15/07/2023
(TARIHIN SARKI UMARUN NAKALA GWANGWAZO DA GWAGWARMAYARSA AKAN DAWA KASHI NA BAKWAI 7)
Farautar Sarki Umarun Nakala Gwangwazo A Ƙasar Saudi Arabia 🇸🇦.
To Farautarsa A Ķasar Saudi Arabia 🇸🇦 Sunje Aikin Umrah Ne Dashi Da Amininsa Alhaji Ɗan Muntari, Ba Aikin Hajji Bane Yaje Yayi Farauta Domin Kuwa Allah SWT Ya Haramta Farauta Ga Dukkannin Mutumin Da Yayi Haramar Aikin Hajji.
Da S**aje Aikin Umrah Bayan Sunje Madina Sunyi Ziyarar Shugaba Annabi Muhammad SAW, Da Ahlin Gidansa Da Sahabbansa Masu Daraja,Sai S**a Dawo Masaukinsu A Makkah,Da S**a Dawo Makkah Shida Alhaji Ɗan Muntari Kowannesu Yayi Tsari Na Zuwansa Masallacin Harami,Lokacin Da Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Zaije Masallacin Harami Shi Kuma Alhaji Ɗan Muntari Yana Masaukinsu,Lokacin Da Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Yake Masauki Shi Kuma Alhaji Ɗan Muntari Yana Masallacin Harami,Haka S**a Tsara Ayyukansu.
Lokacin Da Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Ya Tafi Masallacin Harami Yabar Alhaji Ɗan Muntari A Masaukinsu, To A Bisa Al-ada Ga Mutumin Da Yasaba Zuwa Aikin Hajji Ko Umrah Yasan Ana Sauke Masu Zuwa Aikin Hajji Ko Umrah A Hotel Ne Babba Ɗakin Za'a Iya Haɗaku Da Mutanen Da Ba Tafiyarku Ɗaya Dasu Ba,To A Wannan Tafiyar An Haɗa Su Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Da Alhaji Ɗan Muntari Da Wasu Mutane Suma Daga Kano Suke Amma Basusan Juna Ba.
A Al-ada Ta Mutanenmu Hausawa Mazaunan Ƙasar Saudi Arabia 🇸🇦Waɗanda Sun Daɗe Acan Wasu Ma Sun Zama Ƴan Ƙasa,S**anyi Abinchi Iri-Iri S**awowa Ƴan Uwansu Waɗanda S**aje Aikin Hajji Ko Umrah K**ar Tuwo,Ƙosai,Kunu,Koko,Waina Da Sauransu.
To Alhaji Ɗan Muntari Yana Masaukinsu Baije Masallacin Harami Ba,Shi Kuma Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Yana Masallacin Harami,Baya Alhaji Ɗan Muntari Yakwanta Yatashi Saiya Ɗan Kishingiɗa Kaɗan Yana Hutawa,Sai Ga Wani Mutum Mazaunin Ƙasar Saudi Arabia Yashigo Masaukinsu Wajen Ƴan Uwansa Da S**azo Aikin Umrah Ya Kawo Musu Abinchi,Saiya Cewa Ɗan Uwan Nasa Ga Tuwo Na Kawo Maka Ga Lemonan Ga Kuma Nama BAREWA,Abinka Da Mafarauci Alhaji Ɗan Muntari Yanajin Mutumin Ya Ambaci Naman BAREWA Saiya Gyara Zamansa,Sai Wancan Mutumin Da Aka Kawowa Abinchin Yace Shi Bazaici Naman BAREWA Ba,Sai S**a Cewa Alhaji Ɗan Muntari Bismillah Tunda Duk Sun Zama K**ar Ƴan Uwa,Alhaji Ɗan Muntari Yana Karɓar Naman Nan Yakaishi Baki Tabbas Yaji Naman Barewa Ne,Domin Naman Daji Yafi Naman Gari Daɗi,Sai Ya Karɓi Naman BAREWAR Nan Yasakashi A Cikin Freez,Kafin Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Ya Dawo Sai Alhaji Ɗan Muntari Ya Sha'awantu Da Tayayi Aka Sami Naman BAREWA Anan,Sai Ya Tambayi Mutumin Yace Mallam Tayaya Kuka Sami Naman BREWA Anan,Sai Mutumin Yace Masa Ni Asalina Mutumin Kano Ne A Unguwar FAGGE Ina Aikine A Gidan Wani BALARABE SUNANSA IMAD BUKHARI Kuma Ɗan Farauta Ne,Sannan Yana Daga Cikin Iyalen Masarautar (ROYAL FAMILY) NA MASARAUTAR SAUDI ARABIA 🇸🇦 Sai Alhaji Ɗan Muntari Yace Masa Kaga Kuwa Muma Muna Farauta S**ayi Sallama Yatafi,Da Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Ya Dawo Daga Masallacin Harami Sai Alhaji Ɗan Muntari Yace Masa Sarki Ga Naman BAREWA!!!,Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Saiyaji Abin K**ar Almara Sai Ya Karɓi Naman Nan Yasashi Abakinsa Yaji Tabbas Naman Jeji Ne,Domin Naman Jeji Yasha Banban Da Naman Dabbar Da Take A Gari Saboda Daɗinsu Ba Ɗaya Bane Ba,Duk Wanda Yasaba Cin Naman Jeji Bazaici Naman Gari Ba Sai Dole.
