Jaridar Ji da Gani

  • Home
  • Jaridar Ji da Gani

Jaridar Ji da Gani Wannan Bahaushiyar Jarida tana bada labarun cikin gida da wajen Najeriya.

JERIN WURAREN DA ZA'AYI HORASWAR MASU AIKIN KIDAYA NA WUCIN GANI A TARABA1. ARDO KOLA - Sunkani Primary school,  Koffai ...
27/03/2023

JERIN WURAREN DA ZA'AYI HORASWAR MASU AIKIN KIDAYA NA WUCIN GANI A TARABA

1. ARDO KOLA - Sunkani Primary school, Koffai Primary school, GDSS Iware, Iware Primary school.

2. BALI - Barba GDSS, GSS Bali, GTSS, Bali 1 special primary school, Bali 2 primary school, Central primary school, Garba Chede Primary school, GDSS Garba Chede, Suntai Primary school, GDSS Suntai.

3. D**G - GSSS Donga, Dozonga Primary school, Central primary school Mararaba, East primary school Mararaba.

4. GASHAKA - GDSS Mohammed Sambo Serti, Dadin Kowa Special Nur/pri, Hamman Gabdo Nur/pri, Mohammed Sambo pri/school

5. GASSOL - Luga GDSS Mutum Biyu, Marafa GDSS Mutum Biyu, Special Education Mutum Biyu, Central primary school, Alhassan Primary school, Almajiri School Mutum Biyu, GDSS Mutum Biyu, GDSS Dambazan, Dambazan/M ararraba primary, Tella primary school, Njiddaawo primary school

6. Ibi - GSS Ibi, CRCN primary school, Islamiyan primary school

7. Mohammed Nya primary school, Tukur primary school, Nyamusala primary school, Howie primary school.

8. Karim Lamido - GDSS Karim, primary school Bambur, GDSS Jen central, GDSS central

9. KURMI - GSSS Baissa, Baissa central primary school, GDSS Baissa.

10. LAU - Lau central primary school, GDSS Lau, Dala primary school, Pilot primary school kunini.

11. GEMBU - GSS Gembu, GDSS Mbamga, GDSS Nguroje,

12. TAKUM - GDSS Army Barrack, Salama primary school, Chanchanji special primary school, GDSS Chanchanji, Alheri Primary school, Takum

13. USSA - Central primary school Lissam, GDSS Kutam Yamusa, GDSS Lissam, GDSS Kpambo west, GDSS Kwambai.

14. WUKARI - Central primary school, Marmara Primary /Secondary school, St. Mary Prima2/Secondary school

15. YORRO - Kpantisawa special primary school, GDSS kpantisawa, Ngorey Gada primary school, GDSS Pupule, Pupule special primary school.

16. ZING - GDSS Zing, Lagbima primary school, Yakoko central primary school, Monkin central primary school.

Abin lura; ka halarci wuri mafi kusa.

MUHAWARAR YAN TAKARAR MAJALISAR JALINGO ONE; Sharhi na. Daga: Zaharadden Ibrahim Ba shakka wannan muhawara da kungiyar w...
09/03/2023

MUHAWARAR YAN TAKARAR MAJALISAR JALINGO ONE; Sharhi na.

Daga: Zaharadden Ibrahim

Ba shakka wannan muhawara da kungiyar wake wake ta shirya garkuwa ga demokoradiyya da muke kwaikwaya ta yancin bayyana ra'ayi, kalubalanta da gabatarda tambayoyi da amsa. Wanda hakan ya haska mana yan takarar da suke neman wannan kujera ta Jalingo, game da kudurorinsu da karfin basirarsu game da wannan takara da suke nema. Babban abinda sha'awa ma shine yadda su yan takarar guda biyu da s**a halarci wannan muhawara masu zurfin ilmi ne wanda ilminsu yakai duk matakin da akeso shugaba mai ilmi yakai, kuma kwararru ne akan abinda s**a karanta.

