Al Hamid TV

Al Hamid TV Wannan shafi an bude shi don kawo labarai da video

https://youtu.be/HtFeYFlmE74 ku kalla kuyi subscribe comments like@shares
15/05/2022

https://youtu.be/HtFeYFlmE74 ku kalla kuyi subscribe comments like@shares

Assalamu akaikum yan'uwa muna maku Barka da ziyartar wannan channel ta HAMID TECH TV 📺 kudanna muna subscribe da kwaraurawar domin samun sabbin Darussanmu m...

DA DUMI-DUMIN SU!Ado Gwanja ya saki matar sa Maimuna saki har 3 Majiyar mu ta Taskar Tsakar Gida tace Ado Gwanja ya saki...
09/02/2022

DA DUMI-DUMIN SU!

Ado Gwanja ya saki matar sa Maimuna saki har 3

Majiyar mu ta Taskar Tsakar Gida tace Ado Gwanja ya saki matar sa Maimuna, inda a wani bincike da Tashar ta YouTube ta gudanar ta gano cewa mawaƙin ya sauwakewa matar tashi, kuma sakin ba daya ba har saki uku.

Tashar Tsakar Gida sun tambayi dalilin saɓanin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi da yin sakin ba su samu wani gamsashshen bayani ba, amma dai sun tabbatar da rabuwar auren masoyan, wanda zai bakanta ran dubunnan masoyan su.

Maimuna Ta Cire Abubuwan Da S**a Shafi Ado Gwanja a Shafinta

Haka kuma a wani bincike da Tashar Tsakar Gida ta sake gudanarwa a shafin Maimuna, sun gano cewa ta cire duk wani abu da ya shafi Ado Gwanja a shafinta, hatta sunan Ms Ado Gwanja da ta sa ta cire ta sa sunan “Fashion Beauty”, haka shafin da take kasuwancin ta mai suna “Munat Gwanja Collection” shi ma ta canja shi zuwa “Munat Dan’auta Collection”.

Baya ga wannan, sanin kowa ne jarumin kan shirya kasaitaccen bikin “Birthday” ga matar tashi da ƴar sa duk shekara, amma wannan shekarar Maimuna ita kaɗai tayi ƴan hotunanta ta wallafa a shafin ta, kuma Ado Gwanja bai taya ta murna a shafin shi ko sashen tsokacin ta ba.

Bugu da ƙari a watan da ya gabata, mahaifiyar Maimuna ta rasu shi ma ta wallafa a shafin ta jaruman Kannywood na ta yi mata ta’aziyya, amma Ado Gwanja bai ce komai ba, haka kuma bai wallafa a shafinsa ba.

Ado Gwanja Ya Bayyanawa BBC Hausa Ba Zai Yi Mata Kishiya Ba

Haka kuma kowa dai yasan irin soyayyar da shakuwar da masoyan ke bayyanawa juna a shafukan sada zumunta, domin har hira BBC Hausa ta yi da Ado Gwanja, inda ya tabbatar da cewa ba zai yiwa matar sa kishiya ba.

Baya ga haka, kowa ya san yadda jarumin yake yawan wallafa hotunan matarsa tare da rubuta kalamai na soyayya da yake mata.

Haka ita ma an gano hotunan ta da bidiyo a wuraren shakatawa ba tare da siffa ta matar aure ba.

Shin meye ra'ayin ku ne?

Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin nera na intanet a ranar Litinin. Shin za ku yi amfani da shi?Hoto: Bashir Ahmad
25/10/2021

Shugaba Buhari ya kaddamar da kudin nera na intanet a ranar Litinin. Shin za ku yi amfani da shi?

Hoto: Bashir Ahmad

Dama Na faɗa muku tun a baya cewar nine zan iya gyara Najeriya domin dawo da zaman lafiyarku ~ Atiku Abubakar.Masu karat...
22/10/2021

Dama Na faɗa muku tun a baya cewar nine zan iya gyara Najeriya domin dawo da zaman lafiyarku ~ Atiku Abubakar.

Masu karatu me zakuce?

Yan bindiga sun kashe 'mutum 12' a Jihar ZamfaraBello MohammedCopyright: Bello MohammedWasu 'yan bindiga sun kashe mutu...
15/10/2021

Yan bindiga sun kashe 'mutum 12' a Jihar Zamfara

Bello MohammedCopyright: Bello Mohammed
Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum fiye da 10 a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda ta Jihar Zamfara ranar Alhamis da dare.

Wani ɗan asalin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun afka wa garin Sakajiki, inda s**a ƙona motoci kusan bakwai ciki har da ta 'yan sanda biyu.