Da Mutumin Nan Yakoma Saiyaje Ya Sami Wannan BALARABEN UBAN GIDANSA Yace Masa Ga Wasu Mutane Sunzo Aikin Umrah Daga Nigeria 🇳🇬 Kuma Ƴan Kano Sunce Su Ƴan Farauta Ne, Kasan Duk Inda Mafarauci Yake A Duniya Akwaishi Da Son Ɗan Uwansa Mafarauci,Saboda Haka Ana Faɗa Masa Sai Shi IMAD BUKHARI Ya Kwaɗaitu Da Su Haɗu Da Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Da Alhaji Ɗan Muntari,To Sai Shi IMAD BUKHARI Ya Turo Yaron Nan Nasa Yace Masa Kazo Ka Faɗa Musu Idan Sun Yarda Inason Na Gansu Lokacin Da Basu Da Wani Uzuri Idan S**a Baka Lokaci Kazo Ka Ɗaukesu Ka Kawosu Wajena,Sai Mutumin Yazo Yasamesu S**a Bashi Lokaci Saiya Koma Ya Faɗawa Ubangidansa.
Da Lokacin Yayi Yazo Ya Ɗauki Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Da Alhaji Ɗan Muntari Yakaisu Wajen Maigidansa IMAD BUKHARI Daya Kaisu Sai IMAD BUKHARI Yabasu Wuri S**a Zauna Acikin Ofishinsa Wajene Babba Akwai Kanta (Canter)Babba Acikin Ofishin Nasa,Bundugogine Iri Daban- Daban Acikin Kantar (Canter).
Sai IMAD BUKHARI Yasa Aka Kawo Musu Abinci Iri-Iri Saida S**aci S**a Sha Lemonan Da Aka Kawo Musu Bayan Sun Gama Cin Abinchin Sai S**a K**a Hirar Daji Da IMAD BUKHARI Sai Yace Musu Ance Daga Nigeria🇳🇬 Kuke S**ace Masa Eh,Ance Kuma Kuna Farauta S**ace Masa Eh Muna Farauta,Sai S**a K**a Hira Ta Naman Daji Saiya Faɗa Musu Irin Dabbobin Dajin Da Suke Dasu A Ƙasar Saudi Arabia 🇸🇦, Sai Suma Su Faɗa Masa Irin Dabbobin Da Muke Dasu Anan Nigeria 🇳🇬.
Bayan Sun Gama Hirar Daji Da IMAD BUKHARI Sai Yace Musu Yanzu Yaushe Zakuzo Mu Tafi Daji Farauta Sai Yace Musu Su Zaɓi Ranar Da Kansu Idan Sun Kusa Tafiya S**ace Masa Yayi Babu Damuwa Sai Yasa Direbansa Ya Ɗaukosu Ya Dawo Dasu Masaukinsu,Sai S**a Sake Sa Lokaci Da Lokacin Yayi Sai IMAD BUKHARI Ya Turo Musu Da Direbansa Yazo Ya Ɗaukesu Ya Tafi Dasu Wajen IMAD BUKHARI,Da S**aje Yasa Aka Kawo Musu Abinchi Iri-Iri Da Lemona Iri Daban- Daban,Bayan Sun Gama Cin Abinchin Sai S**a Shiga Wajen Nasa, Domin Ya Jarrabasu Sai Yace Da Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Da Alhaji Dan Muntari Wacce Irin BINDIGA Zaku Iya Harbi Da Ita A Cikin Wadannan BINDIGOGIN? Sai Alhaji Ɗan Muntari Yace Masa Ko Wacce Irin Bindiga Kabamu Anan Zamu Iya Harbi Da Ita,Sai IMAD BUKHARI Yace Musu Kowacce!!! S**ace Eh Kowacce.
To Akwai Wata Bindiga Sunanta POINT 2-2 RAFFLE Saiya Ɗaukota Saiya Sa Wani Ķyalle Ya Goge Ya Goge Ya Goge,Saiya Miƙowa Alhaji Ɗan Muntari Ita, Alhaji Ɗan Muntari Yabi Dukkannin Sharuɗɗa Na BINDIGA Wanda Bin Wannan Sharuɗɗan Shine Zai Nuna Masa Tabbas Yasan Bindiga,Daka Karɓa Idan Aikinka Ne Wanda Yabaka Yasani Sai IMAD BUKHARI Ya Gamsu Da Cewar Lallai SARKI UMARUN NAKALA GWANGWAZO DA ALHAJI ƊAN MUNTARI Cikakkun Maharba Ne Sunsan Sharuɗɗan Bindiga,Saiya Ɗauko Kwanson Harshashi To Ita Kwalin Harshashinta Guda 50 Ne Aciki Saiya Miƙowa Alhaji Ɗan Muntari Ita Saiya Karɓa Sai Ya Miƙawa Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Ita,Sai Shima Yabi Sharuɗɗan Bindiga Ya Leƙa Ya Juyata Saiya Riƙeta Sai Shi IMAD BUKHARI Yace Musu Yanzu Saiku Tashi Mu Shiga Daji.