Abubakar Yahuza (APC); Shine dan majalisa maici a yanzu, yayi bayanan wasu ayyuka daya aiwatar a cikin shekaru hudu wanda za'a iya cewa ba yabo ba fallasa, duk da cewa mai aiwatar da abinda ake tsammani zai aiwatar ba, a matsayinshi na dan majalisa da al'umma s**ayi tururuwan zabe, duk daya bayyana musu cewa shi talaka ne bashi da kudin dazai basu su zabeshi, idan ban manta ba shine dan majalisa a Jalingo 1 da akafi zaba da kuri'u masu yawa wanda koda za'a hada kuri'un abokan hamaiyarsa bazai kai nashi ba. Yahuza ya fara siyasa da wuri kuma kwararren lauya ne wanda zamu iya cewa yasan doka daidai gwargwado.

Abdulnaseer Bobboji (PDP); Shine dan majalisa dake neman kuma tsohon shugaban karamar hukumar Jalingo, shima kamar dayan ya bayyana wasu aiyuka daya aiwatar a lokacin da yake shugaban karamar hukumar Jalingo, lalle shine a bayanansa yayi aiyuka koda kuwa bas**ai yadda al'umma suke masa tsammani ba, domin zamu iya cewa kafin ya zama shugaban karamar hukumar Jalingo, shine mutumin da al'umma suke dagawa kafa a jam'iyyasu ta PDP, shima ya samu goyon bayan jama'a daidai gwargwado. Nasiru tshohon ma'aikacin gwamnati ne kwararre, zamu iya cewa ya samu yabo a lokacin da yake aikin gwamnati.

Umar Sarki Adamu (NNPP); Shima dan takarar Jalingo 1 ne, amma sai dai kash ya bata rawarsa da tsalle, bai halarci muhawarar ba b***e muji tarihinsa, mafi yawan mutane suna daukan darasi ne akan wadanda s**a gabacesu, shi baiyi abinda mafi yawan mutane keyi na bibiyar tarihi ba wanda nashi abin koyon bai wuce sati biyu da afkuwa ba, kamar shi, SB yaki halartar muhawara kuma a sharhi dana gabatar na bayyana cewa idan ya fadi zabe to ya tuhumi kanshi, kuma haka akayi dakyar ya tsinci kanshi ana 4 a jerin yan takara.

To shima Sarki banaji bazai fiskanci irin abinda wancan ya fiskanta ba koma fiye da haka.
Bakayi kuskure ba idan kace watakila Sarki bashi da abin fada ne, kwarai nima haka nayi zato, domin zamu tabbatar da haka ne idan muka dubi salon yadda yake yakin neman zabensa, wanda abu biyu kawai zamu iya cewa yake gabatarwa, (1) daga ayi SAk (2) Sai Vidiyo na dan Majalisa maici a yanzu da yake yawo dashi a waya yana nunawa mutane (musamman mata a Islamiyya) inda shi Yahuza yake cewa "Taraba ace sai Bwacha" shi kuma yace Allah ya samu za'a, kaga wannan ai ba irin neman kuri'ar data dace a aiwatar bane, inaga babu bukatar bata lokaci akan wannan zance.

'Daurawa

1. An tambayi Maidala'ilu akan rashin jin shawarin jama'a da yakeyi kuma ba'a samun ganinshi, in da ya musa hakan yace gidanshi a Jalingo yake kuma yana daukan waya, ba daidai bane ace baya daukan shawara, da baya daukan shawara da bai samu tiketi na biyu ba.

2. Da aka tambayi Bobboji akan haraji da yasaka lokacin da yake chairman, ya fayyace yadda abin yake, kuma gaskiya yayi bayani mai gamsarwa akai, wanda dayawa sai a lokacin s**a fahimce shi.

3. Babnan abinda mutane da yan takara ya kamata su lura dashi Shine, wannan muhadara bawai kawai ga wadanda suke cikin dakin taron bane a'a, dubbannin jama'a da suke sauraro kai tsaye a gidan radiyo da gidan talabijin shine tafi muhimmanci, kuma duk mai hankali yasan irin tasirin da haka yake dashi, sabida haka wuri ne aka baka kyauta ka baje ayarka, kaida kake bin mutane lungu da sako wannan muhawarar zatakai inda kai ko wakilanka basuje ba.

4. Dole a yabawa Abdulnaseer Bobboji bisa yadda ya samu zuwa akan lokaci kuma yayi hakurin jira na tsawon minti 40 kafin abokin takararsa yazo. Duk cewa shi Abubakar Yahuza ya bada hakuri wa wadanda s**a shirya dama shi abokin takararsa.

