Wikki Leaks News

  • Home
  • Wikki Leaks News

Wikki Leaks News Independent Online Newspaper platform

16/02/2022
KADA KU BADA KO SISI GA MASU SHIGO DA KAYAN ABINCI DA TAKI KASAR NAN, SHUGABA BUHARI YAYI IZININ HAKA WA BABBAN BANKIN K...
11/09/2020

KADA KU BADA KO SISI GA MASU SHIGO DA KAYAN ABINCI DA TAKI KASAR NAN, SHUGABA BUHARI YAYI IZININ HAKA WA BABBAN BANKIN KASA CBN.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

A dai dai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke tafiyar da Shirin Inganta Tattalin Arzikin da tsara muradun da ake bukatar Cimma da shirin Samar da Abinci ta kasa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bada izini wa Babban Bankin kasa CBN da "Kada ta bada ko sisin kobo " cikin ajiyar da kasar ke dashi don shigo da kayan abinci da takin Zamani.

A yayin taron Majalisar Samar da abinci ta kasa daya gudanar a fadar Gwamnati dake Abuja, Shugaban kasa Buhari ya kara jaddada Umarni daya fadi ga Babban Bankin kasa tun a farkon fari, yace ya mika wa Bankin a Rubuce cewa "Kada su bada kudi don Shigo da abinci kasar."

Shugaban kasa yace, Ya karfafa bukatar kara bunkasa abinci da ake Noma a gida,

" Daga kamfanoni Uku kadai da muka zo muka samu suna aiki a kasar, Yanzu munada Kamfanonin Sarrafa Takin Zamani 33 dake aiki. Bazamu biya ko sisin kobo ba ga Asusun mu na ketare don shigo da takin Zamani a kasar. Zamu karfafa Kamfanonin mu na cikin gida."

Bugu da kari, Shugaba Buhari ya kuma bada Umarnin ga masu samar da Sinadaran Sarrafa takin zamani dasu ke samar wa kai tsaye ga Gwamnatocin Jihohi saboda kauce wa 'Yan kasuwa masu harkan dake kawo koma baya ga kokarin Nasarar Samar da Takin ga Manoma a farashi mai sauki.

Shugaban kasa ya Shawarci 'yan kasuwa masu zaman kansu dasu kauce wa shigo da kayan Abinci don samun daman Dogaro ga Babban Banki gurin Samun Chanjin kudi, yace "Kuyi amfani da kudin ku gurin gogayya da Manoma", a Maimakon amfani da Asusun kasa na ketare don Shigo da kayan Abinci dazai kawo Nakasu ga kokarin Manoman mu.

" Muna da Matasa masu Jini a jika da dama dake da aniyar yin aiki wanda kuma hanyar Noma shine kawai Madogara. Akwai aiki dake gaban mu sosai na ganin mun tallafawa Manoman mu," Inji Shugaba Buhari.

Taron wanda Shugaban kasa ya jagoranta da halartan Sauran Muhimman Membobin Majalisa, anyi Bayani kan yadda Matsalar Abinci ke yaduwa a kasa.

Musamman, Mahalarta taron sun hada da Mataimakin Shugaban Majalisar kuma Gwamnan Jihar kebbi Atiku Bagudu, Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban kasa Prof. Ibrahim Gambari, da Wakilcin Gwamnoni dai daya daga Shiyar Siyasa Shidda dake kasar nan, Jigawa, Plateau, Taraba, Ebonyi, Lagos, dakuma jihar Kebbi, Sun Samu Halartan taron.

Ministan Kudi da tsara kasafin kasa, Dr Zainab Ahmed, ta zayyano Matakai da Gwamnati ke gabatarwa don Dakile yawan Koma baya da ake samu sakamakon Annobar Cutar Korona ga Shirin Cigaban Tattalin Arzikin Kasa (NESP).

Sauran abubuwa data gabatar, Ministan ta tsakura cewa Gwamnati zata samar da Sabbin filayen Noma dayakai Kidada Dubu Ashiri 20,000, zuwa Dubu Dari 100,000 a kowace Jiha da Mara baya wa Samar da Guraren fara Sarrafa amfanin Gona wanda haka zai Samar da Miliyoyin guraben aiyuka kai tsaye.

Ta kuma Lissafo Samar da aiki na kai tsaye har guda Dubu dari bakwai da Saba'in da hudu 774,000 Alal akallah matasa Dubu Daya 1,000 a kowace karamar Hukuma, da Gina Rukunin Gidaje Dubu Dari Uku 300,000 a ko wace Shekara don samar da guraben aiki ta hanyar Kamfanonin Gine gine, dama kuma hada Mutane Miliyan Ashirin da biyar 25,000000 da wutan Lantarki da kuma Sabon Shirin nan na Samar da Lantarki ta Hasken Rana ga gidaje, Solar Home System (SHS) da aka tsara zai kai lantarki ga Gidaje Miliyan biyar 5,000000.

Dakta Ahmed ta kumayi Jawabi akan Hadakan kasuwanci da Bankin Duniya don Samar da kudaden gudanar da kasuwanci ga Jihohi don kara inganta Aiyukan kiwon lafiya.