Sai Aka Ɗauko Mota S**a Tafi Daji Suna Shiga Dajin Daga Nesa Sai S**a Hangi Garken BAREYI Sunyi Cunkus! Sai Shi IMAD BUKHARI Yace Abinda Yakeso A Harbi AGARE (Namiji) Sai Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Ya Miƙawa Alhaji Ɗan Muntari Bindiga Saishi Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Yasa Abin Hangen Nesa A Idansa Suna Matsawa Da Motar Kusa Da Garken BAREYIN,Da Alhaji Ɗan Muntari Yai Haka Ya Ɗora Bakin Bindigar Ta Tagar (Window) Motar Yai BISMILLAH YA KARANTA SURATUL FATIHATUL KITAB, Abin Hangen Nesan Yana Hannun Sarki Umarun Nakala Gwangwazo Da Harbinsa Da Faɗuwar Neman Saboda Ita Bindigar Tana Tafiya More than 300m,Saida IMAD BUKHARI Yayi Tafi Sosai Taf! Taf!! Taf!!! Sai Ragowar Garken BAREYIN S**a Tarwatse,Sai S**a Sake Warewa Wannan Harsashin Da S**a Saka Acikin Bindigar Shine Aka Harbi BAREYI Guda Biyu Dasu.
IMAD BUKHARI Yaji Dadi Sosai Ganin Yadda S**ayi Harbin Ba Tare Da Wani Kuskure Ba Yarasa Ma Mezaice Musu Saboda Murna Da Farin Ciki.
Yauwa Akwai Wata Magana Da IMAD BUKHARI Ya Faɗa Musu Kafin Su Shiga Dajin Cewa,Kada Su Sake Su Baiwa Direbansa BINDIGAR Sa Koda Wani Abu Zai Faru Su Sauka Daga Kan Motar To BINDIGAR Ta Kasance Tana Tare Dasu Kadasu Bayi Ya Riƙeta.
Bayan Sauka Sunje Sun Yanka BAREYIN Nan Guda Biyu Da S**a Harba Sai S**a Koma Ofis Ɗin IMAD BUKHARI Inda Yake Ajiye Waɗannan BINDIGOGIN Nashi S**a Ajiyesu Yasake Goggogesu Ya Mayar Dasu Cikin Kantar(Canter)Ta Gilashi (Glass)Ya Irga Harsashin Nan Yagansu Guda 48 Cif,Abinnan Yabashi Mamaki Kwarai Da Gaske.
Anan Nema Shi IMAD BUKHARI Ya Nuna Musu Cewa Su Maizai Hana Sudawo Su Cigaba Dayin Farauta Dashi A Ƙasar Saudi Arabia 🇸🇦 S**ace Masa A'a Su Ma'aikatan Gwamnati Ne A Nigeria 🇳🇬 Yaiyai Akan Su Dawo Su Cigaba Da Farauta Tare Saboda Abin Ya Birgeshi Sosai Ta Yadda S**ayi Harbin BAREYIN Nan Guda Biyu Kuma Da Harsashi Guda Biyu Ba Tare Da Sunyi Kuskuren Harbi Ba.
Sai IMAD BUKHARI Ya Tambayesu Yaushe Zasu Koma Nigeria 🇳🇬Sai S**a Fada Masa, Bayan Yasa Direbansa Ya Mayar Dasu Masaukinsu Da Gari Ya Waye Sai Yasa Aka Soya Musu Kayan Cikin BAREYIN Nan Aka Ciko Foodplask Dashi Aka Kawo Musu Da Lemonan Sha,Sai Shi IMAD BUKHARI Yakai BAREYIN Nan Kamfani Aka Sakasu Acikin Roba (Transferral)Akai Ceiling Dinsu Akayi Musu Handle Maɗauka K**ar Irin Robar Da Ake Zuba Ruwan ZAM ZAM Haka Akayi Musu Aka Sakasu Acikin Firij (Freezer)Yayi Ƙanƙara.
Da Lokacin Tafiyar Su Gida Yayi Ya Turo Direbansa Yazo Ya Ɗaukeso Yakaisu Wajensa Suyi Sallama IMAD BUKHARI Saida Yabawa Kowannesu Kuɗi Acikin Emvelope Yakai 1000💵Dollars Kowannesu,Sannan Yasa Aka Kai Musu BAREWAR Nan Har Airport Na Jeddah.
Das**a Dawo Gida Nigeria 🇳🇬 Aka Bude Robar Da Aka Saka BAREWAR Nan Aciki,Da Aka Soya Naman BAREWAR Nan Sarki Cewa Yayi Bai Taɓacin Naman Jeji Mai Daɗin Naman BAREWAR Nan Ba.
Nan Zamu Tsaya Sai Wani Satin Idan Allah Yakaimu Zamuci Gaba Daga Inda Muka Tsaya,Bissalam.