KU DAN SAURARA KADAN ZAKU AMFANA!
DAN GANE DA MARTABAR MANZON ALLAH ZAKU AMFANA.
A muslumci Babu wani ceremony nashiga sabuwar Shekara, babu happy New year!
BIYAYYA GA IYAYE
Hakika magabatan wannan al'ummah sun kasance masu mutukar biyayya, girmamawa da kyautatawa ga mahaifansu, shi yasa rayuwarsu tayi kyau tayi albarka, suka zamto ababen koyi akowanne zamani.
An karbo daga Sayyiduna Ubadatu bn Assaamit (radhiyallahu anhu) yace Manzon Allah ﷺ yace "KADA KA SA'BA WA MAHAIFANKA. KODA ZASU UMURCEKA KA FITA DAGA DUKKAN ABINDA KA MALLAKA ADUNIYA, TO FITAR KA BAYAR".
Wato wannan yana nufin cewa mahaifanka suna da cikakken iko kenan akanka da kuma dukkan abinda ka mallaka. Kuma wannan gargadi ne ga 'ya'yan dake yiwa iyayensu gori akan 'dan wani Qanqanin abu da sukayi hidima dashi agaresu.
Don me zakayi musu gori alhali su suka zamto dalilin zuwanka duniya, suka dauki dawainiyarka tun kafin haihuwarka har lokacin tasowarka, suka ciyar dakai, shayar dakai, ilmantar dakai, da sauran dawainiyar rayuwarka?
Da ache zaka mallaki dukkan dukiyar dake duniyar nan sannan ka kyautar da ita ga mahaifanka, wallahi duk da haka baka biyasu hakkin haifarka da sukayi ba. Kaji tsoron Allah kaci gaba da kyautata wa iyayenka tare da basu hakuri bisa tawaitawarka. Kada ka damu da cewa wai basu yi maka godiya ba. Kai zaka gode musu tunda har suka yarda suka amshi hidimar da kake musu.
Jabir bn Abdillahil Ansariy (radhiyallahu anhuma) yace Manzon Allah ﷺ yace "KUYI BIYAYYA GA IYAYENKU SAI 'YA'YANKU SUYI MUKU BIYAYYA".
Imam Zaidu 'dan Aliyu Zainul Abideen 'dan Imamul Husain (aminci da yardar Allah ta tabbata garesu) daya daga cikin Manyan Maluman magabata, kuma jikan Manzon Allah ﷺ watarana ya gaya wa 'dansa mai suna Yahya bn Zaid "Ya kai Yahya, hakika Allah Ta'ala bai yardar dakai gareni ba, don haka yayi maka wasiyyar cewa ka kyautata mun. Amma ni kuwa Allah ya yardar dani gareka shi yasa bai yi mun wasiyyah game dakai ba".
Ma'anar maganar tasa itace : Acikin Alqur'ani Allah ya wajabta wa 'ya'ya yin biyayya ga mahaifansu, amma bai wajabta wa iyaye suyi biyayya ko kyautatawa ga 'ya'yansu ba, saboda Ubangiji ya riga ya sanya soyayya