Hausa/Fulani TV

  • Home
  • Hausa/Fulani TV

Hausa/Fulani TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hausa/Fulani TV, TV Channel, FCT Abuja, .

SANARWA! WONDER LIVES FOUNDATION KATSINA Ina masu Sha'awar koyan Sana,oi ga dama tasamu gidauniyar fito da tsarin *Skill...
17/03/2024

SANARWA!
WONDER LIVES FOUNDATION KATSINA Ina masu Sha'awar koyan Sana,oi ga dama tasamu gidauniyar fito da tsarin *Skills acquisition program* inda zata koyar da matasa Maza da mata sama da dari Sana,ar dazasu dogara da kansu Koda bayan karatune wannan program zai hada da masu karatun Boko ko wanne mataki da Wanda Basu dashi,
Sana,oin daza,a koyar sun hada bangarori K**ar haka: *
✓Na,ura Mai Kwakwalwa,
✓Dinki
✓Girke-Girke
✓Turaren wuta,
✓ Gyaran jiki,
✓Sabullai,
✓Kwalliya da sauransu.

Kusani akwai sauki da rangwame acikin tsarin karatun tareda Aiki na zahiri (PRACTICAL ) Sannan Kyauta ne ga marayu da gajiyayyu Wanda s**a cancanta.

Kudin form Dari biyar #500 ne kacal.
An bude siyar da form daga yanzu harzuwa 15/4/2024.

Za,a kulle Registration 20/4/2024
Za,a iya samun form a farfajiyar makarantar MODIBBO ACADEMY KAMBARAWA HAJJ CAMP. KATSINA

Domin Karin bayani ko siyan form atuntubi
Shuwagabanin gudanarwa na wannan shiri ko akira waya ko sakon SMS ko Kafar sadarwa ta WhatsApp:-
08067549931
09064505281
08105978365
MUN GODE
SANARWA DAGA:-
IBRAHIM AMINU RUMAH
REGISTERER.
(SKILLS ACQUISITION PROGRAM) WONDER LIVES FOUNDATION.

Gidauniyar Home Of Hospitality Development Initiatives(HOHDI) Takaiwa  'Yan Gudun Hijirar  'Yargoje Da Burdugau Tallafi ...
14/03/2024

Gidauniyar Home Of Hospitality Development Initiatives(HOHDI) Takaiwa 'Yan Gudun Hijirar 'Yargoje Da Burdugau Tallafi Abinci A Karamar Hukumar Kankara Jihar Katsina.

✍️Mannir Idris Kankara

A ranar 13/3/2024 gidauniyar Home Of Hospitality Development Initiatives takaiwa al'ummar dake gudun hijira dake yankunan Yargoje da Burdugau tallafi.

Gidauniyar Home Of Hospitality Development Initiatives (HOHDI) gidauniya ce Mai zaman kanta wadda aka kafa domin tallafawa al'umma. dake bukatar tallafi ta bangarori daban daban k**ar samar da zaman lafiya,bangaren koyawa al'umma sana'o'i, domin dogaro dakai, samar da ilmi ga sl'umma da sauran al'amuran cigaban kasa.

Awannan karon Gidauniyar HOHDI ta tallafawa masu gudun hijiarar da Yan ta'adda s**a rabo da gidajensu ta hanyar harbi da kone mazuani hadi da yin garkuwa mazauna kauyukan yanki.

Malama Aisha Abdulrashid Kankara wadda itace , shuagabar (Team Leader) gidauniyar ta karamar hukumar kankara ta jagoranci mika wadannan kaya ga masu hijira ayau.

Yayin mika tallafin Malama Aisha Ta bayyana gidauniyar ta Samar da kayan abincin ne ga mutane 200 wadanda s**a kunshi Maza da mata inda aka dauki mutane 100 Ako wane yanki da abun yashafa inda s**a amfana ko wannen su yasamu Garin Kwaki kwano daya da Garin kuli kwata da kakke.

Shugabar ta bayyana gidauniyar tayi hakan ne saboda ganin irin halin da jama'a ke ciki na rashin cikkakken matsugunni.