5. Yan takarar biyu sunyi bajinta wurin kokarin kwantarda tarzomar da magoya bayansu s**aso tayarwa.

6. Ya ragewa mutane suyi alkalanci.

DAN TAKARAR MAJALISAR JAHA A JAM'IYYAR NNPP, YANI WATSI DA DAN TAKARAR JAM'IYYAR SU YA NUNA GOYON BAYA GA DAN TAKARA JAM...
23/01/2023

DAN TAKARAR MAJALISAR JAHA A JAM'IYYAR NNPP, YANI WATSI DA DAN TAKARAR JAM'IYYAR SU YA NUNA GOYON BAYA GA DAN TAKARA JAM'YYAR APC A JAHAR TARABA.

A jiya ne dan takarar dan majalisar jaha a jam'iyyar NNPP wato Hon. Stephen Othaniel yakai ziyarar goyon baya ga dan takarar Sanata Alh. Sani Danladi na jam'iyyar APC a jahar Taraba a gidansa dake birnin Jalingo.

Hon. Stephen ya shugabanci wata tawaga dayace daga mazabar su ta Karim I dake karamar hukumar Karim Lamido, ya siffanta Alh. Sani Danladi a matsayin wanda babu kamar shi, daga bisani yakara da cewa bazasu sake su sake zabar wasu da basu iya shugabanci ba. Sa'annan s**a tabbatar da goyon bayansu dari bisa dari.

A daya bangaren idan mai karatu bai manta ba, jam'iyyar NNPP tana da dan takara Sanata wato Hon. Aminu Abdu Liman wanda rahotanni da dama s**a tabbatar da cewa Jam'iyyar ta karbi kudinshi kimanin naira million sha biyar domin bashi takara harma shugabancin jam'iyyar ta kasa da kanta ta bashi tutun jam'iyyar a wani taro da tayi a garin Bauchi, amma duk da hakan baisa wasu yan jam'iyyar ciki harda yan takara suna nuna goyon bayansu ga wani dan takara ba, duk da cewa hakan ya sabawa dokar jam'iyyar siyasa a kowani mataki.

1. Wasu tambayoyi da suke yawo a kwakwalar mutane sune, shin jam'iyyar a matakin Jaha basu amince da tutar da shugabancin jam'iyyar ta bawa AA Liman din a garin Bauchi bane, idan ta amince to mai yasa bata ladabtar da wannan dan takara nasu da yayi babban sabo ba, tunda laifin babba ne da baya bukatar jinkiri a jam'iyance.

2. Wata alaka jam'iyyar take dashi dashi wannan dan takara na APC Sani Danladi wanda a baya akwai zarge-zarge dayawa na cewa kacokan jam'iyyar a aljihunsa yake bayan kuma shi badan jam'iyyar bane, tunda ana zargin cewa shi ya hana jam'iyyar bada tiketin Sanatan was wasu yan takarkaru masu karfi.

3. Wani mataki jam'iyyar zata dauka akan yayanta da suke mata zagon kasa.

4. Yaya dan takarar yakeji idan yaga yan jam'iyyar sa suna marawa wani baya bashi ba.

Wadanda tambayoyi da makamantan su, wakilan Jaridar Jida Gani zasuyi kokarin tuntubar Shugabancin jam'iyyar dashi kanshi dan takarar Sanatan da aka bawa tiketi wato AA Liman.

Kuci gaba da bibiyar mu domin kawo muku rahotanni daban daban.

19/01/2023

*MAFARAUTAR SUN KOMA*

Daga: Muawuya Dalhatu

Wassu Mafarauta Biyar Sun Yi Tafiyar Shekaru Uku Zuwa Garin Mu Don Su Taimaka Mana a Wasan Bana.

Amma Jagorar Su da Mutum Uku Sun Koma Bayan Sun Fahinci Wassu Daga Cikin Manyan Maluman Mu, Sarakunan Mu Da Manyan 'Yan Siyasar Mu Kai Harma Da Wassu Magobayan Su, Sun Shagalta da La'antar Juna, Tsine Ma Juna, S**ar Juna Da Kuma Yi Wa Juna Habaici ko Izgili Musamman a Shafukan Sada Zumunta Da Lasifika.

