawabin mai girma Firaministan Nageriya, Alhaji Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa wanda ya gabatar a karon farko a matsayin Firaminista a shekarar (1957).
"Wannan muhimmiyar rana ce ga Nageriya, da kuma kasancewa Firaministan Nageriya na farko. Ina alfahari da yi wa ƴan ƙasata jawabi a wannan dare. Ina alfahari da kuma ƙanƙan da kai a duk lokacin da na tuna girman nauyin da ke kaina ni da abokan aikina.
A yau mun kai mataki na ƙarshe kan gwagwarmayarmu ta neman ƴanci, nan da shekaru uku masu zuwa za mu ga nasara mai girma kan fafutukar da mu ke haɗuwa mu ke yi shekara-shekara. Za mu girbi abin da mu ka shuka. Nasarar girbin ta dogara ne akanmu gaba ɗaya, kuma wannan shi ne dalilin ma da ya sanya na ke cike da farin cikin gabatar da wannan jawabi da daddare.
Kowane ɗaya daga cikinmu ya na da rawar da zai taka kan aikin shirye-shiryen samun ƴancin kan Nageriya a ranar 2 ga watan Afril,1960. Ina fatan kowane mutum a Nageriya zai fahimci cewar wannan ba aiki ne mai sauƙi ba, ba aiki ne wanda gwamnatin tarayya da ministocin larduna da ƴan majalissu kaɗai za su yi ba, nauyi ne da ya rataya a kan kowane ɗaya daga cikin ku domin da ƙoƙarin kowane ɗaya daga cikin ku ne ƴancin kan tarayyar Nageriya zai tabbata a shekarar 1960.
Mun riga mun bayyana aniyarmu ta samun ƴancin kan ƙasa a ranar 2 ga watan Afril, 1960, sannan idan mu na fatan ƙasarmu ta kasance cikin ƙasashen duniya masu daraja ya zama wajibi mu yi dukkan ƙoƙari wajen ganin wannan buri ya samu cimmuwa tare da kykkyawar dangantakar ƙasa da ƙasa kan kykkyawan shugabancin nagari a cikin gida.
Yanzu haka Nageriya ta kai wani mataki mai girma a tarihinta. Ya zama wajibi mu yi amfani da wannan dama da mu ka samu mu nuna cewar mu na da damar da za mu kiyaye harkokinmu yadda ya kamata. Duk ɗan Nageriya ko mi ne ne matsayinsa, ko mi ne ne addininsa, ko mi ne ne addininsa ya na ko ta na da gudunmawar da zai bayar kan wannan gagarumin aiki.
Ina roƙon dukkan ƴan Nageriya maza da mata da su ba ni cikakken haɗin kai ni da abokan aikina domin samar da kykkyawar fahimtar juna a tsakanin al'ummarmu. Da kuma samar da yanayi na girmama juna da kuma yarda da juna a tsakanin dukkan ƙabilunmu a kuma haɗa kai kan aiki tare da tsayayyiyar manufa da aiki wanda ba ya buƙatar sadaukarwa mai girma.
Na himmatu, ina kuma fatan kuma za ku himmatu, makomar wannan babbar ƙasa ta dogara ne a kanmu da kuma ƙoƙarinmu mu taimaki kanmu, ba za mu iya wannan ba matuƙar ba za mu yi aiki tare cikin haɗin kai ba. Bugu da ƙari, haɗin kai shi ne babban abin da za mu maida hankali akai yau, aiki ne na kowane ɗaya daga cikinmu kowa da kowa mu yi aiki tare da hakan ne za mu zama masu ƙarfi.
A safiyar wannan rana na faɗa a zauren majalissar wakilai cewa saɓaninmu saboda bambance-bambancen jam'iyyu shi ne ya kai Nageriya halin da ta ke ciki a yau. Na roƙi dukkan shugabannin siyasa na ƙasa gaba ɗaya su kauda bambance-bambancen jam'iyyu. Zuwa gare ku masu saurare na a wannan dare na maimaita wannan roƙo a gare ku mu kauda bambance-bambance gefe guda mu tafi tare zuwa ga samun ƴanci.
