27/02/2024
MASALLACIN DA AL-WAALIDAYN CHARITABLE FOUNDATION TA GINA A GOMBE!
Cibiyar Al-Waalidayn ita ce aka assasa don samar da lada mai gudana ga mahaifi da mahaifiyar su, Malam Isa Ali Ibrahim Pantami (wato marigayi Alhaji Ali Ibrahim da marigayiya Hajiya Ameenah Umar, Allah Ya musu rahama).
Tun gabanin kaddamar da ita jiya a Pantami Gombe, cibiyar ta gabatar da ayyuka a fadin Nigeria, musamman a cikin jihar Gombe. Daga cikin ayyukan da ta gabatar akwai gina sabon Masallaci a Government Science Secondary Gombe. Muna iya ganin hotunan. An sayyawa Masallacin su na "Masjidul Waalidayn."
Wadannan ayyuka dukkan su ana gabatar da su da rokon Allah, Ya kai ladan ga mahaifan mu sannnan, Ya jikan su da rahama. Muna kara rokon Allah, Ya jikan iyayen duk wanda su ka rasu. Muna kara rokon Allah, Ya kyautata karshemu, Ya jikan zurriyarmu, Ya bamu zaman lafiya da kuma sawwake 'kuncin rayuwa ga towards, kuma Ya bamu ikon da wadatar ci gaba da ayyukan alheri don iyayen mu da mu kan mu.
Signed:
Administration