Tace, Don Saukaka wahalan karancin walwalan kudi a hanun Mutane, Gwamnati zatazo da wasu tsare tsare Samun bashi mai saukin ga Masu aikin Kani kanci, Tailoli, Kananan masu Sana'a, Kananan 'yan kasuwa da sauran masu Sana'oin da bai kai ya kawo ba.

Ministan ta kuma kara da cewa, Gwamnatin Tarayya zata kuma samar da Tallafi ga Kanana da Matsakaitan 'yan kasuwa don taimaka musu gurin Cigaba da rike ma'aikatan su da habbaka abubuwa da suke Sarrafawa.

Dakta Zainab Ahmed, tayi bayani filla filla cewa sakamakon Amince da ware Naira Tiriliyan 2.3 (N2.3 trillion) don kara kuzarin kasuwanci wanda Shirin Cigaban Tattalin Arzikin Kasa (NESP) ya bada Shawarin ayi, za'a kara fadada matakan da kara samar da Guraben aikin yi a fannin kasuwancin Zamani, da shirin kara Fadada Shirye shiryen samar sa guraben Dogaro (National Social Investment Programmes)
ta hanyar kara yawan Masu imfana da Shirye Shiryen kamar masu imfana da Cash transfer, N-Power Volunteers, Market Moni dakuma shirin Trader Moni.

A gabatar wa da yayi Ministan Gona, Alhaji Sabo Nanono ya fadawa Majalisar cewa, Ana sa ran Samun karuwan amfanin Gona dukda Ambaliyar ruwa da'aka samu a Arewa da karin samun Ruwan sama da ba safai ba a Kudu.

Ya kafa hujja da ba'asin kasuwa da aka gudanar na baya bayan nan, daya nuna an fara samun koma bayan haw hawan farashi kayan Masarufi.

A Bangaren sa, Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Boss Mustapha kuma Shugaban Kwamitin Shugaban kasa na yaki da Cutar Korona, Presidential Task Force on COVID-19 ya habarto samun koma baya da Annobar ta kawo akan rayuwar yau da kullum na 'yan Kasa, yayin kuma da Babban kanturola na Hukuma hana fasa kwafri na kasa Comptroller-General of Customs, Col Hameed Ali (Rtd), ya bayyana fatan na ganin an sake bude iyakokin kasar sakamakon Cigaba da aka samu ga kasashe makota akan Jami'an Sintirin iya kokin kasashen na Hadin Gwaiwa, wanda yana daya cikin Manyan Sharadodin Najeriya na sake bude iyakokin kasar.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama'a.
10 ga watan 09 2020.

JADAWALIN WASU CIKIN AIYUKA DA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA AIWATAR  DAGA SHEKARA ALIF DUBU BIYU DA SHA BIYAR (2015...
09/09/2020

JADAWALIN WASU CIKIN AIYUKA
DA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YA AIWATAR DAGA SHEKARA ALIF DUBU BIYU DA SHA BIYAR (2015) ZUWA ALIF DUBU BIYU DA ASHIRIN (2020).

A BANGAREN ILMI SHUGABA BUHARI YA CIMMA NASARORI KAMAR HAKA...

1)- Gina Jami'ar abubuwa da s**a Shafi Teku, (Maritime) a jihar Delta dake Shiyar kudu maso kudancin Najeria.

2)- Gina Jami'ar Sojin kasa (Army University) dake Garin Biu, jihar Borno shiyar Arewa maso Gabas.

3)- Gina Jami'a ta Harkokin Noma (Agriculture) dake Garin Zuru, jihar Kebbi shiyar Arewa maso Yamma.

4)- Kafa Tubalin Gina Jami'ar Sufuri a Garin Daura jihar Katsina, shiyar Arewa maso Kudu.

5)- Samar da kudade Naira Biliyan Dari Biyu (200 billon) ga Jami'oin dake kasar nan ta hanyar Hukumar Asusun Ilmin Mai Zurfi (TETFUND).

6)- Kafa Tubalin Gina Jami'a ta Sojin Sama a Garin Tafawa Balewa dake Jihar Bauchi Shiyar Arewa maso Gabas.

7)- Kafa Tubalin Samar da Sabbin Kolejojin Ilmi guda Shida (6) a Jihohi kamar haka;

A) Bauchi
B) Benue
C) Ebonyi
D) Osun
E) Sokoto
F) Edo
G) Da kafa Kwalejin Kimiyya da Safaha a Garin Daura jihar Katsina.

A BANGAREN KIWON LAFIYA SHUGABA BUHARI YAYI NASARA SAMAR DA ABUBUWA KAMAR HAKA;.

1)G- Babban Asibitin Jinya na Sojin Sama a Garin Daura Jihar Katsina.

2)- Babbn Asibin Sojin Sama a Garin Bauchi, dake Jihar Bauchi.

3)- Asibitin Mata da Kananan Yara dake Daura jihar Katsina.

4)- Gina Asibitin Soji dake Garin Kaduna jihar Kaduna.

5)- Gina Cibiyar Kula da masu dauke da Cutar Daji (Cancer) a Birnin Tarayya Abuja.

6)- Gina Cibiyar Kula da masu Dauke da cutar Daji (Cancer) a Babbar Jami'ar koyar wa ta Gwamnatin Tarayya dake Lagos. Jihar Lagos.

