01/04/2022
1 ga watan Afrelu, 2022.
Uwargidan gwamnan jihar Gombe, Dr. Asma’u Yahaya, ta raba kayan abincin azumi wa kungiyoyin addinai, nakasassu ,gidaje da daidaikun jama’a maza da mata don kawo dokin fama da tsadan rayuwa ga marasa galihu.
A Safiyar yau ne, Uwargidan gwamnan jihar Gombe, Dr. Asma’u Inuwa Yahaya, ta raba kayan masarufi wa Kungiyoyin addinai,nakasassu, gidaje dama daidaikun jama’a maza da
mata, yayin da aka fuskanci azumin watan Ramadan, domin rage musu radadin zafin tsadar rayuwar yau.
Uwargidan gwamnan, ta samu wakilcin shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar ta na Jewel Care ,wacce aka raba abincin a karkashin ta , Alhaji Hamisu Saulawa, k*ma shugaban mata na jam’iyar APC na jiha ,Mama Lumbi Abubakar,da mataimakan ta na shiya s**a mara masa baya.
Da yake jawabi kafin kaddamar da raba kayayyakin abincin a farfajiyar APC SQUARE, Alhaji Hamisu ya bayyana Cewar, wannan rabiyar abincin ba yau ne Mai dakin gwamnan ta fara yi ba, don kadan daga cikin ayyukan gidauniyar ta kenan na bada tallafin kayan more rayuwa, da s**a hada da kiwon lafiya , samar da ruwan sha , gina ajujuwa karatu a mazabar, gundumomi da karkara.
Saulawan ya Kara da cewa, a wannan makon ne gidauniyar Uwargidan gwamnan tare hadin guiwan gidauniyar kasar Qatar, ta gudanarda aikin cutar yanar gizon idanu, bada magunguna da gilashi kyauta wa mutane sama da dubu uku(over 3000). Ta kara yin hadaka da gidauniyar AMEN kan horas da unguwan zoma a dukkan kananan huk*momi goma sha daya na jihar ,kan gwajin gano cutar Shankarar nono da Muhaifa a matakinta na farko, don dakile cutar ta sankara.
“A jiya-jiyan nan ne ta aika da kayan abinci, dinkakkun tufafi da takalma gidan marayu dake Tunfure , don taimaka musu a matsayin ta na uwa mabada mama. Yau k*ma gashi ta gayyato mata da maza masu karamin karfi ,daga lungu da sakon jihar Gombe, don tallafa musu da kayayyakin abinci yayin da aka fuskanci azumin watan ramadana....Saulawa”.
Shugaban kwamitin amintattu, ya Kara da cewa, uwargidan gwamnan , ta jinjina wa mata wajen hakuri da juriyar tsananin rayuwa da ake fuskanta a yau, inda ta ce da yardan ubangiji za ta cigaba da tallafa wa mata , matasa da kananan yara don samun ingantaccen rayuwa da zaman lafiya mai dorewa a jihar Gombe.
Ita kuwa shugaban mata na jam’iyar APC na jiha, mama Lumbi Abubakar, ta kirayi mata da babban murya don kara nuna goyon bayan su ga Uwar marayu,Dr. Asma’u Inuwa da. Maigidanta, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da yi musu addu’an ALLAH YA kare su daga sharrin masharranta , k*ma ya basu ladan ayyukan da suke yi wa al’umma, da sakamakon alkhairi.
Hamisu Saulawa ya Kaddamar da raba kayan abincin da fara bayar wa kungiyar FOMWAN , CAN , da ta nakasassu, kana daga bisani aka rarraba sauran kayan abincin .
Bintu Aliyu Sunmonu
Babbar mai taimakawa gwamna
na musamman ka yadda labarai
(Ofishin uwargidan gwamna).