Jagorar Mafarautar Yace Kun Gwada Hakan a Wasannin 2007, 2011, 2015 da Kuma 2019 Amma Ba Ku Samu Sakamako Mafi Kyawu ba . Shin Ku Na Tsammanin Maimaita Tsohon Tsari Zai Ba Ku Sabon Sakamako Mafi Kyawu Ne A Wasan Bana? Kun Fi Kowa Raw Materiyal da 'Yan Wasa Amma Baku Da Tsarin Sarrafa Su.

Ya Kara Da Cewa ƙarin Matsalar Ku A Bana Kuma Shine Kusan Kowa A cikin ƴan Siyasar Ku Yana Da Farashi, Kananan Kuma Sun ce Ba Wanda Za Su Yi Wa Aiki Kyauta Bana (Zabe Ne Kawai Kyauta).
Yuyuyun Ku Kuma Sai Kun Lallaɓa Su Za Su Karbi Katin Zaben Su, Ku Lallaɓa Su Don Su Fita Zaben, Sa'anan Kuma Sai Kun Yi da Gaske Su Hada Kuri'un Su Waje Guda.

Haka Kuma Manyan Ku Sun Fi Maida Hankali Akan Abinda Ku Ke Da Shi Fiye Da Abinda Baku Da Shi Wanda Kuma Shi Ku Ke Ikirarin Nema Kullum.

Jagorar Mafarautar Ya Ce Taimako Baya Tasiri a Inda Ba Sirri, Tsari Da Kuma Kare Mutuncin Juna.

Muka ce da Jagorar Yayi Hakuri Tunda Ya Riga Ya Shigo Ga Kuma Wasa Saura Kiris. Sai Yace Dole Zai Koma Tunda Mun Mishi Alkawarin Zamu Sauya Tsari Amma Kuma Ya Samu Akasin Haka.

Jagora Yace Ya kamata Ku Gane Cewa Mutane Basa Karɓan Gaskiya Daga Wanda Ya Fusata Su Amma Su Na Iya Karɓan Kudi Daga Wanda Ya Cutar Da Su Kuma Su Biya Mishi Buƙata.

Ita Siyasa Ai Kamar Wasan Kwallo Take Ko Noma. Ko Baka Da Kyakkyawan Niyya Zaka Iya Yin Nasara Matuƙar Akwai Kayan Aiki da Tsari.

Ita Siyasa Ba Magana Ba Ce Ta Halal Da Haram Kawai Ba. Tunda Ko a Sallah Ba Dukkanin Abinda Ya Halatta Muke Aikatawa Ba Bare Kuma a Siyasa Irin Ta Amurka Wanda Ba Ruwanta da Shekaru, Aqida Ko Ladabi.

Har Ila Yau Jagorar Baiyi Shiru Ba Yaci Gaba Da Cewa Kuma Ta Yaya Matasa Za Su Fahince Ku Tunda Ba Kuma Bari Aka Kammala Shari'un Da S**a Shafi Zabukan Fidda Gwani A Kotunan Koli Ba, Ba Ku Bar Matasa S**a Saurari ƴan Siya Ba, Baku Bar ƴan Siyasa S**a Gama Yakin Neman Zabe Ba (Kai Wassu Ma Basu Fara Ba Fa), Su ka Nuna Bajintan Su, Su Ka Fitar Da Manufofin Su. Su Ka Kuma Bawa Mutane Abinda Allah Ya H**e Mu su ba.

Mutum Dayan Kuma Yace Bazai Koma Ba Zai Zauna Ya Nemi Kuɗin Shi Kawai Kamar Yadda Sauran Baki Da ƴaƴan Su Su ke Nema a Garin Mu.

Mafarautar Dai Sun Koma Amma Sun Mana Alkawarin Za Su Ke Mana Fatan Alheri A Comment Daga Garin Su.

Muawuya Dalhatu
Malami a Jami'ar Tarayya ta Wukari dake, Jahar Taraba.