SAMAR DA KUDADEN TALLAFI GA JIHOHI.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samar da Tallafin kudade wa Gwamnonin Jihohi 27 daya kai Kimanin Biliyoyin Daloli don Cire su cikin Sananin Rashin kudi.

MANYA AIYUKAN GADOJI DA SHUGABA BUHARI YAKE AIWATAR WA.

1)- Babbar Gadar nan data Hada jihohin Delta da Anambra (Second Niger Bridge)

2)- Aikin Babbar Gadar nan ta Kogin Benue (Second Benue Bridge)

3)- Aikin Gina Gadar Loko zuwa Oweto data hada Jihohin Nasarawa da Benue da yankin Kudu maso Gabas.

BANGAREN TASHOSHIN JIRAGEN RUWA.

1)- Gina tashar jirgin Ruwa a Baro dake jihar Niger (Baro Inland water Port)

2)- Gina Tashar jiragen kasa a Kaduna (Kaduna Dry Port)

3)- Tashar Jirgin ruwa na shiyar Yamma a Jihar Delta (Eastern Port)

4)- Gina Gada da Hanya a tashar Bony a jihar Rivers.

SAMAR DA HUKUMOMIN CIGABAN SHIYA SHIYA.

1)- Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas (Northeast Development Commission)

2)- Hukumar Raya yankin kudu maso Gabas (SouthEast Development Commission)

GINA MANYA MANYA HANYOYIN MOTA.

1)- Babbar hanyar Lagos zuwa Sagamu zuwa Ibadan.

2)- Babbar Hanyar Kano zuwa Maiduguri.

3)- Babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

4)- Babbar Hanyar moto ta Apapa zuwa Oshodi zuwa Oworonshoki jihar lagos.

5)- Gina Sabon Hanyar Filin Girgin sama na kasa da kasa dake Birnin Tarayya Abuja.

6)- Babbar Hanyar Enugu zuwa Port Harcourt.

7)- Babbar Hanyar Abuja zuwa Keffi zuwa Lafiya zuwa Makurdi.

A BANGAREN KASUWANCIN JIRAGEN SAMA.

1)- Gina Sabon Tashar Jiragen Sama a Filin sauka da Tashin jiragen Sama na Abuja.

2)- Gina Sabon Tashar Jiragen Sama a Filin sauka da Tashin jiragen Sama na Lagos.

3)- Gina Sabon Tashar Jiragen Sama a Filin sauka da Tashin jiragen Sama na Port Harcourt.

4)- Gina Sabon Tashar Jiragen Sama a Filin sauka da Tashin jiragen Sama na Enugu.

5) Gina Sabon Tashar Jiragen Sama a Filin sauka da Tashin jiragen Sama na Kano.

A BANGAREN WUTAN LANTARKI.

1)- Gina Tashar Samar da Lantarki na Dadin Kowa a jihar Gombe.

2)- Kammala aikin Tashar Samar da Lantarki ta Kashimbilla.

3)- Bada Kwangilar Tashar Lantarki na Mambilla.

4)- Samar da tashar lantarki mai zaman kanshi a Babban Kasuwar Ariaria dake Aba jihar Abia.

5)- Samar da Tashar Lantarki mai zaman kanshi a Babbar Kasuwar Sabon Gari dake Kano, jihar Kano.

6)- Samar da Tashar Lantarki mai zaman kanshi a Rukunin Kasuwar Sura dake Lagos.

7)- Samar da Tashar Lantarki mai zaman kanshi wa Manyan Jami'oin Gwamnatin Tarayya 37 dake fadin kasar nan.

8)- Samar da Tashar Lantarki mai zaman kanshi wa Manyan Asibitocin Koyarwa guda 7.

9)- Kammala Aikin Tono Mai a Alkaleri jihar Bauchi.

10)- Samar da kudade sama da Biliyan 200 ga Jami'oin irin sa na farko a Tarihi.

BANGAREN SUFURIN JIRAGEN KASA.

1)- Gina Hanyar Jirgin kasa na Abuja Metro.

2)- Gina Hanyar Jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.

3)- Gina Hanyar Girgin kasa na Itakpe Jihar Kogi zuwa Warri Jihar Delta.

4)- Gina Hanyar Jirgin kasa na Lagos zuwa Abeokuta jihar Ogun.

5)- Gina Hanyar Jirgin kasa na Abeokuta jihar Ogun zuwa Ibadan jihar Oyo.

6)- Fara aikin Gina Hanyar Jirgin kasa daga Lagos zuwa Kaduna.

7)- Taskar baje kolin Jiragen kasa dake Ogun

SHIRIN SHUGABAN KASA BUHARI AKAN KASUWANCI DAZAI JA HANKALIN MASU ZUBA JARI ZUWA KASAR.

1)- Babban Kamfanin Sarrafa Shinkafa a yankin Afirka ta WACOT a jihar Kebbi.

2)- Babban kamfani Samar da abincin Tsuntsaye da Dabbobi a Afirka OLAM a jihar Kaduna.

3)- Babban kamfanin Samar da Suga a Afirka SUNTI dake Jihar Niger.

BANGAREN SHIRYE SHIRYE NA SAMAR DA WALWALA.