Wasu daga cikin wadanda s**a amfana sun nuna godiyar su ga gidauniyar ga bisa talfafamasu da wannan kayan abinci .

Al'ummar sun kuma gode da hanyar da aka bi wurin raba masu a kai tsaye hannu zuwa hannu.

Cikin wadanda s**a gudanar da aikin rabon tallafin sun hada da Abdul Male,Hajiya Rayya Male, Malama Aisha Musa Shehu hadi da taimakon jami'an tsaron Katsina State Community Watch Corps domin bada tsaro.

Gidauniyar na sanar da al'umma kofa abude take ga masu dama da niyyar taimakawa ga Account Number 👇
1461211077
Access Bank

GAYYATAR DAURIN AURE Amadadin Iyalan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comr. AMINU ABDUSALAM GWARZONSuna Gayyatar Ku Zuwa Da...
17/02/2024

GAYYATAR DAURIN AURE
Amadadin Iyalan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comr. AMINU ABDUSALAM GWARZON
Suna Gayyatar Ku Zuwa Daurin Auren Diyar Shi HAFSAT AMINU.

Rana24

INNALILLAHI WA'INNA ILAHIRRAJIUNAllah yayiwa Alhaji Hamisu Yusuf Jarman Kahutu Rasuwa.Marigayin Hamisu Yusuf Kafin Rasuw...
04/01/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAHIRRAJIUN
Allah yayiwa Alhaji Hamisu Yusuf Jarman Kahutu Rasuwa.

Marigayin Hamisu Yusuf Kafin Rasuwarshi Shine Jarman Kahutu Ta Karamar Hukumar Danja Dake Jihar Katsina.

Ya Rasu Ayau Alhamis A Asibitin Garin Shika Dake Jihar Kaduna.

Za'a Gudanar Da Janazar Maragayin A Gobe Juma'a Agarin Kahutu Da Misalin Karfe 10:00.

Allah yajikshi da rahama Amin.p

Katafaren sayar da suturu na SANTIAGO SPECIAL BOUTIQUES KANKARA na yiwa Al'ummar maza da mata marhabun lale domin ya Sam...
30/12/2023

Katafaren sayar da suturu na SANTIAGO SPECIAL BOUTIQUES KANKARA na yiwa Al'ummar maza da mata marhabun lale domin ya Samar maku kayayyakin sawa na maza da mata yara da manya iri daban daban.

Kayayyakin das**a hada:
•Shadodi
•Atamfofi
•Lasususs**a
•Yadudduka
•Kayan Yara Yan Kanti.
•Takalman Maza Da Mata
•Jikkuna.
•Da sauran kayayyakin masu nagarta Cikin sauki da rangwame.

SANTIAGO SPECIAL BOMOUTIQUES Na Nan Kusada gidan Marigayi Alhaji Babajo Lawal S/Pauwa Kankara Kuma ko akira 07037279262

Na Fatan Alheri agareku Ashiga Sabuwar Shekara lafiya.

Gwamnatin Jihar Katsina Bazata Ja Da Baya Ba, Ko Mika Wuya Akan Samar Da Tsaro Don Ganin An Kawar Da ‘Yan Bindiga A Jiha...
29/12/2023

Gwamnatin Jihar Katsina Bazata Ja Da Baya Ba, Ko Mika Wuya Akan Samar Da Tsaro Don Ganin An Kawar Da ‘Yan Bindiga A Jihar.

Daga: Mannir Idris Kankara

Mataimakin gwamnan jihar Malam Faruk lawal HCIB ya bayyana haka a lokacin da ya jajantawa iyalan marigayi Malam masaudu na kauyen kwanar dutse da ke karamar hukumar safana.

Malam masaudu wani jami’in sa ido a Katsina ya rasa ransa a bakin aiki yayin da yake kokarin dakile wani hari da ‘yan bindiga s**a kai ranar Laraba.

Yana aiki tare da takwarorinsa da mambobin kungiyar ’yan banga a yankin.

An bayyana marigayi Malam masaudu a matsayin jajirtacce kuma kwazon jami’in sa ido na al’umma.

Tuni dai akayu Jana'izar shi bisa Tsarin Addinin Musulunci.