Mutumin wanda muka ɓoye sunansa saboda dalilai na tsaro ya ce har yanzu bai yi magana da 'yan uwansa ba da ke Ƙaura Namoda saboda katse layukan waya da aka yi.

Sai dai ya ce sun samu labari daga waɗanda s**a samu fita daga garin zuwa Gusau babban birnin jihar cewa mutum 12 ne aka kashe tare da ƙona shaguna masu yawa.

Gwamnatin Zamfara a yankin arewa maso yammacin Najeriya ta katse layukan salula da zummar katse hanzarin 'yan fashi da ke zaune a dazuka masu garkuwa da mutane. Daga baya an buɗe layukan a Gusau

INNA LILLAHI  WA INNA ILAIHI RAJI'UNA!SAKAJIKI  MUN  KWANA CIKIN TASHIN HANKALI, MUN TASHI CIKIN MUMMUNAN TASHIN HANKALI...
15/10/2021

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UNA!

SAKAJIKI MUN KWANA CIKIN TASHIN HANKALI, MUN TASHI CIKIN MUMMUNAN TASHIN HANKALI!

Tun misalin karfe 9 na daren jiya Alhamis 6arayi ke cin karensu ba babbaka har kusan wayewar garin yau! A garin namu na sakajiki!

Sun kashe mutanen da har yanzu bamu gama sanin adadinsu ba!

Sun kone motoci, ciki har da mopol guda biyu!

Sun kone wurin kwanan mopol dinmu duk da mopol din sun yi iya bakin kokarinsu, amma abin ya fi karfinsu!

Sun kone muna shaguna da dukiyoyin da har yanzu ba mu san adadinsu ba!

Sun kora shanu da tumakai da awakai da ba mu san iya adadinsu ba!

Babu abinda za mu ce sai Inna lillahi wa inna ilaihi raji'una. La haula wala kuwwata illa billahi!

Muna kira ga Gomnatin jahar zamfara, karkashin jagorancin maigirma Gomna Dr. Bello Muhammad matawallen maradun, Barden kasar hausa, da Ya taimaka Ya kai muna agajin gaggawa a sakajiki! Domin wallahi Al'umma na cikin hali!

Muna rokon Allah Ya gafartama duk wadanda s**a rasa rayukansu! Allah Ya ba wadanda s**a jikkata lafiya! Wadanda aka kone ma shaguna da motoci da dukiyoyi Ubangiji Allah Ya mayar masu da mafi alkhairi! Allah Ya amintar damu, Ya kare gaba. Allah Ya kawo muna zaman lafiya a zamfara da Najeriya baki daya ameen.

Yau kwanaki ashirin (20) cif da wasu mutane bata gari s**ayi garkuwa da Mai Martaba Sarkin Fulanin Bungudu Alh. Hassan A...
05/10/2021

Yau kwanaki ashirin (20) cif da wasu mutane bata gari s**ayi garkuwa da Mai Martaba Sarkin Fulanin Bungudu Alh. Hassan Attahiru akan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

📮 Abdul Balarabe

Babban Daraktan Yada Labarai na Gwamnan Zamfara Malam Yusuf Idris ya bayyana cewa, Gwamna Bello Matawalle ya shiga cikin rudani na awanni (48) bayan da ya samu labarin sace Sarkin Bungudu Alh Hassan Attahiru.

Mai taimakawa gwamnan kan harkokin watsa labarai ya ce, Gwamnan ya kadu sosai kuma ya tausaya akan abunda da ya faru da sarkin sannan kuma yana daukar matakan da s**a dace don ganin an sako shi ba tare da wani sharadi ba daga wadanda s**a sace shi.

Ya ce, tun shekaru biyu da s**a gabata tun lokacin da ya fara aiki da Bello Matawalle bai taba ganin ranar da Gwamna Bello Matawalle ya harzuka fiye da lokacin da aka sanar da shi cewa an sace Sarkin Fulanin Bungudu Alh. Hassan Attahiru ba.

Ya yi bayanin cewa duk da cewa an yi garkuwa da sarkin a cikin yankin Kaduna, gwamnatin jihar tana yin hadin gwiwa tare da hukumomin tsaro don ganin an sako shi ba tare da wani sharadi ba.

Dangane da zargin daya daga cikin masu kallon shirin Thunder Blowers kai tsaye na “Tiryan-Tiryan” Jameel Umar Bungudu cewa gwamnatin jihar Zamfara ba ta aike da tawaga don ta’aziyya ba, kuma ba ta taimaki iyalan sarkin ba, Yusuf Idris ya ce idan aka saki Sarkin mutane za su ji kokarin gwamnatin jihar daga shi kansa sarkin.