A ƙoƙarin haɓaka wannan batu na haɗin kai, abokan aikina a majalissar ministoci na yanke shawarar yi wa ƙasa jagoranci ta hanyar gayyatar shugabannin (Action Group) domin samarwa kanmu tsarin gwamnati mai armashi tare da membobin ainahin jam'iyyun da ke ƙasa gaba ɗaya. A kan wannan gaba, ya zama wajibi na yabawa Dakta Azikiwe da Chief Awolawo da Dakta Endeley da kuma shugaban jam'iyyata Sardaunan Sokoto bisa yadda ya amince min kan wannan shawara da na yanke.
Da ni da sauran abokan aikina na NCNC da na NPC za mu haɗa hannu mu yi maraba da membobin Action Group na majalissar ministoci, na yi muku alƙawarin za mu yi dukkan abin da ya dace wajen ganin mun tafikar da harkokin mulki tare da gudunmawar dukkan jam'iyyu".
Sannan kuma ina son na furta kalmomi akan ma'aikatan gwamnati. Mu na yabawa dukkan ma'aikata domin ta hanyar aikinsu Nageriya ta samu nasarar kaiwa matakin cigaba da ta ke kau yau a siyasa. Na sani cewa kowane matakin cigaba na kundin tsarin mulki ya kan haifar da tarnaƙi ga ma'aikata ba wai don an ƙara aiki kaɗai ba amma wasu daga cikin ma'aikata karɓan sabon tsari na ba su wahala, sai dai ya zama wajibi mu nusar cewa yau Nageriya ta kai kan wani ƙarin muhimmin mataki na cigaba, dan haka muddin mu na buƙatar nasara sai mun girmama dukkan ƴan Nageriya da ma'aikata a wannan lokaci kan muradun gwamnati da ta ke son ta cimma.
Cigaban siyasata ba zai zama mai daraja ba matuƙar bai goyi bayan cigaban tattalin arziƙi ba, mu na da dukkan tsare-tsaren da su ka kamata kuma nan da shekaru uku za mu buƙaci duniya ta yi la'akari da mu kan samun ƴanci da tsayayyiyar gwamnati a ƙasa.
Ina mai tunatar da ku abin da wani babba a ƙasar Amurka ya ce "mu haɗa kai mu samu ƙarfi, mu rarrabu mu faɗi". Wannan bayani gaskiya ne yau a Nageriya da kuma duk wata ƙasa. Ya zama wajibi al'ummar Nageriya mu haɗa kai domin cimma burin da mu ka sanya a gaba.
Aiki ne na kowane ɗaya daga cikinmu mu samar da haɗin kai da kuma ƙarfafar sauran al'ummarmu gaba ɗaya su zauna tare cikin zama lafiya da girmama juna. Za mu yi wannan aiki ne ta hanyar samar da fahimtar juna da girmama juna da kuma yarda da juna. Muhimmin al'amari ne mu fahimci cewa sai mun fara nunawa juna girmamawa kafin mu buƙaci duniya ta girmama mu
Da wannan ne na ke yi muku fatan mu kwana lafiya, amma kafin na kammala ina faɗa muku wannan fafutuka saboda makomarku ne da makomar Nageriya wadda kuma ƴaƴanku za su gada, a wannan lokaci kafin samuwar ƴanci akwai buƙatar mu zama masu haɗin kai mu zama masu gaskiya a junanmu da zama masu adalci da sanin duk abin da za mu yi, mu na da tabbacin za mu samu ƴanci kuma za mu same shi akan lokaci.
A daidai wannan lokaci irin wannan ya zama wajibi mu karkatar da zukatanmu zuwa ga Allah mai girma da ɗaukaka mu nemi taimako da agajinsa ba makawa za mu yi nasara".
Jawabi kenan mai cike da kishin ƙasa da ƙaunar al'umma daga bakin marigayi Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, wanda ya gabatar a karon farko a matsayin ministan Nageriya na farko a shekarar 1957.
Allah ya ji ƙansa ya gafarta masa.