Hoto mai magana: Hotunan wurin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Lebour Party, Peter Obi kenan daga fil...
07/12/2022

Hoto mai magana: Hotunan wurin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Lebour Party, Peter Obi kenan daga filin wasa na Jolly Nyame anan garin Jalingo.

Salamu Alaikum, muna iya daukacin al'ummar dake bibiyar wannan shafin fatan alkairi, sannan muna masu baku hakuri kasanc...
20/10/2022

Salamu Alaikum, muna iya daukacin al'ummar dake bibiyar wannan shafin fatan alkairi, sannan muna masu baku hakuri kasancewa an Kwan biyu baku jimu ba hakan ya faru ne sabida wasu yan gyararraki da mukeyi da wannan muke muku albishir cewa da yardan Allah zamu dawo bada jimawa ba, kuma muna tafi da ingantattun labarai da wasu shirye shirye masu kayatarwa.

Mungode.

Gwamnan jahar Taraba ya nada Shugabanin kananan hukumomin Jahar na rikon kwarye. A yau ne gwamnan hajar Darious Dikson I...
24/08/2022

Gwamnan jahar Taraba ya nada Shugabanin kananan hukumomin Jahar na rikon kwarye.

A yau ne gwamnan hajar Darious Dikson Ishaku ya rattaba hannu akan Shugabanin rikon na kananan hukumomin guda 16 Wanda s**a haka da;

Hon. Ammazalla John, Kurmi LGA
Hon. Jugulde, Sardauna LGA
Hon. Aminu Danbaba, Bali LGA
Hon. Ismaila, Ardo Kola LGA
Hon. Aminu Hassan, Jalingo LGA
Hon. Bala S Bako, IBBI LGA
Hon. Stephen, Wukari LGA
Hon. Niamel Tudun, Yorro LGA
Hon. Musa Abashi, Ussa LGA
Hon. Paul Dogoh, Gashaka LGA
Hon. Daniel Zading, Lau LGA
Hon. Dan Asali Biru, Gassol LGA
Hon. Barr. Shehu Vocks, Karim/L LGA da
Hon. Nicodemus, Donga LGA

A kwannanan ne gwamnan ya rushe Shugabanin kananan hukumomin sakamakon karewar wa'adinsu.

Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!Rubutawa...
21/08/2022

Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!

Rubutawar Dakta Auwal Mustapha Imam

Wani Malamin Jami'a Dakta Auwal Mustapha Imam yayi rantsuwar cewa matukar gwamnati bata biyasu albashin su na wata shida ba to zaibar aikin jami'a. Kamar yadda ya bayyana a shafin shi na Facebook kamar haka; 👇

PhD ne da ni, duk Arewa ni kaɗai na ƙware a arean da na ƙware. Ina koyarwa a jami'o'i guda biyu na gwamnatin tarayya. Wasu jami'a'o'in na buƙatar aiki na.

Muna da damar aiki mai kyau a ƙasashe da yawa da ake mutunta ilimi, amma muka zaɓi mu dawo gida saboda babu isassun Malamai. Ana biyanmu abinda ba ya iya ɗaukar nauyin hidindimunmu.

Gwamnati ta yi alƙawura na inganta rayuwarmu, amma an gaza. Mun shiga yajin aiki domin nema wa kawunanmu mafita, amma gwamnati na barazanar ƙin biyanmu albashinmu da aka riƙe na wata shida.

Ga wannan mawaƙin waƙa kawai ya iya, ba ya amfanar da Nijeriya to kowace hanya, amma a jirgin ƙasar mu ake ɗaukar sa. Mu kuma da muke bauta wa ƙasar mu, mun zama abin wulakantawa.

Na rantse da Allah! Idan gwamnati ba ta biyamu albashinmu na wata shida ba, na bar aikin jami'a kenan har abada!

AN SAKE JOLLY NYAME An saki tshohon Gwamnan jahar Taraba Rev. Jolly Nyame daga gidan kurkuku, bayan shafe shekaru da dam...
08/08/2022

AN SAKE JOLLY NYAME

An saki tshohon Gwamnan jahar Taraba Rev. Jolly Nyame daga gidan kurkuku, bayan shafe shekaru da dama a gidan kurkuku. A shekarar 2018 ne mai shara'a Adebukola Banjoko ta fara daure Jolly Nyame bisa samunsa da kayi da sace wasu kudade a lokacin da yake gwamna a Jahar Taraba, daga bisani kuma a shekarar 2020, kotun kololuwa ta tarayya ta tabbatar da shara'ar karamar kutun sannan ta tabbatar masa da daurin shakaru 12 a gidan gyaran hali.

