21/09/2020
Gwamna Buni Ya Sakanya Hannu Kan Aikin Dindin Ga Ma'aikatan Wucin Gadi Na YTV, YBC
Maigirma Gwamna Mala Buni Ya Sakanya Hannun Yarjejeniyar Bayarda Aikin Dindin Ga Wayanda Suke Aikin Taimakawa Na Wucin Gadi Batare Da Sun Shiga Tsarin Gwamnati Ba Na Sashen Sadarwa Guda Biyu Na Jihar Yobe.
Kwamishinan Sadarwa Na Jihar Yobe Hon Bego Ne Ya Bayyana Hakan A Yayin Da Ma'aikatan Sassa Biyun Kuma Masu Kula Da Lamuran Ganau Wato Kungiyar (RATTAWU) S**a Ziyarceshi A Ofishinsa Dake Damaturu.
Abdullah Bego Ya Bayyana Musu Yanda Gwamnan Ya Cire Makudan Kudade Domin Gyara Wadannan Yankunan Na Labaru Da Tsarin Zamani Na Cigaba.
"Matakin Na Gaba Na Bayarda Horo Ga Ma'aikatan Sadarwa Na Wannan Yankuna Domin Samun Ingantaccen Kwarewa Kusa Da Abin.
Kwamishinan Ya Bayyana Yanda Wannan Kudiri Na Ma'aikata Yakai Kusan Shekaru Takwas Inda Wasu Sunkai 5 Zuwa Shida Ba Tare Da Sun Zama Ma'aikatan Dindin Din Ba.
Kwamishinan Yayi Jinjina Ga Kungiyar Gamayyar Labaru (RATTAWU) Akan Himmarsu Na Nishadantarwa Da Kuma Bayarda Gudumawa Ga Al'ummah.
Shugaban Kungiyar (RATTAWU) Comrade Nasiru Iliya, Ya Bayyana Cewa Munje Ofishinsa Domin yin Rajistar Akan Kudirin Maigirma Gwamna Mai Mala Akan Sashe Guda 2 Na Sadarwa A Jihar.
"Ranka Shi Dade Muna Godiya Kasancewar A Dan Kankanin Lokaci Daga Zama Kwamishina Na Sadarwa Mun Fara Ganin Sauye Sauye Da Ayyukan Cigaba Musamman Akan Wassu Ayyuka Na Kwangila.
Musamman Domin Sabon Tsari ga YTV Da YBC Zuwa Tsarin Zamani.
"Maganan Nan Danake Muku Yanzu Haka YBC Ta Zama Tashar Yanar Gizo Iliya Ya Rufe Da Haka.
Labarin -LEADERSHIP
FASSARAR: Mallam Nura Muhammad Distin ZONAL COORDINATOR EDUCATION R/C YOBE STATE