1)- Kara Albashi masu karanci na Dubu talatin 3000.

2)- Samar da aikin Npower ga Matasa Dubu dari biyar 500,000 da basu Albashin Dubu Talatin 30,000 Kowace wata.

3)- Ciyar da yara 'yan Makaranta Kyauta.

4)- Sanar da Trader Moni ga Kananan 'yan kasuwa.

5)- Samar da Farmer Mini ga Manoma.

BANGAREN KUDIN FANSHO DA GURATUTI.

1)- An biya kudin Hutu na Ma'aikatan Gwamnati.

2)- An biya kudin Guratuti na Ma'aikatan Gwamnati.

3)- Anbiya hakkokin Sojojin da s**ayi yajin Biyafara bayan Shekaru aru aru.

4)- Anbiya kudaden Jami'an 'yan Sanda da s**a kammala aiki.

5)- An biya kudaden Ma'aikatan Kamfanin jirgin Sama na kasa daya ruguje hakkokin su.

AIYUKAN SAMAR DA RUWA DA DAM NA NOMAN RANI DA GWAMNATIN SHUGABA BUHARI TA KAMMALA.

1)- Aikin Samar da Ruwa na Ogbia a Jihar Bayelsa.

2)- Aikin Samar da Ruwa na Sabke, Dutsi da Mashi a jihar Katsina.

3)- Aikin Dam na Kashimbila dake Jihar Taraba.

4)- Aikin Samar da Dam a Ogwashi-Uku dake Jihar Delta.

5)- Aikin Dam na Shagari don Noman Rani a jihar Sokoto.

BANGAREN SAMAR DA GIDAJE.

1)- Samar da Rukunin Gidaje Dubu Goma 10,000 a Jihohi 36 dake fadin kasar nan..

2)- Da Samar da wasu gidajen na daban karkashin Shirin (Buhari Quarter housing scheme) a Jihohi kasar nan.

Wannan Jadawali kadan ne Cikin Aiyukan Maigirma Shugaban kasa daya Cimma daga 2015 zuwa 2020.

Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

FADAR SHUGABAN KASA TAYI NA'AM DA HUKUNCIN KOTUN BURTANIYA AKAN RIKICIN P&ID.Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaba...
05/09/2020

FADAR SHUGABAN KASA TAYI NA'AM DA HUKUNCIN KOTUN BURTANIYA AKAN RIKICIN P&ID.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Fadar Shugaban kasa tayi Na'am da Hukuncin kotun Burtaniya nayin da Bukatar Najeriya don na lokaci da Saukaka Hukuncin cin tarar kasar Dala Biliyan Goma ($10 billion), wanda kotun Da'ar Ma'aikata ta yanke kan rikici dake tsakanin kasar da Kamfanin (P&ID). Industrious Development Limited dake Najeriya.

A Nazarin mu, Hukuncin yayi Dai de, zamu iya cewa ya Samar da wani dama mai karfi a rikicin Rashin Gaskiyar da aka tafka a Dillancin Iskar Gas tsakanin Najeriya da Kamfanin P&ID, dama hukuncin daya biyo baya da kotun ta yanke cewa Najeriya ta biya Dala Biliyan Goma ($10 billion). wanda kuma karara wani Yunkuri ne na Cutar da kasar biliyoyin Daloli da kamfanin da bai taba zuba jari a kasar mu ba.

Bisa ga yarjejeniyar da aka yi, haka wani babbar dama ce nayin na'am da kotun na Burtaniya da Sauran su, da s**a yanke Hukunci:

"Najeriya ta taka wani Babban mataki don Tunkarar rikicin kan ikirarin kasar na cewa ita kanta Kamfanin dake Samar da Iskar Gas, (Gas Supply and Processing (GSPA). An kafane ta hanyar Cin hanci da Rashawa da aka biya wasu dai-dai ku, cikin wani bangare na Babban Shirin da aka shirya na Damfarar Najeriya.

" Sa'annan kuma akwai wani babban hasken nasara a Shari'ar tunda Babban Shaida na kamfanin (P&ID). Mr Quinn, ya bada Shaidar Karya ga Kotun, da kuma bada Sabanin Shaida wanda ke nuna shi kanshi Kamfanin (P&ID) bashi da ikon tafiyar da kwangilar da yake Ikirarin yi a kasar."

Fadar Shugaban kasa ta Nuna jindadin ta, kan yadda Shara'ar ke tafiyar wanda ya haifar da wannan hukunci a kotun na Kasar Burtaniya, Fadar ta Shaida cewa hukuncin ya bada wani Dama da Saukaka wa Gwamnatin Najeriya kara bada kariya ga Kadarorin kasar daga Bata garin Kamfanoni da dai-dai kun Mutane.

Dubi da wannan Hukuncin kotun na Burtaniya, haka ya Samar da yalwataccen dama ga Gwamnatin Tarayya taci gaba da kalubalantar Damfara da kamfanin ta shirya dama ture Hukuncin kotun na farko.

A sabo da haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa Tawagar Lauyoyin da s**a Wakilci Najeriya akan Rikicin da Kamfanin (P&ID), dama kara bada tabbacin ga 'yan kasa na Gari da Sauran kasashen Duniya akan Rashin Tararrabin Jajircewar sa na Yaki da Rashawa da cin Hanci ta kowani fuska.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama'a.
4 ga watan 9, 2020.