A ranar 14 ga watan 4 na wannan shekara ne gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari ta yafewa Jolly Nyame da wasu mutane da kotu ta daure bisa, amma ba'a sako suba a wancan lokacin sabida ba'a gama cike wasu ka'idodi ba.

MATSALAR GARKUWA DA MUTANE (Kidnapping) A JALINGO DA KEWAYE; SHIN AKWAI MAFITA? Ra'ayin wani Ma'aikacin Jaridar Ji Da Ga...
04/08/2022

MATSALAR GARKUWA DA MUTANE (Kidnapping) A JALINGO DA KEWAYE; SHIN AKWAI MAFITA?

Ra'ayin wani Ma'aikacin Jaridar Ji Da Gani

Matsalar kidnapping dinnan kusan kullum sai anyi shi a Jalingo sai dai kawai idan abin bai shafi na kusa dakai bane, abin har yazama new normal. Ita kuma gwamnati bata damu da tayi wani abu akai ba, su kuma community sun zubawa gwamnati ido duk da cewa ana kokari amma ai kokarin bai isa ba, a duk lokacin da kuke da matsala irin wannan tsayawa zakuyi ku nemi mafita, kamar dai yadda Bahaushe yake cewa ne "Sai da dan gari ake cin gari" dole idan kunaso ku samu mafita kubawa jami'an tsoro hadin kai, duk wadda ake zargi a mikashi hannun jami'an tsoro ba tare da an duba ko dan wanene ba, mutum ko shine jauron gari mai unguwa ko wanne shi idan an zargin shi dole a gayawa jami'an tsoro domi susa ido akanshi.

Ba karamar illa wannan kidnapping din ke jawowa ba, a duk lokacin da akayi kidnapping din mutum aka sako shi yadawo gun iyalanshi a lokacin da iyalan ke murna ni kuma abubuwa biyu ne ke zuwa mini a rai;

Na farko dole zai samu matsala ta gefen lafiyar shi, domin dawuya ya dawo daidai yadda yake ada, koda ma zai dawo tofa, sannan da wuya ba'a samu matsalar lafiyar kwakwalwa ba, tunda da wuya mutum yadawo ba tare da yarika muggan mafarki ba, da kuma razana bacci kuwa dole sai an dauki lokaci kafin ya dawo daidai.

Na biyu shine gefen tattalin arziki, duk mutumin da akayi kidnapping dinshi dinnan kafin a sake shi dole sai anbiya wasu makudan kudade, kuma duk yadda arzikin mutum yake idan aka biya kudin fansa dole zai dauki lokaci kafin tattalin arzikin shi yadawo, wani ma baida shi family ne suke hadawa, kenan abin kowa yake shafa ta yadda idan aka biya kowa sai yaji a jika, wasu dole sai an saida kadara, nasan wadda aka saida gadon shi kafin aka biya masa wannan duki. To duk baza mu fahimci illan data mana ba sai lokacin abin ya wuce tukun.

Shin akwai mafita?

Babu wata matsala data taba samun wata al'umma kuma aka samu mafita ba tare da, sun tsaya da addu'a sannan s**abi da aiki ba, dole sai an cire tsoro kuma an mika duk wani bara gurbi ga jami'an tsoro.

Gwamnan jahar Taraba ya cika shekaru 68 a yau.A yau Gwamnan Taraba Arc. Darius Ishaku ya cika shekaru 68 a duniya.Gwamna...
30/07/2022

Gwamnan jahar Taraba ya cika shekaru 68 a yau.

A yau Gwamnan Taraba Arc. Darius Ishaku ya cika shekaru 68 a duniya.

Gwamnan wadda ke takarar Sanata a Taraba ta kudu ya cika shekaru 68 da haihuwa inda dan takarar Shugaban kasa, Gwamnoni da manya manyan Nijeria s**a rubuta mishi sakon murnan bazde dinshi a kafofin sada zumunta daban daban.