Jaridar Rana24 ta ruwaito Mataimakin gwamnan jihar Malam Faruk Lawal yayin da yake mika ta'aziyyarsa ya jinjinawa jami'in da aka kashe tare da yi masa addu'ar Allah ya jikansa.

Ya kuma kara da cewa niyyar gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa jami’an tsaro domin kawar da ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

Ya kara tabbatar da cewa gwamnatin jihar a yanzu ba za ta sake shiga wata tattaunawa da ‘yan bindiga ba.

Malam Faruk Lawal ya jaddada cewa za a gano su a duk inda s**a boye.

Ya kuma yi kira da a tallafa wa al’umma ta hanyar samar da bayanan da s**a dace ga hukumomi domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Al'ummar kwanar dutse sun yaba da ta'aziyyar tare da tabbatar da goyon bayan gwamnati don tabbatar da 'Yancin Al'ummomin.

Haka zalika mataimakin gwamnan ya jajantawa Alhaji Awwalu sada safana bisa rasuwar diyar sa fiddausi sada.

Fiddausi mai shekaru 32 ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ta bar 'ya'ya 3 mijinta, iyayenta da danginta.
Tuni dai aka Jana'izar ta k**ar yadda addinin Musulunci ya tanada .
Allah ya jikanta da rahama.

Mahaifin marigayin ya godewa Mataimakin Gwamna Malam Faruk lawal bisa wannan ta'aziyyar.

An Ƙaddamar Da Shirin Farfado Da Shirin Tattalin Arziki A Jihar Katsina Na Covid 19 A Shiyyar Funtua.Daga : Mannir Idris...
15/12/2023

An Ƙaddamar Da Shirin Farfado Da Shirin Tattalin Arziki A Jihar Katsina Na Covid 19 A Shiyyar Funtua.

Daga : Mannir Idris Kankara

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe HCIB(Sarkin Fulanin Joben Katsina) ne ya kaddamar da shirin a madadin gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda PhD.

Wakilin Rana24 a Funtua ya ruwaito Makasudin shirin shine fadada hanyoyin samun tallafin rayuwa da wadatar abinci ta hanyar ayyuka da tallafi ga al'umma mabukata ta hanyar manoma.

Malam Faruk Jobe ya bayyana cewa shirin wani shiri ne da aka samar a cikin gida na shirin kula da Nigeria wanda Bankin Duniya ke tallafawa da nufin rage yunƙuri da ƙalubalen da ke tattare da cutar ta Covid 19 da shafama abaya.

📷 Al-amin Katsina

Kungiyar Kankara Youths Forum (KYF) Ta Gudanar Da Gasar Wasa Kacici-Kacicin Late Yakubu NadsboA Tsakanin Makarantun Fira...
04/12/2023

Kungiyar Kankara Youths Forum (KYF) Ta Gudanar Da Gasar Wasa Kacici-Kacicin Late Yakubu NadsboA Tsakanin Makarantun Firamaren Kankara

A ranar Lahadi 3/12/2023 Kungiyar Matasa Karamar Hukumar Kankara mai Kankara Youths Forum ƙarƙashin Jagorancin Comr. Kabir Abdullahi s**a Kammala gasar da s**a shirya atsakanin Makarantun Karamar hukumar Kankara.

Taron daya gudana a dakin taron hukumar Ilmin Karamar Hukumar Kankara LEA HALL.

Jawabin maraba daga Shugaban Kungiyar Comr. Kabir Abdullahi yayiwa al'ummar da s**a Halarci taron barka da zuwa ya kuma bayyana dokokin yadda gasar zata kasance domin gujewa Yashin tashina ayayin Gasar.

Bayan Kammala jawabin shi afara fafatawa da shirin Kacici-Kacici inda daga karshe Makarantar Firamare Unity Nursery And Primary School Kankara da zama ta daya inda màkaranatar Uncle D Memeorial International School ta zamo itace ta Biyu.

Bayan Kammala gasar Kacici-Kacici ne aka gudanar da gasar Spelling B inda awannan bangaren kuma Makarantar Uncle D Memeorial International School ta zamo ta Daya ,Hashim Day Girls Primary School Kankara ta zaki ta biyu.

