Usman Abdulkarim

  • Home
  • Usman Abdulkarim

Usman Abdulkarim ‏وما مِن شدةٍ إلا وفيها
‏من الفرَجِ المُؤمَّلِ ما يفيها

‏فطِب نفسًا إذا اشتدت كروبٌ
‏ فإنَّ عواقبَ الحُسنى تليها

06/12/2024

With UMAR SHEHU ZARIA – I'm on a streak! I've been a top fan for 3 months in a row. 🎉

06/12/2024

With Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria – I'm on a streak! I've been a top fan for 3 months in a row. 🎉

13/09/2024

Matuƙar ka san kana buɗe social media a gaban yaranka, to ya k**ata ka rinka cewa su matsa idan ka bude abun da zai amfane su sai ka nuna musu. Domin social media kam yanzu sai addu'a kana budewa tsiraici da rashin tarbiya ake cin karo da shi.

UMAR SHEHU ZARIA

10/09/2024

Shin idan mutum yaje kabarin Annabi (S.A.W) sai yaje daf da kabarin akeyi masa sallama.?

Tambayoyi

1. Shin idan mutum yaje kabarin Annabi (S.A.W) shin sai yaje daf da kabarin akeyi masa sallama ko kafin a karasa.

2. Gafarta malam, ina kyautatawa mahaifina sosai, amma malam duk abinda na kai masa sai ya dauaka ya siyar, sannan yace a karo masa wani.

3. Malam mukan siyo kaya da Dalar Amerika, sai kuma daga baya farashinta ya daga ko ya sauka, shin ya sheikh zamu daga farashinmu ne ko kuwa.?

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

4.

10/09/2024

Duk wanda ya yi haƙurin rashin ɗari, matuƙar yana nema watarana zai samu dubu.
©Anas Darazo

04/09/2024

ZAN IYA ZAMIYAR BASHINA DAGA ZAKKA ??

Tambaya
Assalamu Alaikum. ya sheikh. Ina da tambaya. Idan ina bin mutum bashin kudi kuma zan yi zakka, zan iya cewa na bar mai abin da nake bin shi a matsayin zakka?

Amsa
Wa alaikum assalam
Malamai sun tattauna a wannan mas'alar zuwa zantuka guda biyu:

1. Ba ya halatta mutum ya mayar da bashin da yake bin wani a matsayin zakka, saboda Zakka hakkin Allah ne, yin hakan kuma zai zama ya amfanar da kansa da zakkar saboda in ba ta hanyar ta ba da kudinsa ba za su fito ba, Wannan ita ce fatawar Malaman Hanafiyya da Hanabila sannan kuma ita ce fatawar malaman Malikiyya in ban da Ash'habu, hakan kuma shi ne mafi inganci a wajan Shafi'iyya.

2. Ya halatta ya mayar da bashinsa da yake kan wani ya zama Zakka, saboda in da zai ba shi zakkar ya dauke ta ya biya shi bashi da ita da ya halatta ya amsa, wannan ita ce fatawar Ash'habu daga Malikiyya, sannan kuma Kauli ne a mazhabar Shafi'iyya k**ar yadda Nawawy ya ambata a Almajmu'u.

Don neman Karin bayani duba: Almausua Alfiqhiyya 23/131.

Duk da cewa babu nassi yankakke bayyananne a mas'alar a iya bincikenmu, Saidai fatawar manyan malamai na rashin yin ZAMIYAR ita ce ta fi rinjaye, saboda kubutar da wuyaye daga yiwuwar kuskure yana da kyau sannan fita daga sabanin Malamai abin so ne.

Allah ne mafi sani
Dr, Jamilu Zarewa
19/04/2018

31/08/2024

Ka kiyayi cutar da yaro domin ba a san me gobe za ta haifar ba.

UMAR SHEHU ZARIA

30/08/2024

YAWAN AMBATON ALLAH..!!.

Yawan ambaton Allah na daga cikin manyan ni'imomin Allah ga bayinSa na musamman. Ambaton Allah shi ne abincin zuciyarka da natsuwarta. Sannan kuma waraka ne daga qunci da damuwarka.