100 SELECTED PROJECTS, PROGRAMS & ACHIEVEMENTS INITIATED, ONGOING, EXECUTED OR COMMISSIONED BY THE MUHAMMADU BUHARI'S AD...
19/08/2020

100 SELECTED PROJECTS, PROGRAMS & ACHIEVEMENTS INITIATED, ONGOING, EXECUTED OR COMMISSIONED BY THE MUHAMMADU BUHARI'S ADMINISTRATION IN 5 YEARS.

1. The second Niger Bridge
2. The Warri-Itakpe rail line
3. The Abuja-Kaduna-Kano Expressway
4. The Ilorin-Bode Sadu-Jebba Road
5. The Implementation of the TSA and BVN
6. The Lagos-Ibadan rail line
7. The approval for the establishment of 6 colleges of education in Benue, Bauchi, Sokoto, Eboyin, Osun and Benue states
8. The Ajaokuta-Abuja-Kaduna-Kano Gas Pipeline
9. National Cancer Center in Lagos State
10. The Lagos-Ibadan Expressway
11. The construction of Oju-Loko-Oweto bridge connecting Benue and Nasarawa states to the Eastern and Western States.
12. Discoveries, collection and transfer of over N500 billion from EFCC to FG purse.
13. Construction of Gombe-Biu road
14. Payments of pension arrears to 3,542 Delta steel pensioners.
15. Ongoing work on the 700MW Zungeru hydro power supply in Niger State
16. Completion of 40MW Kashambilla hydro power Station
17. Payments of pension arrears to Nitel staff
18. Dredging of the Onne port in Rivers State
19. Dredging of the Calabar Port in Cross River state
20. $3.9 billion Warri seaports.
21. Completion of Abuja-Kaduna rail line.
22. Reconstruction of Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja.
23. Reconstruction of Aminu Kano International Airport Kano.
24. Reconstruction of Port Harcourt International Airport Port Harcourt
25. Construction of new Tower & second Runway for Murtala Mohammed International Airport I Lagos.
26. Reconstruction of the Akanu Ibiam International Airport in Enugu.
27. National Cancer Center in Kano state
28. Nigeria Army University in Biu, Borno State.
29. Nigeria Maritime University, Delta State
30. Nigeria Airforce University, Bauchi state
31. Nigeria Airforce Hospital, Daura, Katsina state.
32. Presidential Fertilizer Initiative on fertilizer saw a disruption from importation to local production of over 10 million tonnes.
33. Payments of pensions to ex Biafran soldiers.
34. National Cancer Center in Umuahia, Abia state.
35. Implementation of the FG N30,000 minimum wage
36. Approval for N33,000 minimum allawee to NYSC
37. Inauguration of Baro ports at 28% status.
38. Purchase of 38 brand new fighter jets for the Nigeria Airforce.
39. National Housing Program across Nigeria. To build 300,000 houses in all, over 25,000 houses of low, medium and high income in all the 6 geopolitical zones.
40. Construction of Konar Dumawa-Kunya-Babura to Níger Republic
41. Construction of Gaya-Jahun-Kafin Hausa road in Jigawa state.
42. Total overhaul of Nigeria Army weaponry through purchase of armoured carriers from China and Russia.
43. Establishment of Federal University of Agriculture in Zuru, Kebbi state.
44. Completion of the Zobe dam in Katsina state.
45. Approval and released of N75 BILLION Farmers money to cover for agricultural activities as first batch to states.
46. N20 billion Credit loan of N10,000 to 2 million Nigerians.
47. Engagement of 500,000 Nigerians and payment of N30,000 monthly for 3 years in Batch B of the Npower scheme.
48. Payment of N5,000 each monthly to 3.2 million vulnerable Nigerians in the last two years.
49. Establishment of the Federal University of Transportation in Katsina state.
50. Four (4) rehabilitated and reconstructed roads in BUK in Kano state.
51. 2.8MW solar power plant in Federal University of Technology in Eboyin state.
52. Provision of 2MW solar power plant in Bayero university in Kano state
53. Supply of solar panel grid for power supply to Nnamdi Azikiwe University in Anambra state.
54. Completion of the Abuja airport-City center rail line.
55. Ongoing total overhaul of the power sector with the FG/Siemens 25,000 power generation transmission and distribution power road map. FG already paid N8.7 billion counterpart funding.
56. Ongoing reconstruction of the Enugu-Port Harcourt dual carriageway.
57. Ongoing reconstruction of the Onitsha-Enugu Expressway
58. Ongoing reconstruction of the Benin-Ofosu-Ore-Shagamu Expressway
59. Ongoing dualization of the Ibadan-Ilorin Expressway
60. Ongoing rehabilitation and expansion of the Lagos-Badagry Expressway
61. Ongoing rehabilitation of the Lagos-Otta road
62. Ongoing dualization of the Obajana junction-Auchi-Ehor-Benin road.
63. Ongoing reconstruction of the Enugu-Port Harcourt DCW Aba-Port Harcourt section.
64. Ongoing dualization of Yenegwe-Kolo-Otuoke-Bayelsa road.
65. Ongoing construction of the Ikom Bridge in Cross River State.
66. Ongoing dualization of Sapele-Ewu road in Delta State.
67. Ongoing reconstruction of the Alesi-Iyamoyung-Ugep road in Akwa-Ibom state.
68. Ongoing dualization of the Suleja-Lambatta-Minna road in Niger State.
69. Ongoing construction of the Gwagwalada-Abaji-Kotonkarfe-Lokoja Expressway
70. Ongoing reconstruction of the Bida-Lapai-Lambatta road in Niger State.
71. Ongoing reconstruction of the Makurdi-Naka-Adoka-Ankpa road.
72. Construction of road linking Baro ports to Gulu town in Niger State.
73. Ongoing Keffi-Akwanga-Lafia-Makurdi Expressway
74. Ongoing dualization of Akwanga-Jos-Bauchu-Gombe Expressway
75. Ongoing dualization of the Kano-Maiduguri Expressway Shuari link to Azare to Potiskum to Damaturu to Maiduguri.
76. Ongoing rehabilitation of Gwoza-Damboa-Goriri road in Borno State (Commencing)
77. Ongoing reconstruction of the Mayo-Jada-Ganye-Tougo road in Adamawa state.
78. Commencement of the construction of the Ibi Bridge in Taraba state linking PLATEAU, Benue and other states.
79. Ongoing rehabilitation of the Nguru-Gashua-Bayamari road(Just awarded as work is commencing soon)
80. Ongoing reconstruction of the Kano-Maiduguri Expressway linking Wudil to Shuari.
81. Ongoing dualization of the Kano-Katsina Expressway.
82. Approval for the Kano-Kaduna rail line.
83. $5.6 billion approval for the Ibadan-Ilorin-Minna-Kaduna-Kano rail line.
84. Establishment of the Nigeria/Chinese train coaches and wagon workshop and training center in Ogun state.
85. Ongoing construction of the Kaduna eastern bypass.
86. Ongoing construction of the Kano Western bypass.
87. Rehabilitation of the Sokoto-Jega-Kontagora-Makera road across Sokoto, Kebbi and Niger States.
88. Establishment of the N75 billion Nigeria Youth Investment Fund. Youth Bank
89. Establishment and commencement of the North East Development Commission.
90. Bailing off 27 failed states unable to pay salaries in 2015.
91. The establishment of the N50 billion Household TCP
92. Recruitment of 10,000 police officers in 2015/2016.
93. Putting up the Covid-19 financial support for SMEs. N50 billion for payroll support, N200 billion for loans to artisans and N10 billion to private transport companies.
94. School feeding program sees the feeding of 9.1 million pupils in 32 states of the federation.
95. Total overhauling of the Ajaokuta steel company with the released of over N10 billion as counterpart funding to the Russians.
96. Approval and commission of the Ariaria IPP in Abia state.
97. Approval and Commissioned of the 10MW IPP at the Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja.
98. Ongoing recruitment of 400,000 police to reinforce the wide gap for effective community policing.
99. Ongoing recruitment of 400,000 for the Batch C Npower program.
100. Payments of the backlog of pension arrears to 9,216 federal government pensioners in 2018. N24 billion was paid and all payroll into the system.

