MAI DOKI HAUSA 24

  • Home
  • MAI DOKI HAUSA 24

MAI DOKI HAUSA 24 Kamfanin jaridar hausa mai zaman kansa wanda yake kawo labarai da s**a shafi al'amuran yau da kullum

23/04/2024

Shugaban EFCC ya yi barazanar yin murabus idan ba a gurfanar da Yahaya Bello ba.

Ya kuma rantse da Allah cewa zai bibiyi shari'ar tsohon gwamnan Kogi har zuwa ƙarshe.

Ola Olukoyede Ya ce duk wanda ya kawo cikas a kokarin k**a Bello doka za ta yi aiki a kansa.

16/10/2023

Kotun ɗaukaka ƙarar da ke zama a Abuja ta ce akwai ƙuri'un da ba halastattu ba cikin waɗanda aka kaɗa wa Mista Abbo na jam'iyyar APC, bisa la'akari da Dokar Zaɓe ta 2022.

28/09/2023

Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya.

28/09/2023

Da Dumi-Dumi

Rudu a hukuncin kotun zaben Kaduna

Uba Sani ya taya kansa murnar nasara a shari'ar zaben Gwamnan Kaduna daidai lokacin da rudani ya mamaye hukuncin kotun ta Kaduna. Lauyoyin PDP sun ce kotu ta ce zaben Kaduna bai kammala ba, yayin da Uba Sani ya yi ikirarin samun nasara a kotu har ya taya kansa murna.

Tashin hankalin da ake fuskanta a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar bai taimaki Najeriya baKamfanonin casar shinkafa ...
27/09/2023

Tashin hankalin da ake fuskanta a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar bai taimaki Najeriya ba

Kamfanonin casar shinkafa da gwamnatin tarayya sun harba farashin buhuna a shekarar nan

Daminar bara ba ta yi kyau sosai ba, sai kuma ga shi ana fama da karancin ruwa sama a shekarar nan

Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta hango babban abin damuwa yayin da zaben gwamnan Kogi da Imo ke ƙara matsowa.Hukumar ta...
27/09/2023

Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta hango babban abin damuwa yayin da zaben gwamnan Kogi da Imo ke ƙara matsowa.

Hukumar ta ce halin rashin tsaron da ke ƙara tsamari babbar barazana ce ga zaɓen.

Ta buƙaci a ƙara tsaurara matakan tsaro domin mutane su samun ikon kaɗa kuri'unsu.

A yau Google ya cika shekara 25 da buɗewa.Wacce gudunmawa ya bawa rayuwarku?
27/09/2023

A yau Google ya cika shekara 25 da buɗewa.

Wacce gudunmawa ya bawa rayuwarku?

Ba ni na kashe Mohbad ba kuma ni ba ɗan ƙwaya ba ne - Naira Marley
27/09/2023

Ba ni na kashe Mohbad ba kuma ni ba ɗan ƙwaya ba ne - Naira Marley

Barkan mu da zagayowar Mauljdi
27/09/2023

Barkan mu da zagayowar Mauljdi

Gwamnatin Kano ta ce za ta maka alkalin kotun zaben gwamnan jihar kan zargin sa da cin mutuncin 'ya'yan Jam’iyyar NNPP d...
27/09/2023

Gwamnatin Kano ta ce za ta maka alkalin kotun zaben gwamnan jihar kan zargin sa da cin mutuncin 'ya'yan Jam’iyyar NNPP da kuma 'yan Kwankwansiyya.

Shafin Facebook ya yi ta tura wa mutane saƙo na cewa sun cancanci samun alamar tantancewar da ake kira “Blue Tick”, wato...
27/09/2023

Shafin Facebook ya yi ta tura wa mutane saƙo na cewa sun cancanci samun alamar tantancewar da ake kira “Blue Tick”, wato “Shudin Maki”, amma fa sai sun dinga biyan kudi har Naira 4,500 duk wata.

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Dakta Olayemi Michael Cardoso a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).
26/09/2023

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Dakta Olayemi Michael Cardoso a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN).

Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun ce sun yanke hukuncin tafiya yajin aikin ne saboda gaza girmama yarjejeniyoyinsu da ...
26/09/2023

Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun ce sun yanke hukuncin tafiya yajin aikin ne saboda gaza girmama yarjejeniyoyinsu da gwamnati ta yi, wadanda s**a cimma kan batun cire tallafin man fetur.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sake fasalin Naira da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), G...
26/09/2023

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sake fasalin Naira da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bullo da shi, kafin zaben da ya gabata, an yi shi ne don kawo cikas ga harkokin zabe.

26/09/2023

Jam'iyyar APC ta yi magana kan N169.4bn da Tinubu ya kashe domin tallafin mai a watan Agusta.

Jam'iyyar ta bayyana cewa an kashe kuɗin ne domin daidaita farashin man fetur.

Ta musanta iƙirarin hadimin Atiku na cewa an dawo da tallafin man fetur ne ta bayan fage.

26/09/2023

Zargin da gwamna Lawal ya yi cewa wasu jami'an FG sun shiga tattaunawa da yan bindiga ya tada ƙura.

Ministan Tinubu ya fito ya zargi gwamnatin Zamfara da sanya siyasa a harkar tsaron al'umma.

To sai dai gwamna Lawal ya sake maida martani mai zafi yau Talata, ya ce yana da hujjoji.

26/09/2023

Sojojin Nijar sun ce dole ne a zauna a fitar da jadawali wanda duka bangarorin s**a amince da shi kan yadda sojojin Faransa za su janye daga Nijar.

