27/03/2024
Facebook ko rudani.....
1. Babu Web3 infrastructures akan Facebook.
2. Babu tsaro akai, kowa zai iya bude Account da sunan ka exactly, za su iya maka verified ko ba Hoton ka ne akan Profile ba.
3. Shekaru kusan 20 mutane dubu 5,000 ne rak zaka iya karba a cikin Facebook Friends list dinka, sauran sai dai suyi following dinka, ko ka mayar da Account din Page.
4. Discrimination, nuna wariyar addini, bangaranci, goge maka rubutu babu gaira babu dalili. Kamar bayyana kiyayya ga Palasdinawa da goyon bayan Israela a Fili duk girman ta'addancin ta.
5. Ayi banning dinka daga Posting na tsawon watanni, a haka na yin Live Stream for nothing.
6. Babu revenue sharing me kyau ga users, sai yanzu da s**a ga Pavel Drove ya gama gina Telegram sannan suke son su gyara Revenue Model dinsu.
7. Ba kowane Facebook Application ne yake iya yin permanent deletion na private chats tsakanin ka da mutum ba.
~ Ga yawan Ads, kana cikin kallon Story sai su shigo maka da wani shirmen da kai baka da alaka dashi, duk don a samu Kudi.
8. Neman Kudi ko ta halin kaka, har ka gagara gane menene hikimar yin Advance Facebook App, Facebook Messenger da kuma Facebook Lite. A kimiyayyance ana iya hade wadannan features din waje daya akan App daya tak..
~ Sun kirki Reels, amma daga karshe sai aka fahimci tsabar wahala da bautar da mutane ne kawai kafin a baka 'dan abinda za'a baka.
9. Gwamnatocin kasashe suna zargin Facebook da abubuwa munana daban daban daga cikin kin biyan Haraji, kwarmata sirrin masu amfani da Facebook din, kamar wajen aikin su, cikin sauki ayi locating inda kake, siyar da User Data wa kamfanoni.
~ Hakan na daga cikin dalilan da yasa Gwamnatin kasar China, Rasha, Syria da Iran s**a yi banning Facebook a kasashen su tun da dadewa.
10. Duk da yawan mutanen dake amfani da Facebook kusan mutane Biliyan hudu a duniya Facebook basa iya tafiya da zamani kamar yadda Twitter da Telegram suke tafiya da zamanin.
~ Facebook yafi kowane Social Media yawan samun matsala a duniya duk da sun fi kowa samun Kudin shiga.
11. An dade ana korafi Facebook basa karban suggestions daga Masana a fadin duniya wajen inganta Facebook, an dade ana basu shawarar kawo sabbin features akan Facebook da Whatsapp dinsu s**a ki, hakan yasa wasu s**a samar da GB Whatsapps s**a zuba features masu kyau wanda har yau asalin Whatsapp sun ki kawo irin wannan feature din zuwa kan Whatsapp domin samar da customer's satisfaction da kuma janye hankalin mutane daga unofficial Whatsapp wato GB.
12. Ba'a yin korafi akan su sai sun goge rubutun da aka yi na 'korafi, kamar yadda zaku gani zasu goge wannan rubutun da nayi, ko suyi banning dina.