Yawan ambaton Allah na qara kusantar da bawa ga mahaliccinsa har bawa ya zama mai gata a wajen Allah, tare da bashi kariya daga mugayen mutane da shaidanu.

Sabo da darajar ambaton Allah Mala'iku kullun a cikinsa suke. Kuma shi ne numfashin 'yan Aljannah. Kar ka manta ! Malai'ku na rubuta dukkan ayyukanka; yi qoqari su rubuta maka ambaton Allah da yawa a kundin ayyukanka.

Akwai wasu bayin Allah da ambaton su ga Allah fa ya fi maganarsu yawa a wannan rayuwar. Yi qoqari ka samu rabonka.

Subhanallah, wal-hamdulillah, wa la ilaha illalLah, wallahu Akbar, wala haula wala quwwata illa billah.

Dr. Jameel Muhammad Sadis

Jameel Muhammad Sadis

MALAMINA YA FAƊA MIN 7. Ilmi yafi dukiya ta fuskoki masu yawa; daga ciki:-(a) Ana gadon dukiya, amma ba a gadon ilmi.(b)...
29/08/2024

MALAMINA YA FAƊA MIN

7. Ilmi yafi dukiya ta fuskoki masu yawa; daga ciki:-

(a) Ana gadon dukiya, amma ba a gadon ilmi.

(b) Ilmi na baka tsaro, amma dukiya kai kake tsaronta.

(c) Ilmi kayan Annabawane, ita ko dukiya kayan masu mulki da ƴan duniya.

(d) Dukiya na raguwa da bada ita, shi ko ilmi yana ƙaruwa ne sak**akon bada shi.

(e) Mai ilmi kowa ke buƙatarsa har da sarakuna, shi ko mai dukiya; mabuƙata da talakawa ke da buƙatarsa.

✍️ Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria

28/08/2024

HUKUNCIN ASKE GEMU

Tambaya :
Malam menene hukuncin tsayar da gemu shin wajibi ne ko mustahabbi?, sannan aske shi haramun ne ko makaruhi ne ?

Amsa :
To dan'uwa Annabi s.aw yana cewa : (Ku sabawa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki), k**ar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta : 5553 da kuma Muslim a lamba ta : 259.
Wannan yasa da yawa daga cikin malamai s**a tafi akan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman k**ar Ibnu Hazm sun hakaito ijma'in malamai akan haka, k**ar yadda ya zo a littafinsa na maratibul ijma'i shafi na : 157.
Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai k**ar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da alhaji yakan yi bayan ya gama aikin hajjinsa.

Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke karawa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana k**a da tsohuwar da kyanta ya disashe, k**ar yadda Sa'adi ya fadi a Bahjatu kulubul abrar shafi na : 50 .

Saidai malamai suna cewa idan mutum yana garin da za'a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, saidai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta .
Don neman karin bayani duba littafin : Wujubu I'ifa'ul liha .
Allah ne mafi sani .

Jamilu Zarewa
17\10\2014

28/08/2024

LARABGANA A WATAN SAFAR !

Tambaya:
Assalamu alaikum mallam tambaya na shine, na ji wasu mutane suna yin wani sallah yau, raka'a hudu wai sunan sallar LARABGANA, Ena so dan Allah mallam yamin bayanin sallar ?

Amsa :
Wa alaikum assalam, To dan'unwa yana dağa cikin bidi'o'in zamanın maguzanci kudirta cewa Larabar karşhen watan Safar tana kunshe da bala'oi, addinin musulunci ya karya wannan camfin bayan zuwan Annabi S.A.W. don haka watan safar daya ne dağa çıkın watanni (12) wadanda Allah ya tabbatar a suratu Attauba, bai kebanta da wani bala'i na musamman ba.

Babu wata aya ko hadisi da ya kebance Larabar karshen watan Safar da wata ibada ta musamman, don haka yın nafilfili saboda neman kariya dağa musifun LARABGANA, na daga çıkın bidi'o'i da ba su da asali a Musulunci.

