Kevin

Kevin Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kevin, Media/News Company, .

11/02/2023
10/02/2023

Daga taskar Masana
******
Da yawa muna ganin masu sallah suna canja wajen sallah bayan idar da sallar farilla don yin sallar nafila, kuma mafi yawa su kan yi hakan, ba tare da ililmin hukuncinsa ba.

Shin canja waje tsakanin salloli?

*Bidi'a ne?*
*Ko Sunnah?*
*Ko abin so?*
*Ko kuma wajibi?*

Kuzo muji hukuncin canja waje tsakanin salloli.

An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin (Rahimahullah), shin akwai wani dalili kan canja muhalli don yin sallar nafila bayan farillah?

*AMSA (JAWABI)?*

*1* Yazo cikin hadisin mu'awiyya (RA) yace: *_Annabi (SAW) ya umurce mu da, kada mu hada sallah da sallah har sai mun yi magana, ko mun fita (daga cikin masallaci)._*

📘 Muslim ya ruwaito.

*Malamai ma'abota ilimi sun riki wannan kan zai fi kyau, a rarrabe farilla da nafila ko ta hanyar magana ko canja wajen sallah.*

*2* Daga Azraq ibn Qais yace: Wani mutum yayi sallah tare da manzon Allah (SAW) sai ya mike, don yin shafa'i, sai Sayyidina Umar ya kamo kafadarsa ya hana shi, yace zauna. *Yace masa ahlil kitab su hallaka ne, saboda ba sa rarrabe sallolinsu.*

Sai Annabi (SAW) ya mi ke ya ke cewa: _*Allah ya datar da kai Umar ibn kattab.*_

📗 Abu Dawud ya ruwaito, Albani ya inganta shi.

*Don haka, yin istighfari sau uku (3) ya isar a matsayin magana.*

Kayi kokarin isar da sakon, ga 'yan uwa musulmi.

*Daga karshe:*

Mai yiwuwa wannan hukunci zai fi amfani wajen mata saboda sun fi yin sallah a gida su kadai. Tana sallar farilla sai ta mike, ta kawo nafila, babu magana a tsakaninsu.

Don haka a yi kokari, a isar da wannan sako ga wasu.

Yada ilimi yana daga cikin manyan ayyukan alkhairi.

Plow me🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

08/02/2023

Manzon Allah (s a w) yace duk Wanda yayi Imani da Allah daranan tashin alqiyama to ya Fadi alkhairi ko yayi shiru

08/02/2023

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم من كان يومن بالله واليوم الأخر فاليقل خيرا او ليسمت

19/01/2023

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم
من كان يومن بالله واليوم الاخر فاليقل خيرا او ليصمت

Manzon Allah tsira da aminchin Allah su tabbata agareshi yace duk wanda yayi Imani da Allah da Ranan tashin alqiyama to ya Fadi alkhairi ko yayi shiru

Send a message to learn more

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kevin posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kevin:

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share