A yau, 26 ga Satumba, 2023 ake cika wata biyu da sojojin .Nijar s**a kifar da  gwamnatin Shugaba Mohamed Baozum.Yaya kuk...
26/09/2023

A yau, 26 ga Satumba, 2023 ake cika wata biyu da sojojin .
Nijar s**a kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Baozum.
Yaya kuka ga kamun ludayin sojojin, idan aka kwatanta da na Bazoum?

Dan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaben 2023 Sanata Rabiu Kwankwaso da gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yus...
26/09/2023

Dan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaben 2023 Sanata Rabiu Kwankwaso da gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ranar Litinin sun kai ziyarar ta'aziyya ga kungiyar Izala a ofishinta na Abuja bisa rasuwar fitaccen Malamin nan Sheikh Abubakar Giro Argungu.

Sojoji sun kubutar da 10 daga cikin daliban da ’yan bindiga s**a yi garkuwa da su daga Jami'ar tararyya da ke Gusau a Ji...
26/09/2023

Sojoji sun kubutar da 10 daga cikin daliban da ’yan bindiga s**a yi garkuwa da su daga Jami'ar tararyya da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Kasashen uku wadanda suke karkashin mulkin soji, sun ce za su taimaki junansu duk lokacin da aka kai wa kowacce daga cik...
26/09/2023

Kasashen uku wadanda suke karkashin mulkin soji, sun ce za su taimaki junansu duk lokacin da aka kai wa kowacce daga cikinsu harin soji.

Ban taba karbar cin hanci a rayuwata ba - Mai magana da yawun yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi
25/09/2023

Ban taba karbar cin hanci a rayuwata ba - Mai magana da yawun yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi

Akwai shari’o’i dubu 39,526 a gaban mu — Kotun Ɗaukaka Ƙara
25/09/2023

Akwai shari’o’i dubu 39,526 a gaban mu — Kotun Ɗaukaka Ƙara

Ranar Laraba, 27 ga watan Satumba ce zata zamo ranar hutun Maulidi a Najeriya.Wasu Musulmai na bikin Maulidi ne domin mu...
25/09/2023

Ranar Laraba, 27 ga watan Satumba ce zata zamo ranar hutun Maulidi a Najeriya.

Wasu Musulmai na bikin Maulidi ne domin murnar ranar haihuwar fiyayyen halitta (S.A.W).

Ministan cikin gida, Tunji-Ojo, ya roƙi Musulmai su yi koyi kyawawan ɗabi'un Annabi SAW.

Aliko Dangote ya tafka mummunar asarar Naira biliyan 525 a kwana daya kacal.Wannan asarar ta saka shi a matakin farko a ...
25/09/2023

Aliko Dangote ya tafka mummunar asarar Naira biliyan 525 a kwana daya kacal.

Wannan asarar ta saka shi a matakin farko a Afirka cikin wadanda su ka tafka asara.

Abdussamad Rabiu da Mike Adenuga na daga cikin wadanda su ka tafka mummunar asara.

Nasrun Minallah: Sojoji sun ƙara sheƙe yan bindiga da yawa, sun ceto ƙarin mutane a Zamfara.Rahoto ya nuna yadda sojin s...
25/09/2023

Nasrun Minallah: Sojoji sun ƙara sheƙe yan bindiga da yawa, sun ceto ƙarin mutane a Zamfara.

Rahoto ya nuna yadda sojin s**a tari 'yan ta'addan, aka yi artabu, s**a kashe da dama, saura s**a arce.

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan sojojin sun ceto ƙarin dalibi 7 na jami'ar tarayya, Gusau.

25/09/2023

Tsohuwar minista Sadiya Farouk ta bai gangamin kuɓutar da ɗaliban jami’ar Gusau

DA DUMI DUMINSA: Zamu rabawa Magidanta Kimanin Miliyan 15 Makudan kudade, inji Gwamnatin Tarayya.Gwamnatin Tinubu Za Ta ...
25/09/2023

DA DUMI DUMINSA: Zamu rabawa Magidanta Kimanin Miliyan 15 Makudan kudade, inji Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin Tinubu Za Ta Kaddamar Da Shirin Bada Tallafin Kudi Mai Tsoka Ga Magidanta Milyan 15 Domin Yin Sana'a Ministar jinkai, Misis Betta Edu ce ta bayyana hakan, inda za a soma bada tallafin a cikin watan Oktoba, 2023.

25/09/2023

Kotun Ƙoli ta maida martani kan cece-kucen da ake cewa gobara ta laƙume takardun karar zaben shugaban ƙasa.

Mai magana da yawun Kotu lamba ɗaya a Najeriya ya ce gobarar da ta shafi ƙarar ba ko kaɗan.

Yan sanda sun fara bincike don gano abinda ya haddasa gobara a Kotun da ake ce ma ta Allah ya isa.

Kamfanin Siminti na Ɗangote ya musanta cewa ya rage farashin siminti zuwa ₦2700Rukunin Kamfanin siminti na Ɗangote ya mu...
25/09/2023

Kamfanin Siminti na Ɗangote ya musanta cewa ya rage farashin siminti zuwa ₦2700

Rukunin Kamfanin siminti na Ɗangote ya musanta rahotannin da ke cewa ya rage farashin siminti da kaso 50 cikin 100 a ranar 1 ga Oktoba, 2023 k**ar yadda rahoton ke yawo a wasu kafofin yaɗa Labarai dake dandalin sada zumunta ”

“A cikin saƙonnin daban-daban kuma da aka riƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta da dama ciki har da manhajar WhatsApp da dai mak**antansu da aka ce Dangote ya rage farashin siminti daga ₦5500 zuwa ₦2700, saidai rukunin kamfanin ya nesanta kansa da waɗannan rahotonnin k**ar yadda binciken Jaridar MAI DOKI HAUSA 24 ta samu tabbacin wannan saƙo a yau Litini 25/09/2023.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MAI DOKI HAUSA 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share