![Tinubu Zai Halarci Zikirin Juma’a A Fadar Aminu Ado Ta NassarawaGidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi za ta gudanar da t...](https://img4.medioq.com/701/534/426795367015344.jpg)
04/07/2024
Tinubu Zai Halarci Zikirin Juma’a A Fadar Aminu Ado Ta Nassarawa
Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi za ta gudanar da taronta na Zikirin Juma’a na shekara a fadar Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero da ke Nasarawa. An shirya gudanar da taron ne a gobe Juma’a, 5 ga Yuli, 2024, da karfe 4:00 na yamma.
Taron dai zai kasance ƙarƙashin jagorancin Babban Jagoran Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda zai kasance babban baƙo na musamman. Manyan baƙin da zasu halarci taron sun haɗa da; Alhaji Aminu Ado Bayero, da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Taron Zikirin zai mayar da hankali ne kan karatuttuka da addu’o’i da nufin magance matsalolin tsaron da Nijeriya ke fuskanta.
Leadership ✍️