14/08/2020

NAJERIYA NA SAMUN CIGABA A MAIDO DA KAYYADE SAMUN TAKARDAN BIZA NA KASAR AMURKA: CEWAR SHUGABA BUHARI.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Najeriya na samun cigaba kan Dakatar da samun takardan biza da Kasar Amurka tayi "Immigrant Visas" ga 'Yan Najeriya da s**a mallaki takardan Fasfo, a cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari yau a birnin Abuja.

A lokacin daya amshi Rahoton Kwamiti kan bayanan 'yan Kasa karkashin Shugaban cin Ministan Cikin gida Rauf Aregbesola, Shugaban kasa ya nuna jin dadi kan cewa an magance matsaloli biyu cikin guda shida da kasar Amirka ta nuna damuwa akai.

Kwamitin wanda aka kafa a watan Febuweru na wannan Shekara da zumman magance matsaloli dayayi sanadiyar da kasar Amirka ta dakatar da takardan biza ga masu rike da takardun fasfo na Najeriya.

Da katarwar, wanda yafara aiki a ranar 21 ga watan Febuweru, 2020, bai shafi wadan da keda takardan bisa kasar Amurka kamar su Jami'an Gwamnati, 'Yan kasuwa, Masu yawan bude Ido dakuma masu tafiya karatu a kasar ba.

Dayake Yabawa wa Kwamitin kan nuna kishin kasa da yin aiki tukuru yayin gudanar da aikin da aka rataya a wuyar su, Shuagaban kasa Buhari ya bada tabbacin ga 'Yan Najeriya da Sauran kasashen Duniya kan aiki da Shawarwari da kwamitin ya bada akan lokaci bayan an nazarci rahoton yadda yakamata.

"Na kuma San irin cigaba da Nigeriya ta samu akan batun cire dakatar da samun takardar biza nasa sanun magance kaso biyu cikin shida na Dalilan da Gwamnatin kasar Amurka ta nuna, an kammala da kaso biyu yayin kuma da ake samun cigaba akan kaso biyu da s**a rage.