Ya ce fatan alherin Gwamna da haƙiƙanin alherin mutanen Zamfara shi ne tabbatar da sakin sarkin ba tare da wani lahani ba, yana mai ba da tabbacin ƙoƙarin da ake kan yi, kuma ana kan gaba don cimma abunda ake bukata.

Muna rokon Allah SWA ya bayyana shi cikin aminci. Muna rokon Allah ubangiji ya kubutar dashi ya kuma dawo dashi cikin iyalansa lafiya.

Wani hali Kuka tsinci kanku a ciki, lokacin da Kuka rasa damar shiga dukkannin Manhajojin nan????Daga: ULR
04/10/2021

Wani hali Kuka tsinci kanku a ciki, lokacin da Kuka rasa damar shiga dukkannin Manhajojin nan????

Daga: ULR

"SUNANA ALIYU HUSSEIN" SAHABI A ƘWANA CAS'IN....Da yawan mutanen dake ta yada hoton Matata Hassana har suke kokarin aiba...
15/06/2021

"SUNANA ALIYU HUSSEIN" SAHABI A ƘWANA CAS'IN....

Da yawan mutanen dake ta yada hoton Matata Hassana har suke kokarin aibata halittar ta, sun san ni bayan dana zama SAHABI a cikin shirin Kwana Chasa'in, basu sanni a lokacin da nake Aliyu ba....

Alhamdulillah Hassana ta kaunaceni a lokacin da ni ba kowan kowa bane, lokacin da hatta a unguwarmu ba kowa bane yasan dani, don haka ne nima na rike alkawarin ba zan iya rabuwa da Hassana ba, koda kuwa me na zama a wannan duniyar...

Akwai Yan'mata masu yawa da s**a nuna kauna gareni a yanzu bayan dana zama SAHABI, to amma anya kuwa Aliyu suke so, kodai Sahabin Kwana Chasa'in suke so...?

Soyayya ta tsakani da Allah Hassana ke yimun, haka nima dai soyayya ta gaskiya nake mata, ni da ita ba kyale kyale muka kalla ba...

Ni Aliyu Hussain ina cigaba da yiwa Allah godiya sak**akon kyautar Mata Hassana daya bani, ina kallon kyawunta kwatankwacin sarauniyar kyau ta duniya, ina addu'ar Allah ya hadani da Matata Hassana a aljana....."

Rabiu Biyora

Hattara !!!!Fadakarwa.Irin wannan rigar waya yana burge mutane matuka, musamman ma samari.Ko kun san kalolin nan me suke...
05/06/2021

Hattara !!!!
Fadakarwa.

Irin wannan rigar waya yana burge mutane matuka, musamman ma samari.
Ko kun san kalolin nan me suke nufi?

Wannan ba komai bane face tutar LGBT ma'ana masu auren jinsi daya.

Aiki da wannan rigar wayan na nuna goyon baya ga auren jinsi daya Koko, yana nuna kana daga cikin su.

Sayan sa da anfani dashi yana kara ma kungiyoyin karfin tattalin arzikin da karfin gwiwa.

A kasashen turai duk Wanda yake rike da Shi an San me yake nufi.

Turawa sun rantse ta kowane hali sai sun sa musulmai hanyar bata.

Mu karfafa bincike da kuma karatu.

Allah ganar da mu.

Najeriya ta zama kasar bakin ciki da tashin hankali saboda rashin iya shugabancin Buhari~ObasanjoTsohon shugaban kasar N...
04/06/2021

Najeriya ta zama kasar bakin ciki da tashin hankali saboda rashin iya shugabancin Buhari~Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cheif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa Najeriya ta zama kasar tashin hankali da bakin ciki a wannan lokaci da ake.

"A can da Najeriya kasa ce mai dadin rayuwa, amman yanzu ta zama kasar bakin ciki da tashin hankali saboda rashin iya shugabanci daga shugabannin da ke shugabantar a yanzu".

"Doli ne mu tashi tsaye mu hada kai don ceto Najeriya tun kafin ta wargaza".

Obansanjo ya bayyana hakan ne a yayin wani bikin Littafe da aka yi a dakin kayan tarihi na "Obansanjo Library" dake Abeokuta k**ar yanda jaridar Punch ta wallafa.

Shin ya kuke kallon wadannan kalamai na Obasanjo ne?