An bada kyaututtuka ga dukkanin Makarantun 8 da s**a samu damar halartar wannan gasar, Makarantun sune Nuhu Model Primary School Kankara,Lawal Primary School Kankara,Hashim Girls Day Primary School,Unity Nursery And Primary School, Uncle D Memeorial International School,Pilot Science Primary School da Kuma Sheikh Abubakar Muhmud Gumi Primary School.

Uwargidan Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Asma'u Faruk Lawal Jobe (Sarkin Fulanin Joben Katsina) wadda ta samu wakilcin Malama Hafsat Bature Darda'u ta bayyana sakon Uwargidan Mataimakin Gwamnan na yiwa duk Makarantun da s**a dauki lamba ta daya akwai kyautar dazata ba wannan Makarantu.

Sannan Hajiya Asma'u Faruk Jobe ta godewa Waɗannan Kungiyar matasa duba da yanda s**ayi amfani da kudaden aljihun su awurin tsarawa da kuma Gudanar da wannnan gasa atsakanin Makarantu.

Akkn Kuma Gudanar da Bayayin Tarihin Maragayi Alhaji Yakubu Nadabo a

Ma'aikatar Ilmin Bai Daya Ta Jihar Katsina Reshen Karamar Hukumar Kankara Ta Karrama Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Gidan ...
26/11/2023

Ma'aikatar Ilmin Bai Daya Ta Jihar Katsina Reshen Karamar Hukumar Kankara Ta Karrama Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina.

Wannan karramawa dai ta biyo bayan gagarumar gudunmuwa da Namijin kokari da matashin ke bawa bangaren ilimi a karamar hukumar.

Lambar Yabon ta fito ta hannun Education Secretary na wannan karamar hukuma Wato Malam Yusuf Ali.
Bayan yabo, godiya da Kuma jinjina ga matashin, yayi kira ga matasan Yan siyasa da suyi koyi da irin halinsa Don ciyar da Al'umma da Kuma wannan yanki a gaba.

*Gwagware Jobe Ambassadors*

SANARWA DAGA KANKARA STIDENTS UNION (NATIONAL BODY)Kungiyar Dalibai Ta Karamar Hukumar Mulki Kankara nasanar da wadanda ...
14/10/2022

SANARWA DAGA KANKARA STIDENTS UNION (NATIONAL BODY)
Kungiyar Dalibai Ta Karamar Hukumar Mulki Kankara nasanar da wadanda s**a cike fom din shirin da zata gudanar Na Horas da Sana'o'i ENTERPRENUERSHIP Dasu Halarci Taron Kaddamar Da Fara Shirin Bayar Da Horon Wanda Za'ayi K**ar Haka:

Ranar: 15/10/2022
Lokaci:9:00 - 11:00
Wuri: Read Room Kofar Fada (WOMEN CENTRE) Kankara

Zankadeden nāmji ne sunan sa Idris Okuneye amma anfi saninsa da Bobrisky,Iyayensa mű§ulmai ne na hakika amma shi ya zabi...
21/09/2022

Zankadeden nāmji ne sunan sa Idris Okuneye amma anfi saninsa da Bobrisky,

Iyayensa mű§ulmai ne na hakika amma shi ya zabi zama D0n D@udu kodayake ya sha fadawa duniya cewa abuņdã yake yi ya sab@wa k0yarwaar addinįn mūsolünci.

Hotunan Yadda Gwamna Ganduje Yagina Katafariyar Kasuwar Zamani Kano Economic City a garin Ɗan Gwauro dake titin Zaria.Da...
21/09/2022

Hotunan Yadda Gwamna Ganduje Yagina Katafariyar Kasuwar Zamani Kano Economic City a garin Ɗan Gwauro dake titin Zaria.

Daga Adam Hassan, Chairman Gawuna/Murtala Reporters Kano State.

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano
Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, tare da Maitamakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna sun kai ziyarar duba yadda aikin ginin kasuwar zamani wato Kano Economic City wacce gwamnatinsa ke ginawa a garin Dan Gwauro dake kan titin zuwa Zaria.