YANDA MINISTAN SUFURI ENGR. MUAZU JAJI YA BADA MUKAMI DAYA GA MUTUM BIYU A LOKUTA MUBANBANTA.  A farkon wannan wata ne k...
28/07/2022

YANDA MINISTAN SUFURI ENGR. MUAZU JAJI YA BADA MUKAMI DAYA GA MUTUM BIYU A LOKUTA MUBANBANTA.

A farkon wannan wata ne kafar sada zumunta na Facebook ya cika da taya murna wa Abdulazeez Mafindi yadda mutane s**a tayashi murnan cewa Ministan Sufuri Engr. Muazu Jaji ya nadashi a Matsayin shugaban ma'aikatanshi, duk da irin wannan dunbin mutane da s**a taya wannan murna baisa shi Ministan ya karyata bada aikin wa Abdulazeez Mafindi din ba koda kuwa ta fejin shi na sada zumunta ne, kenan wannan yana nuna cewa nadin gaskiya ne ba jita jita bane.

Kwasan sai aka sakejin shi Ministan ya sake nada Dr. Abubakar Dantsoho har ilayau a Matsayin shugaban ma'aikata kamar dai yadda ya nada Abdulazeez Mafindi dn, batere ya an banawa al'umma soke shi wannan nadin na farko ba.

Duk da cewa takardan daukan aikin (Appointments) duka biyu baiyi yawo kamar yadda rubuce rubucen jama'a ya bayyana ba, sai dai ai shirun budurwa na'am ne.

Zuwa yanzu mutane sun gagara fahimtar wanne daga cikin wadanda aka bawa mukamin na boge, ko Kuma dai Ministan ya janza hukunci ne daga baya. Kodai rashin chantantar shi na farkon ne ta bayyana bayan an bashi mukami.

Munyi kokarin tuntubar Ministan domin jin yadda abin yake amma ya cutura.

Sen. Bwacha ya nada Malamin da Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar a Matsayin Darektan Kamfe. Malam Abdulrahma...
25/07/2022

Sen. Bwacha ya nada Malamin da Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar a Matsayin Darektan Kamfe.

Malam Abdulrahman Dahiru Jen shine Malami kuma shugaban Komitin marayu da Kungiyar Izala reshen Jahar Taraba ta dakatar daga shiga harkokinta dare da jagorancin Sallah a masallacin ta dake Unguwar Barade Jalingo a ranar 14 ga watan shida bisa ga zargin shi akan hada kai da kuma marawa Sanata Emmanuel Bwacha baya a Siyasar Taraba.

Abin tambaya anan shine, shin daukan Malamin a Matsayin Darektan Kanfe zai taimakawa Sanata Emmanuel Bwacha gurin samun kuria'ar Musulman jahar ko a'a.

A Jahar Taraba dai siyasar addini ne kai tsaye yayi kamari, kusan za'a iya cewa anja layi a tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci sai dai yan kadan daga cikin mabiya addinan guda biyu.

Ku cigaba da bibiyar mu domin kawo muku ingantattun labarai da rahotanni.

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta bayyana ranar 31 ga watan Juli a matsayin ranar da zata rufeyin rijistar zabe....
25/07/2022

Hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta bayyana ranar 31 ga watan Juli a matsayin ranar da zata rufeyin rijistar zabe.

Hukumar ta bayyana cewa, daga yanzu za'a cigaba da gudanar da yankan katun zaben ne daga karfe 9 na safe zuwa karfe 5 na yamma, haka zalika ta bayyana cewa ranar Asabar da Lahadi suna cikin ranakun da za'a rika gudanar da rijistar.

Hukumar tayi kira ga wadanda basu riga sunyi katin ba da suyi gaggawar zuwa yankan katin kafin lokaci ya kure, domin babu tabbacin sake kara wa'adin ranakun rijistar.

Kamar yadda aka sani ne, ana gudanar da rijistar katin zaben ne a ofishin INEC din na kawace karamar hukuma.

Ɗaya daga Cikin waɗanda aka sace a jirgin ƙasan Kaduna - Zuwa Abuja ya Kuɓuta.Elkalil Muhammad yace;Alhamdulillah!Bayan ...
25/07/2022

Ɗaya daga Cikin waɗanda aka sace a jirgin ƙasan Kaduna - Zuwa Abuja ya Kuɓuta.

