28/08/2020
HIKAYATA JARINA kashi na 5
wallafawar Hamza Danwaya
bayan zama na sarkin birnin nakowa da shekara 1, wasu bayin Allah sunzo guri na da wata matsala, mai girman gaske amma na maida ta yar karama saboda son zuciya ta.
Mutane 3 ne s**azo suna rigima akan gado da mahaifin su ya barmasu
, duk dacewa yariga yaraba masu kaso 70 na abun da ya mallaka, kaso 30 ne kawai yarage.
amma s**a kasa samun fahimtar juna kasancewar sudin ba musulmai bane, acikin kayan da yabari akwai gonaki 10, dabbobi jimilla guda 200 sai kuma bayi 10 mata.
to baban nasu ya bar,musu wasiyya akan yadda zasu raba sauran abun nan da ya mutu ya bar,musu kamar haka
Kamar haka acikin wasiyyar yace dokiyoyi na da nabari karamin cikin ku yadauki kaso 50, wanda yake bimawa yadauki kaso 30, babban ku kuma yadauki kaso 20.
to babban nasu a tunanin sa baban nashi yanuna mashi rashin kauna, hakan yasa yakawo karar uban nashi da sauran yan uwamshi agabana
s**a kwashe bayanin duk abunda yafaru daga farko har karshe s**a fada mani, bayan naji sai nace zan tura da wakilai domin suke su tabbatar mani da gaskiyar abunda s**a fada mani kafin ya ke hukunci.
nayi hakan ne domin nasamu nutsuwa don sanin yadda zan warware wannan rikici na tsakanin wadan nan magada su 3, bayan na sallame su da hukuncin su dawo bayan kwana 2
nashiga nazarin yadda zan bullowa wannan lamari nasu ana cikin haka ne washe gari, sai babban nasu yakawo mani ziyara hakan yasa nayi mamaki nabashi dama yashigo,
muka gaisa sannan yafara da cewa nazo ne domin muyi wata magana mai muhimmanci ni da kai ranka shidade, nasaki baki nace to ina jinka, ya gyara zama yace ranka shidade a gaskiya inaso ni na mallaki kaso 50 zuwa 70 na cikin dukiyar da babana yabari, saboda nime babba amma tawace hanya zamu bullowa wannan lamari ? zan iya baka duk abunda kakeso ranka yadade yardar ka kawai nakeso !
nayi shiru na dan wani lokaci sannan nace yanzu kana nufin na tauye hakkin yan uwan ka kenan ?
muhadu a kashi na 6