Gwamnan ya miqa takardun mallakar shaguna ga wasu daga cikin wadanda s**a mallaki shaguna bangaren masu siyar da magunguna wanda aka kamma wani shashi kuma ake dab da kaddamarwa.

Gwamnati Cikin Gwamnati.....Farfajiyar Bello Turji a ƙauyen Fakai jihar Zamfara Ƴan ƙwanaki kafin Sojan jirgin Saman Naj...
20/09/2022

Gwamnati Cikin Gwamnati.....

Farfajiyar Bello Turji a ƙauyen Fakai jihar Zamfara Ƴan ƙwanaki kafin Sojan jirgin Saman Najeriya s**ai mashi hari.

Mamman Bashar Kanoma

YANZU-YANZU: Atiku Abubakar ya gana da jaruman  fitaccen film din tsaraicin nan mai suna BBNaija  a Jihar legas, domin t...
19/09/2022

YANZU-YANZU: Atiku Abubakar ya gana da jaruman fitaccen film din tsaraicin nan mai suna BBNaija a Jihar legas, domin taya shi yakin neman Zabe, K**ar yadda Jaridar Daily African Newspaper ta rawaito

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka birnin Amurka domin halartar taron shuwagabannin kasashen Duniya karo na 77Me kuke so ...
19/09/2022

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka birnin Amurka domin halartar taron shuwagabannin kasashen Duniya karo na 77

Me kuke so Buhari ya yi magana akai a lokacin jawabinsa a wajen taron?

Mutumin Da Ya Tattaki akan Buhari A 2015, Yanzu ya Fara yawo Da Akwatin Gawar APC.
18/09/2022

Mutumin Da Ya Tattaki akan Buhari A 2015, Yanzu ya Fara yawo Da Akwatin Gawar APC.

Banike a Minna jihar Neja ya Kera Baron dakon Kaya Mai dauke da inji na tafiyaDaga Elhajji Awwerl Minna Wani Bakaniken M...
16/09/2022

Banike a Minna jihar Neja ya Kera Baron dakon Kaya Mai dauke da inji na tafiya

Daga Elhajji Awwerl Minna

Wani Bakaniken Mashin a garin Minna Jihar Niger Unguwar Tudun natsira Wanda ya kera Baro na diban kaya ko shara Mai amfani da Injin, "Inda Jaridan ALFIJIR HAUSA ta bibiya lamarin turyan-turyan bisani ta bayyanawa duniya.

Bakaniken Mai Suna injiniya Mathew Ya bayyana irin farin cikin da yake ciki na kera baron ganin yadda Jama'a keta tururuwan zuwa gani tare da yaba masa na irin basiran da allah yabashi.

Yace Kawai ya a zaune yaji abun ya fado mashi a rai, kuma cikin taimakon Allah sai gashi ya samu nasaran hada abun a tsakanin Kwana 7.

ALFIJIR HAUSA tattaro maku cewa; Injiniyan Yace Yana, Niman tallafin Gwamnati dama sauran Yan kasuwa domin bunkasa wannan basiran nashi da samun sauki na Al'umma wurin daukan kaya ko kuma masu daukan dako.

Da Na Yi Tattaki Daga Garin Dirin Daji Dake Jihar Kebbi Zuwa Wata Jiha Da Sunan Ganin Wani Mawaki Ko Dan Fim, Gara Na Yi...
13/09/2022

Da Na Yi Tattaki Daga Garin Dirin Daji Dake Jihar Kebbi Zuwa Wata Jiha Da Sunan Ganin Wani Mawaki Ko Dan Fim, Gara Na Yi Tattaki Don Zuwa Ganin Sheik Dahiru Bauchi, Ko Banza Zan Samu Addu'a Da Kuma Tubarraki

Cewar Murjanatu Diri

DA DUMI-DUMINSA: Jami'an 'Yan Sanda Sun Dakile Wani Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane Da 'Yan Bindiga S**a So Yi A Kaduna
12/09/2022

DA DUMI-DUMINSA:
Jami'an 'Yan Sanda Sun Dakile Wani Yunkurin Yin Garkuwa Da Mutane Da 'Yan Bindiga S**a So Yi A Kaduna

An Sace Makarar Daukar Gawa A Wani Masallaci Dake Unguwar Hayin Banki A Jihar KadunaDaga Taskar Labarai Wani dan Jarida ...
12/09/2022

An Sace Makarar Daukar Gawa A Wani Masallaci Dake Unguwar Hayin Banki A Jihar Kaduna

Daga Taskar Labarai

Wani dan Jarida Shuaibu Abdullahi ya bayar da labarin cewa makarar da aka sace ta karfe ce a wani masallaci dake Unguwar Hayin Banki, har ma'ana danganta batun da masu siyar da karfe a kan sikeli a cikin Unguwanni wato 'yan gwan-gwan.