" Nayi murna akan samun wannan Cigaba, musamman kan tura bayanan fasfo daya bata ko kuwa aka sace da sauran muhimman takardun tafiye tafiye da Gwamnatin Amurka ta amince dashi," Inji Shugaban kasa.

Cikin Shawar warin kwamitin sun hada da kafa Hukumar bayanan bata gari na kasa (National Criminal Information Management), wanda zai tafi kan tsarin Hukumar 'yan sanda na kasa da kasa (INTERPOL model), dakuma National Criminal DNA Laboratory, don taimakawa kan bincike akan bata gari da tafiyar da Hukuncin bata gari dana de rarraba bayanai da suke da alaka da haka.

Shugaba Buhari ya shaida cewa aiki da wadan nan kamar yadda aka bayyana a rahoton zai magance dukkanin sauran matsaloli da s**ayi sanadin dakatar da samun takardan na visa.

"Samar da cikakken tsarin hukumar tattara bayanai abune da keda muhimmanci kan tsarin tafiyar jin dadin kasuwanci, da kara inganta gudanar da aiyuka dakuma tafiyar da Gwamnati mai kyau, dama kuma tsaron kasa da ketare. Hakan kuma nada wasu amfanin na daban a fannin inganta Tagomashin shaidan 'Yan kasa da zummar rarraba bayanai.

"Bisa tsari da bin ka'idoji, shawar warin kwamitin kan Tsara da sake nazartan bayanai da tuntuni ke akwai, da kara inganta muhimman bayanai 'yan kasa dama kara sa ido kan aikin Hukumar National Identity Management Commission dazai samu kulawa ta musamman.

" Gabatar da Shawar warin kamar yadda kwamitin ya kwatan ta zai samar da hanyoyin Samun kudi da yawa. Akan wannan batu za'a kafa wata kwamitin dazai aiki da shawarin da aka bada da kara nazartan dukkan Shawarin da kara fadada fasali yadda za'ayi aiki dashi," Cewar Shugaban kasa Buhari.

Shugaban kasa yakuma yi Alkawari yunkurin Gwamnatin tarayya na cigaba da bibiyan don ganin an cire dokar dakatar da takardan biza da Gwamnatin Amurka tayi, dakuma sake nazari kan tsarin tattara muhimman bayanai na 'yan kasa.

Shugaba kasa Buhari yayi waiwaye kan Amsar da Gwamnatin Tarayya ta bada kan Dakatar da samar da takardan biza data sa kan 'Yan Najeriya da kasar Amurka tayi a watan Janeru na wannan Shekara, wanda haka yayi sanadin kafa kwamiti daze kara nazartan dakatarwan da samar da tsari da shimfida yadda za'a magance barazanar tsaro da kasar ta Amirka tayi nuni.

" Bisa dubi kan gaskiyar batun Damuwar da kasar ta nuna ya jefa shakku kan Sahihancin tsarin tattara muhimman bayanai na 'yan kasa, an fadada aiyukan Kwamitin wanda ya kunshi tsara da sake dubi kan muhimman bayanai na 'yan kasa dake a hanun Ma'aikatun Gwamnati, Hukumomi da Cibiyoyi daban daban.

" Na duba wasu Rahoton kwamitin kuma dole a yabawa Shugaba da Membobin Kwamitin bisa yadda s**ayi tunani gurin tafiyar da aikin su dukkan Kalubale da Annobar Cutar Numfashi ta Korona ta janyo.

Shawar warin kamar yadda ya nuna zai iya magance Damuwa da Gwamnatin kasar Amurka ta gabatar dama kuma jagorantar ya za'a samo tsarin Tattara muhimman bayanai na 'yan kasa." Cewar Shugaban.

A Jawabin sa, Ministan Cikin Gida kuma Shugaban Kwamiti kan kan sake nazartan Hukumar tattara Muhimman bayanai na 'yan kasa, Ogbeni Rauf Aregbesola, yayi waiwaye kan ranar 3 ga watan Febuweru, 2020, ranar da aka kafa kwamitin da sauran abubuwa, na kara dubi kan dakatar da samar da takardan biza da Gwamnatin Amurka ta kakaba, da kuma samar da tsari dazai magance barazanar tsaro da kasar tayi nuni.

Wani aiki kuma da aka rataya a wuyan kwamitin, cewar Ministan, shine sake dubi kan bayanan 'yan kasa dake aje, ciki harda Hoton yatsun hanu, da Ma'aikatun Gwamnati daban daban keda su da Hukumomi da Cibiyoyi, da kara nazari da samar da tsari na bai daya.

Cikin farin ciki ya kayi rahoton cewa Najeriya ta gamsu matuka da kaso biyu cikin Shidda na Damuwar da kasar Amurka tayi nuni dashi, wasu biyu kuma an dan gansu dasu kuma ana samun cigaba kan sauran guda biyu daya rage.

"Muna fatan cewa za'a samu mafita, tsarawa da Gabatar da shirin da aka yi, Matukar aka gabatar dashi yadda ya dace, za'a dage dakatar da samar da takardan bisar, a sa'ili guda kuma kawo sauyi kan tsarin bayanan 'yan kasa," a cewar Ministan.

