12/01/2025
Taurarin Kannywood bakwai da s**a yi tashe a 2024
Shekarar 2024 ta kasance cike da abubuwa masu yawa, musamman a bangaren nishaɗi wanda ya zama wani ɓangare na rayuwar mutane wajen kawar da damuwa da samun nishadi.
A cikin shekarar, akwai jarumai da dama da s**a yi fice sosai, la'akari da yawan rawar da s**a taka a finafinai da yadda s**a samu karɓuwa a wajen masu sha’awar Kannywood da finafinan Hausa.
Sadiq Sani Sadiq
Sadiq Sani Sadiq shi ne jarumin fim ɗin Labarina, inda ya fito a matsayin Alhaji Mainasara. A cikin fim ɗin, yana da mata biyu, Maryam da Dokta Asiya. Haka kuma, ya fito a wasu shirye-shiryen finafinai k**ar Manyan Mata da sauransu.
Zahrah Muhammad
Zahrah Muhammad, da aka fi sani da Diamond Zahra a masana'antar Kannywood, ta samu karbuwa sosai a shekarar 2024. Ta taka rawar gani a finafinai da dama, ciki har da Labarina, inda ta fito a matsayin Dokta Asiya, matar Mainasara kuma kishiyar Maryam.
Maimuna Gombe Abubakar
Maimuna Abubakar, wacce ake wa lakabi da Momee Gombe a Kannywood, ta fito ne a cikin fim ɗin Gidan Sarauta. Ita ce jarumar da ta haskaka fim ɗin wanda ke da dogon zango kuma yana tashe a shekarar 2024. Haka kuma, ta bayyana a cikin fim ɗin Manyan Mata, wanda ya haɗa manyan jarumai da dama.
Firdausee Yahaya
Bayan fitowarta a fim ɗin Labarina, Firdausee Yahaya ta ci gaba da jan hankalin masu kallo a cikin wasu finafinai, ciki har da Manyan Mata, Allura Cikin Ruwa, Garwashi, da Jamilun Jiddan, wanda ake shirin fara haskawa a watan Janairun 2025.
Fa'iza Abdullahi
Fa’iza Abdullahi ta yi fice a cikin fim ɗin Daɗin Kowa na dogon zango, inda aka fi saninta da sunan Bilki mai abinci. Wannan fim ya sanya ta haskaka a masana’antar Kannywood, duk da cewa ta bayyana a wasu finafinai da dama.