Yace Limamin Masallacin ne ya fada a yayin hudubar Juma'a, inda yayi tsokaci tare da jan hankali kan satar kayan mutane musamman a masallatan Unguwanni.

Yawaitar Matasa Masu Maula A Wuraren Ɗaurin Aure Ko Wurin Zaman Gaisuwa....Lamarin Maula a tsakanin Matasa yana ta ƙara ...
08/09/2022

Yawaitar Matasa Masu Maula A Wuraren Ɗaurin Aure Ko Wurin Zaman Gaisuwa....

Lamarin Maula a tsakanin Matasa yana ta ƙara ɗaukar wani sabon salo, tare da ƙara ta'azzara Musamman a wuraren bukukuwan Ɗaurin Aure, wajen zaman gaisuwa musamman na manyan Mutane da ma Ma'aikatun Gwamnati.

Wannan Al'amarin dai baya da tak**aimai wuri kusan ko'ina ka zagaya zakaga irin waɗannan Matasan sunata ƙara yawaita abin takaici kuma zaka tarar dasu ƙarfafa masu jini a jika amma sun kashe zukatan su wajen Maula.

Dazarar sunga Mota mai Ɗan sheƙi ko s**a ganka da rigar Mutunci sai kaji ana Oga ga Yaranka ko ranka yadaɗe muna gaisuwa da sauran kalamai mak**antan wannan.

Idan kayi Magana sai kaji wasu na cewa wai ai babu aikin yi shiyasa Mutane s**a koma irin wannan ɗabi'ar, Lamarin da na kasa yadda dashi har yanzu.

Shin wai ina Matsalar take kuma yaya za'a gyara ?

Matsalar shine wasu Matasa suna son jikin su dayawa da dama sun tsugunna suna jiran sai aiki yazo ya same su basu zasuje su nemeshi ba, ga kuma raina ƙaramar sana'a.

Matuƙar dai bamu taru mun yaƙi wannan mummunar ɗabi'ar ba haka Matasan zasu ci gaba da ganin cewa abinda sukeyi dai daine kuma babu ranar dainawa.

Da Ɗumi Ɗuminsu; Hukumar dake kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ta haramta sanya Waƙar Ado Gwanja ma taken "WARR"...
08/09/2022

Da Ɗumi Ɗuminsu; Hukumar dake kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC ta haramta sanya Waƙar Ado Gwanja ma taken "WARR" a gidajen Radiyo da Talabijin a faɗin ƙasar nan.

A cewar takardar Sanarwar Hukumar ta lura cewa Waƙar ta karade Gidajen radio da Talabijin a faɗin Arewacin ƙasar nan, sannan akwai yiyuwar masu Gidajen kafafen yaɗa labaran basu saurari Waƙar da kyau ba domin tana ɗauke da wasu kalamai na rashin Ɗa'a.

DA DUMI-DUMINSA: Wani Jigon Boko Haram Ya Mika Wuya A Garin Bama Dake Jihar Borno Bayan Ya Sha Wuya A Hannun Sojojin Nij...
05/09/2022

DA DUMI-DUMINSA:
Wani Jigon Boko Haram Ya Mika Wuya A Garin Bama Dake Jihar Borno Bayan Ya Sha Wuya A Hannun Sojojin Nijeriya

HOTO: Kai Tsaye Yadda ake wayar da Kan 'yan Takarar Gwamnan Jihar Kano Gawuna & Garo, Abba Gida Gida & Comrd Aminu Abdul...
04/09/2022

HOTO: Kai Tsaye Yadda ake wayar da Kan 'yan Takarar Gwamnan Jihar Kano Gawuna & Garo, Abba Gida Gida & Comrd Aminu Abdulsalam Gwarzo.