Femi Adesina:
Babban Mai Bada Shugaban Kasa Shawari kan kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan jama'a
13 ga Watan Agusta , 2020.

SHUGABA BUHARI YA KADDAMAR DA GININ BENE MAI TSAWO 17 NA HUKUMAR NCDMB, YAYI ALKAWARIN KASHE KUDADE MASU YAWA KAN  MANYA...
14/08/2020

SHUGABA BUHARI YA KADDAMAR DA GININ BENE MAI TSAWO 17 NA HUKUMAR NCDMB, YAYI ALKAWARIN KASHE KUDADE MASU YAWA KAN MANYAN AIYUKA DON SAMAR DA AIYUKAN YI.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranan Alhamis a Abuja ya yi alkawarin karin samar da kayayyakin more rayuwa a fadin kasa, ta hanyan mai da hankali akan kammala aiyuka daga yan kwangila na gida da kuma sarrafa fasaha wanda dai samar da aiyukan yi ma dubban yan Najeriya.

Shugaba Buhari yana magana ne ta kafar sadarwa a lokacin kaddamar da sabon hedkwatar ginin Nigerian Content Development and Monitoring Board (NCDMB) a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa.

Shugaban kasa yace ginin mai hawa sha bakwai 17, wanda aka san shi a matsayin Nigerian Content Tower, wanda ya ke dauke da wutan lantarki mai karfin Mega wat goma 10 da kuma dakin taro mai daukan mutane guda dubu 1000 yayi nuni da cewa gwamnatin sa data ci gaba da samar da kayan more rayuwa a fadin kasa baki daya domun jan hankalin masu zuba jari, samar da aiyukan yi da kuma kauda da talauci.

"tare da shaida bude wannan aikin, ni ina so in haskaka cewa wannan mun ajiye wani alama wanda dai zama shaida a wannan yanki na Niger delta domun ya wakilci wani dogon tarihi na cewa saka hannu na shekaru man fetur da iskar gas amfani da kuma ni ina bada tabbaci cewa akwai karin abubuwa suna zuwa inji shi. "

Shugaba Buhari yayi amfani da taron ya bayyana jin dadin sa cewa dubban aiyuka ne na kai tsaye da kuma kaikaicce dasu samu aiyuka a lokaci kawo wannan aikin gudu da kari sauran kasuwanci daban daban dasu samu zarafi.

"wannan kaddamar wan dai ayi da muhimmancin gida cikin dukkanin aiyuka a matakin rayuwa na kasa musamman tare da kariya akan annobar cutar korona COVID:-19

"ni nayi imanin cewa karfi akan kayan da mu ke sarrafawa kuma dai taimaka namu kaya kuma aiki a matsayin wani hanyan tabbata an karfafa samar da aiyukan ma yan kasa kuma ya basu wani dama domun zaban wani fasahohi na sana'a da kuma kasuwanci fitattu.

"cewa ne don me aka gabatar da umurni na sakamako biyu karkashin wannan gwamnatin mu wanda ya tilasta amfani da kayan gida cikin aiyuka da kuma kwangila zuwa ga rubunya samun nasarorin su kasancewa an dogara bangaren masana'antun man fetur da iskar gas.

"kayan cikin gida da kuma dogaro da kai shine ginshikin amincewa da kudi har Naira Tiriliyan biyu da digo uku 2.3 trillion cikin tsarin tattalin arziki na kasa da aiki tare. shirin yana da nufin kara daukaka, kayan cikin gida kayan al'adu da kuma amfani da kayayyakin gida. inji shi.

ya yaba ma Ma'aikatan kula da albarkatun man fetur da karamin Ministan albarkatun man fetur, shugaban hukumar gudanarwa da kuma hukumar da ma'aikatan wannan hukuma na Nigerian Content Board akan wannan nasara, inji Shugaban kasa.

wannan ginin da muka kaddamar yau ya kasance ranan haihuwa kyauta a matsayin shekaru goma 10 a matsayin kayyadewa da kuma ci gaba kayan gida watacce cikin masana'antu man fetur da iskar gas.

"Ni haka naji dadi cewa wannan aikin mun kammala shi daga goyon baya na yan kwangila na cikin gida da sauran injiniyoyi da kuma masu saka shawara a aiki. mu dole dukkanin mu muyi alfahari cewa mun kare wannan aiki.

"mata da kuma maza ni ina so nayi muku godiya akan kasancewa wani sashi na wannan abun tarihi na lokaci har a matsayin wannan amfani da damar godiya ma mutanen Bayelsa da kuma taya su murna a matsayin masu masaukin baki na wannan aiki abun tarihi cikin zuciyar Niger delta.

"shine tare jin dadi da yarda cewa ni na bada umurni na shaidawa karamin Ministan albarkatun man fetur da ya kaddamar da wutan lantarki na Mega wat goma 10, da dakin taro mai daukan mutane guda dubu 1000, wanda aka fi sani da dakin taro na NCDMB da kuma har ila yau kaddamar da gini hawa sha bakwai 17 a matsayin Nigerian Content Tower amadadin ni. "

Femi Adesina:
Babban Mai bawa Shugaban kasa Shawara kan kafofin Watsa labarai da Wayar da kan jama'a
13, ga Watan Agusta na Shekarar 2020.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wikki Leaks News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share