![TSOKACI AKAN QUR'AN DAY DA AMARE SUKE SHIRYAWA 1. A yayin shagulgulan biki, abubuwa da dama sun halatta musamman ga mata...](https://img4.medioq.com/581/188/601621645811880.jpg)
25/01/2025
TSOKACI AKAN QUR'AN DAY DA AMARE SUKE SHIRYAWA
1. A yayin shagulgulan biki, abubuwa da dama sun halatta musamman ga mata da yara matuƙar dai ba'a ƙetare iyaka wajen aikatasu ba. Babbar matsalar da muke fuskanta itace rashin kiyaye ladubban shari'a tareda koyi da yahudawa a yayin shagulgulan bukukuwan mu.
2. "Qur'an day" yini ne da ake shiryawa a yayin shagulgulan biki, amarya da ƙawayenta suna yin shiga ta kamala. Suna rarraba Alƙur'ani (juz'i- juz'i) a wajen domin a karanta, ko kuma asamu waɗansu da s**a iya karatun Alkur'ani su rera shi da kyakkyawan sauti. Wannan babu laifi.
3. Galibi matan da suke shirya wannan yini basa rasa alaƙa da karatun islamiyya ko na Tahfeez. Kuma babu shakka shi wannan yini yafi taron kaɗe-kaɗe (Dj) da raye-raye, Arabian Night da sauran nau'ukan ƙetare iyaka.
4. Shi a karan kansa "Qur'an day" ɗin al'ada ce mai kyau amma baya daga cikin karantarwar sunnah don haka babu wani lada na musamman da za'a baiwa mutum don ya halarci "QUR'AN DAY" face ladan karatun Alkur'ani idan anyi da ikhlasi. Duk Amaryar da take son dacewa da karantarwar sunnah a yayin shagalin bikinta sai ta shirya walima daidai gwargwadon ikonta.
5. Akwai wasu abubuwa goma (10) marasa kyau da a tareda wannan sabuwar al'ada ta "QUR'AN DAY". Sun haɗarda:
i. Maye gurbin walima da "Qur'an Day" ma'ana ɗaukar "QUR'AN DAY" a matsayin ibada.
ii. Shigar maza wurin wannan taro koda kuwa mahaifin amaryar ne.
iii. Cire shigar kamala yayin da aka tashi za'a tafi gida. Mace tazo da hijabi ta koma gida da gyale.
iv. Mayar da hankali akan ɗaukar hoto amadadin karatun.
v. Ɓarnatar da kuɗi masu yawa don ƙayatar da taron.
vi. K**a Event hall domin yin wannan yini wanda hakan zai buɗe ƙofofin fitina.
vii. Kunna kiɗa da raye-raye a ƙarshen karatun.
viii. Kallafawa kai da ɗaukarsa a matsayin wajibi.
ix. Wasa, ihu, ko surutu a yayin gudanar da karatun.
x. Zargi ko aibata wacce bata yi ba ko bata halarta ba.
6. Allah yayi riƙo da hannayenmu.
✍️
Umar Sa'ad Abdullahi
25/01/25