DA DUMI-DUMI: dakarun sojojin Najeriya sunyi Nasarar tarwatsa sansani na karshe na yan Boko haram a dajin Sambisa, Wanda...
01/09/2022

DA DUMI-DUMI: dakarun sojojin Najeriya sunyi Nasarar tarwatsa sansani na karshe na yan Boko haram a dajin Sambisa, Wanda a Jima ana bata kashi, a kalla yan boko haram 56 da Shida ne su bakunci lahira,

© Mai Dara Katsina Media

01/09/2022

Anyi Nasarar K**a Wani Mugun Ɗan Ta'ada Dake Safarar Mak**ai Tsakanin Jihohin Arewa.

Asirin wani mugun tsohon Soja ya toni Inda Jami'an tsaron Ƴansanda s**ayi nasarar chafke shi yayinda yake kan hanyar shi ta safarar Mak**ai zuwa jihar Zamfara daga jihar Nasarawa.

Wanda Jami'an tsaron s**a k**a tsohon Soja Cpl Sa’idu Lawal Ɗan kimanin Shekaru 41 a Duniya an k**ashi da abubuwa k**ar haka;

1 AK-47 Rifle Breech No. Q971987
1 AK-49 Rifle Breech No. 34-7094
200 7.6mm Rounds of Live Ammunition
501 7.62X51mm Rounds of GPMG Live Ammunition
8 Empty Magazines

Lamarin rashin tsaro dai yana Ci gaba da addabar Jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger, Kebbi da jihar Sokoto, a ranar 27th August, 2022 da misalin ƙarfe Biyar da Rabi na Yammaci Jami'an Ƴansanda da suke aiki tare da ƙwamishinan ƴansandan jihar Zamfara, CP Kolo Yusuf psc s**a samu bayanan sirri da s**ayi sanadiyyar kamun tsohon Sojan Wanda yayi aiki ƙarƙashin Bataliya ta Saba'in da Ukku 73 dake Barikin Sojoji ta Janguza jihar Kano.

An dai k**a Wanda ake zargin ne da Mota ƙirar Pontiac Vibe Mai ɗauke da lamba KRD 686 CY Lagos, akan hanyar Abuja – Kaduna bisa hanyar shi ta zuwa jihar Zamfara, yayinda aka bincike shi shine aka samu waɗannan Miyagun Mak**ai a tare dashi.

Yayin da yake amsa tambayoyin Jami'an tsaron ya tabbar da cewa ya ɗakko waɗannan Mak**ai ne daga ƙaramar hukumar Loko ta jihar Nasarawa zai kuma kaisu ga wani Dogo Hamza dake ƙauyen Bacha cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Wanda ake zargin ya tabbar da cewa a baya ya zamo mai Safarar Mak**ai a Jihohin Kaduna, Katsina, Niger dama jihar Kebbi Jami'an tsaro sun tabbar da cewa suna bincike domin samun sauran Abokan ta'adancin nashi.

Rundunar Ƴansandan Najeriya Reshen Jihar Katsina Ta K**a Ƴanfashi Da Makami Da Masu Garkuwa Da Mutane.A Yau Laraba Talat...
31/08/2022

Rundunar Ƴansandan Najeriya Reshen Jihar Katsina Ta K**a Ƴanfashi Da Makami Da Masu Garkuwa Da Mutane.

A Yau Laraba Talatin da Ɗaya 31 ga watan Agusta rundunar ƴansanda a jihar Katsina ta gabatar da Mutane Goma Sha Tara, ga manema labarai da ake zargi da laifuka daban-daban a faɗin jihar.

Da yake gabatar da jawabinsa ga manema labarai, Ƙwamishinan Ƴansandan jihar Katsina CP Idris Dauda Dabban ya bayyana, gungun ƴan fashi da makami da Ɓarayin Motoci da aka kamo daga jihohin Kano, Bauchi, Jos da kuma Katsina, kazalika kuma an gurfanar da masu garkuwa da mutane guda Bakwai daga ƙaramar hukumar Danja.