Don neman karın bayani duba Fatawaa Alajnah Adda'imah 2/354. Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa
9/12/2015.

28/08/2024

Wasu mutanen duk ranar da ka ga sun kira wayarka, ka kashe kunne kawai ka ji menene ya faru har su ka kira😃
Wasun kuma duk ranar da ka ga ba su kira ka ba, bincika ka ji meya faru har ba su kira ba😍
Haka rayuwa take, ba ka zama mutum mai muhimmanci a wurin dukkan mutane, wadanda ka zama mai muhimmanci a wurin su ka tabbatar kai ma sun yi muhimmanci a wurinka, kada kuma ka taɓa bari ka rasa wannan matsayin.
©Anas Darazo

DUNIYA MAKARANTA 141. Idan kana son ganin yadda duniya za ta kasance a bayanka, ka duba yadda take a bayan mutuwar wani ...
27/08/2024

DUNIYA MAKARANTA

141. Idan kana son ganin yadda duniya za ta kasance a bayanka, ka duba yadda take a bayan mutuwar wani irinka.

Za ka ga yadda masoya ke manta masoyansu, rigima ta harɗe tsakanin magadansu.

Wanda bai manta ka kawai
shi ne Allah mahaliccinka. Manta da kowa ka nemi yardarSa.

✍️ Prof. Mansur Sokoto, mni




15/05/2024

لا ينشرُ المرء في دنياهُ منشورا
إلا ويلقاه يوم النشر منشــــورا

هناك يلقاهُ منشوراً بصفحتِــــهِ
وفي كتابٍ مبينٍٍ كان مسـطورا

بل كل قولٍ وفعلٍ كان عاملَهُ
فسوف يلقاه مخطوطاً ومزبورا

وسوف يجزيه ربُّ العالمين بهِ
ولن يغادرَ شيئاً فيه مذكــــــــورا

فلتتق اللهَ في ما أنت تنشــــــرُهُ
إن شئتَ ربحاً وإلا كنتَ مخــسورا

ولا يسرُّكَ كُثْرُ المعجبـــيــــنَ به
أو كُثْرُ تعليقِهمْ إن كنتَ مَـــــوْزورا

ولا يسوؤكَ قِلُّ المعجبيـــــــنَ بهِ
أو قِلُّ تعليقِهِمْ إن كنتَ مَأجــــــورا

فقد يسرُّكَ منشــــــــورٌ تصيرُ بهِ
يوم النشورِ لدى الرحمن مثبـــــــورا

وقد يسوؤكَ منشــــــــورٌ تصير بهِ
يوم النشور لدى الرحمنِ مســــرورا

لقائلها

19/04/2024

Da ka cutar da su, gara su cutar da kai.
Da ka ɗau fansa, gara ka ɗau haƙuri.
©Anas Darazo

19/04/2024

Zuciya ita ke saƙa mana irin mutumin da muke so mu zama, zata cusa mana son gobe mu zama wane, muyi nasara k**ar wane, mu taka mataki kaza, amma ba ita ce ke tabbatar da mun zama ɗin ba, ayyukanmu ne ke wannan. Wannan son da zuciya ke saka mana hoto ne kawai baya taɓa motsi, ayyukanmu na yau da kullum su ne zasu kai mu ga abunda zamu zama gobe, idan kana aiki mara kyau amma zuciyar ka tana saƙa maka gobenka mai kyau ce to yaudaran kai ne kawai, aikin yau da kullum shine abunda zaka zama gobe.
©Anas Darazo

19/04/2024

Matuƙar kana so kasuwancinka ya ɗaure ba tare da ya karye ba kuma dukiyarka ta yi albarka, to kar ka kuskura ka rinƙa cakuɗa dukiyarka da dukiyar haram.

✍️ UMAR SHEHU ZARIA
08 Shawwal, 1445
(18/04/2024).

19/02/2024

Duk wanda yake ganin yafi ƙarfin hukuma to bai fi ƙarfin ALLAH ba, zai haɗu da ALLAH !!!

-Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah)

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Usman Abdulkarim posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Usman Abdulkarim:

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share