27/02/2022
Ku gudu zuwa Poland, Gwamnatin Nijeriya ta shawarci ƴan ƙasar mazauna Ukraine
Gwamnatin Najeriya na shawartar 'yan ƙasar da yaƙi ya ritsa da su a Ukraine da su tsallaka zuwa ƙasar Poland mai maƙotaka don samun taimako.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta shawarci 'yan Najeriya su shiga Poland ta kan iyakoki huɗu tsakaninta da Ukraine.
"Ma'aikatan jakadancin Najeriya da masu aikin sa-kai na nan suna jira da motoci don kwashe 'yan Najeriya a kan iyaka," a cewar sanarwar mai ɗauke da adireshin da ta ce 'yan Najeriya su nuna wa jami'an kan iyaka idan sun ƙarasa.
Tun ranar Alhamis Najeriya ta ce za ta shirya aikin ceto na musamman amma daga baya ta ce ba za ta iya ba har sai an buɗe filayen jiragen sama na Ukraine.
A jiya Asabar Ministan Harkokin Waje na Nijeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya gana da jakadun Ukraine da Russia Abuja.
A hannu guda kuma, gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta iya kwashe ƴan ƙasar ba a Ukraine har sai an buɗe filayen jiragen sama a ƙasar da ke fuskantar hare-haren Russia.
Russia na ci gaba da kai hare-hare a Ukraine, bayan da shugaba Putin ya bayar da umarnin mamaye ƙasar.
Ma’aikatar harakokin wajen Nijeriya ta ce ƴan Najeriya 5,600 ne a Ukraine, kuma yawancinsu ɗalibai ne.
Ƙungiyar ɗaliban ta yi kira ga Shugaban Ƙasar Naieriya, Muhammadu Buhari da ya gaggauta kwashe su daga Ukraine.
A ranar Juma’a ne dai Onyeama ya ce gwamnati ta damu da halin da ƴan Najeriya ke ciki a Ukraine.