An samu Motoci guda Goma sha Ukku, da Rasiɗin mota da suke haɗawa na bogi da hatimin da suke bugawa Rasiɗan da sunan saida Motocin. Akwai sauran nau'ikan mak**ai da s**a haɗa da Adduna Wuƙake da makullen Motoci daban-daban, da ma Lambobin Motoci daban-daban.

A wani samamen kuma da rundunar ƴansanda ta jihar Katsina ta gudanar a ranar sha Biyu 12 ga watan Agusta sun dira maɓoyar Ƴan bindiga a garin Babban Duhu dake ƙaramar hukumar Safana, inda s**a isa maɓoyar masu garkuwa da mutane, s**a samu bindiga AK47 Guda da alburusai. Rundunar ta ce tana nan tana tsananta bincike akan lamarin

Da yake ƙarin haske akan masu laifin kakakin Rundunar ƴansandan jihar Katsina SP Isah Gambo ya bayyana waɗanda ake zargin Ɗaya bayan ɗaya da kuma laifukan da ake zargin sun aikata, kuma wasunsu sun tabbatar da laifin nasu a gaban manema labarai.

Annabi Muhammad Shine Wanda Ya Fi Kowane Mutum Nagarta, Cewar Rani Mukerji"Annabi Muhammad mutum ne mai inganci wanda a ...
31/08/2022

Annabi Muhammad Shine Wanda Ya Fi Kowane Mutum Nagarta, Cewar Rani Mukerji

"Annabi Muhammad mutum ne mai inganci wanda a tarihin ɗan Adam har yanzun babu k**ar sa, na karanta rayuwarsa da halayensa, sai na gane cewa Annabi Muhammad ya fi kowa nagarta." Inji Rani Mukerji

Rani Murkeji wacce addininta Hindu ne, shahararriyar ƴar fim ɗin Indiya ce da ta lashe kyaututtuka da dama don kwarewarta a harkar fim.

Hotuna masu ɗauke da saƙo mai muhimmanci ga matasa.Ko wane sako kuka fahimta ?
30/08/2022

Hotuna masu ɗauke da saƙo mai muhimmanci ga matasa.

Ko wane sako kuka fahimta ?

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers” Tana Jajantawa Ƴan Kasuwar Kantin Kwari Dake Jihar Kano, Bisa Iftila'in A...
30/08/2022

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers” Tana Jajantawa Ƴan Kasuwar Kantin Kwari Dake Jihar Kano, Bisa Iftila'in Ambaliyar Ruwan Sama Da Yayi Ɓarna A Kasuwar
..Haka zalka ƙungiyar tana jajantawa ƴan kasuwar waya na “Beirut Road” bisa Iftila'in da ya faru na ruftowar gini wanda hakan yai sanadiyar mutuwar wasu da raunata wasu da dama wanda har yanzu ba'a gama tantance adadinsu ba.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, da shugaban ƙungiyar na jihar Kano Comr Umar Kabir Dakata, suna miƙa saƙon jajantawa ga ƴan kasuwar kantin ƙwari musanman waɗanda Iftila'in ambaliyar ruwan sama ya shafi shagunan su, sak**akon mamakon ruwan sama.

Haka zalika ƙungiyar “Arewa Media Writer” tana ƙara jajantawa ƴan kasuwar waya na “Beirut Road” bisa Iftila'in da ya rutsa na ruftowar gini wanda hakan yai sanadiyar mutuwar wasu da raunata wasu da dama wanda har yanzu ba a gama tantance adadinsu ba.

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana kira kira ga Gwamnati da masu ruwa da tsaki dasu taimakawa mutanen da wannan Iftila'i ya shafa, ta basu gudunmawar da ta dace domin sauƙaƙa musu raɗaɗin abinda ya same su.

“A ƙarshe ƙungiyar “Arewa Media Writers” tana Addu'ar Allah ya kare afkuwar hakan a gaba, ya mayar masu da mafi Alkhairin abinda s**a rasa.

Rubutawa✍️✍️✍️
Comr Umar Kabir Dakata,
Chairman "Arewa Media Writers" Kano State Chapter.

Address

FCT Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa/Fulani TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share