21/06/2023
TUSHEN BAHAUSHE
Daga ina Mal. Bahaushe ya fito? Mafi saukin sanin wannan zamu duba harshensa, Hausa, daga ina ta fito? Wa ya kirkiro harshen?
Farkon harshen Bahaushe ya yi asali ne daga Proto-language da ake kira Afro-Asiatic. Zan kira shi Tushen Harshe. Ya yi rasa inda ya haifar da harsuna kusan 300 da ake magana da su a yau, a sassa daban daban, Magrib, Sassan Habasha zuwa Masar (horn of Africa), Asiya ta Yamma, da Sahara/Sahel. Dukkan rassansa ana magana da su a Africa sai reshen Semitic da yake a Asiya ta Yamma.
RASSAN TUSHEN HARSHE
Rassan Tushen Harshe sun kinshi:-
1. Berber
2. Chadic
3. Cush*tic
4. Egyptian
5. Semitic
6. Omotic
Reshen Semitic ya kunshi:-
Arabic
Akkadian,
Hebrew,
Phoenician,
Caananite languages,
Amorite,
Ugaritic
Aramaic
Reshen Chadic ya kunshi
Chadic Ta Yamma
1. Hausa, Ron, Bole, da Angas.
2. Bade, Warji, da Zaar.
Chadic Ta Tsakiya
1. Bura, Kamwe Bata
2. Buduma da Musgu
3. Gidar
Chadic Ta Gabas (CHADI)
1. Tumak, Nancere, da Kera
2. Dangaléat, Mukulu, da Sokoro.
3 Masa
Hakika an samu sabani daga manazarta cewa a ina ne mutanen da s**a kirkiro Tushen Harshen s**a zauna? Mafi yawansu sun yarda a Africa ta Gabas ne s**a fara zama. Ko shakka babu an samu kabilanci cikin nazarin. Akwai wadanda s**a ce Levant (Sham) ne, wanda kabilanci ne zalla. An kawo gabacin Masar, amma mafi yawan manazarta sun karbi sassan Habasha (horn of Africa).
A wace shekara ce masu Tushen Harshe s**a fara zama? To manazarta sun kiyasta lokuta daga 7,500 BC (shekara 9,500 da s**a wuce) zuwa 16,000 BC (shekara 18,000 da s**a wuce). Igor M. Diakonoff (1988) ya ce ana magana da Tushen Harshe tun 10,000 BC. Christopher Ehret (2002) ya kiyasta tun a kalla11,000 BC zuwa16,000 BC. Amma wadandan Ehret C, et al (December 2004) ne s**a kawo bayanan (as quoted by...). Wadannan lokuttan sun wuce duk wani proto-language tsufa. Saboda haka babu kuskure idan aka ce Hausa tana daga cikin harshe na farko da Dan Adam ya fara magana da ita.
YAUSHE NE YAN