Elkalil Muhammad yace;

Alhamdulillah!

Bayan watanni 4 Allah ya kuɓutar da Barrister Hassan Othman daga hannun Kidnappers. Kamar yadda kuka gani a cikin faifan Video da s**a fitar jiya, Barrister Hassan yana daga cikin waɗanda aka ba dama yayi Jawabi.

Kawo yanzu bamu san yadda akayi Barrister Hassan ya kuɓuta ba. Muna roƙon Allah ya kuɓutar da sauran Ameen.

Jerin sunayen yan takarar gwamna da hukumar zabe ta jahar Taraba ta kafe. Sunayen sun hada da;1. Sen Emmanual Bwacha  (A...
23/07/2022

Jerin sunayen yan takarar gwamna da hukumar zabe ta jahar Taraba ta kafe.

Sunayen sun hada da;

1. Sen Emmanual Bwacha (APC)
2. Yahaya Mohammed Sani(NNPP)
3. Kefas Agbu (PDP)
4. Philip Munlip (LP)
5. Dr David Charima (AAC)
6. Ibrahim Sani (NRM)
7. Haniel Henry Banti (APP)
8. Manu Fedemure Sunday (APGA)
9. Adda Gideon Wunuji (APM)
10. Wasa Josiah Wukari (PRP)
11. Bala Kabiru (Boot Party)
12. Adamu Bello (Zenith Labour Party)
13. Hamman Mohammed Mbali (Accord party)
14. Aminu Ibrahim (ADC)
15. Saadu Abubakar (YPP)
16. Mustapha Hamman Abubakar (ADP)
17. Gambo Abubakar Sadiq (AA)
18. Baido Danladi Tijo (SDP)

Zan iyacin zabe a Taraba koda dan uwana Kirista na dauka a matsayin mataimaki ba Musulmi ba.  Sen. Emmanuel Bwacha dan t...
22/07/2022

Zan iyacin zabe a Taraba koda dan uwana Kirista na dauka a matsayin mataimaki ba Musulmi ba.

Sen. Emmanuel Bwacha dan takarar gwamna a Jam'iyyar APC a Taraba ya bayyana cewa zai iya daukan wanda ba musulmi ba a matsayin mataimaki kuma yaci zabe.

Sen. Bwacha ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da yan jarida, yace shi zai iyacin zabe koda bai dauki musulmi a matsayin mataimaki ba amma amma baiyi haka ba.

Da yake maida martani akan ko yadace Sen. Bola Tinibu ya dauki Sen. Kashim shatima a matsayin mataimaki duk cewa a akwai Kiristoti da s**a chanchanta?

"Bansan dalilin shi na yin haka ba Watakila idan ya dauki Kirista bazai ci zabe bane, amma ni nasan ko ban dauki Musulmi ba zan iyacin zabe amma banyi haka ba" cewar Senata Bwacha.

Wannan furuci da Bwacha yayi ya jowo cece kuce musamman a kafar sada zumunta yayinda wasu ke cewa kwatakwata bai kamata yayi wannan furucin ba a matsayin shi na Wanda yake neman bayan musulmai, in da wasu kuma ke cewa dama tun fil'azal shi Bwacha ya zani Musulmai wannan furucin ma na boye ne ya fito fili.

Shin wadannan kalamai zai taimakawa shi Emmanuel Bwacha ko kuma zai kara mishi bakin jini?

Ku cigaba da bibiyar Jaridar Ji da Gani domin cigaba da kawo muku sharhin yau da kullum.

Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP a Jahar Taraba ya ziyarci mahaifarsa.Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP Col. Agbu Kef...
16/07/2022

Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP a Jahar Taraba ya ziyarci mahaifarsa.

Ɗan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP Col. Agbu Kefas yakai ziyara mahaifarsa dake karamar hukumar Wukari a yau.

Abu Kefas yakai ziyarar ne tare da ɗunbin magoya bayansa, a yayinda ya samu tarba daga shugabanin Jam'iyyar na ƙaramar tasa.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Ji da Gani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Ji da Gani:

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share