Nasara
Media News

Assalam yan uwa da abokan arziki ina mai tallata maku youtube channel ta mai suna HAMID TECH TV da na bude wanda take ko...
27/05/2021

Assalam yan uwa da abokan arziki ina mai tallata maku youtube channel ta mai suna HAMID TECH TV da na bude wanda take koyar da abubuwa masu muhimmanci da s**a shafi sirri waya dafatan zaku yi mani subscribe subscribe don nuna goyon baya ga link a kasa https://youtube.com/channel/UCpT1mJuq0dipI4BeWCdqtEw

Assalamu akaikum yan'uwa muna maku Barka da ziyartar wannan channel ta HAMID TECH TV 📺 kudanna muna subscribe da kwaraurawar domin samun sabbin Darussanmu m...

Sallar Tuhajjud | An K**a Namiji Da Hijabi A Cikin MataKungiyar 'yan Bijilante ta k**a wani katon gardi da hijabi a ciki...
04/05/2021

Sallar Tuhajjud | An K**a Namiji Da Hijabi A Cikin Mata

Kungiyar 'yan Bijilante ta k**a wani katon gardi da hijabi a cikin mata yayin sallar Asham a cikin wani masallaci da ke yankin unguwar Uku' Yan Awaki.

Wata matashiyar budurwa da ta tafi Sallar Asham da wayar ta, bayan an idar da Sallar ta duba ba ta gan ta ba, sai ta fara zargin makociyar ta da su ka yi Sallah a wuri daya.

Matashin da ake zargi mai shigar mata bayan ya dauki wayar, sai ya tafi bayan bandaki ya na cire kayan matan, su kuma 'yan bijilante s**a k**a shi.

Matashiyar da aka dauke wa wayar ta bayyana wa majiyar Zuma Times Hausa cewa, "Har mu ka rabu da matashin ina tsammanin 'yar uwa ta ce mace". Inji matashiya.

Kwamandan Bijilant na yankin, Adamu Abubakar Fiya-fıya ya shedawa Kyakkyawan mu Abba Ibrahim Lafazi cewa, "Akwai bukatar 'yan agajin masallatai su kara zage dantse yayin zabukan da Tahajjudi".

Dan Takaitaccen Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.Daga Aliyu Adamu Tsiga An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan ...
02/05/2021

Dan Takaitaccen Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda s**a kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.

Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.

Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.

Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.

Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun 'yancin kai.

Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista.

Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo s**a jagoranta

DA DUMI-DUMIN SU!Yanzu-yanzu fusatattun matasa sun kone wanda ya yi batanci ga Annabi a LagosWasu fusatattun mutane a ya...
02/05/2021

DA DUMI-DUMIN SU!

Yanzu-yanzu fusatattun matasa sun kone wanda ya yi batanci ga Annabi a Lagos

Wasu fusatattun mutane a yankin babbar kasuwar Mile 12 International Market dake Lagos sun kone wani kwamanda ‘yan banga mai suna Haladu Muhammad biyo bayan batanci ga Annabi S.A.W ta hanyar babbaka masa wuta.

LABARI DA DUMI-DUMIN SA!Saura kwana 5 kacal mu rufe layukkan da ba a hada da NIN ba~ PantamiWa’adin da hukumar da ke kul...
02/05/2021

LABARI DA DUMI-DUMIN SA!

Saura kwana 5 kacal mu rufe layukkan da ba a hada da NIN ba~ Pantami

Wa’adin da hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya karkashin jagorancin Minista Pantami wato NCC ta ɗiba domin yin rajistar layin waya da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN saura kwana 5 kacal ya kare.

NCC ta tunatar da ƴan Najeriya a shafinta na Twitter cewa ranar shida ga watan Mayu wa’adin da ta bayar zai cika.

Don haka hukumar ta bayyana cewa nan da kwana 5 duk layin wayar da ba a yi wa rajista ba da lambar NIN za a rufe shi nan take.

Likitan da ya taimaka aka kashe Osama bin Laden ya nemi a sake shiYayin da ake cika shekara 10 da kisan Osama bin Laden,...
02/05/2021

Likitan da ya taimaka aka kashe Osama bin Laden ya nemi a sake shi

Yayin da ake cika shekara 10 da kisan Osama bin Laden, likitan da ya taimaka wa hukumar leƙen asirin Amurka CIA gano maɓuyar shugaban na Al Ƙai'da ya yi kiran a sake shi.

Lauyan da ke kare likitan ɗan ƙasar Pakistan ya shaida wa BBC cewa ya k**ata a sake shi.

An yanke wa Shakeel Afridi, hukuncin ɗaurin shekaru 23 a gidan yari bayan kashe Osama a wani samamen da Amurka ta kai shekaru 10 da s**a gabata.

Lauyan Afridi, Qamar Nadim Afridi, ya ce ya yi imanin cewa an yi yunƙurin dakatar da soke hukuncin a shari’ar don kaucewa wanke likitan a cikin abin da ya bayyana a matsayin “karya”.

Wasu da dama sun imanin cewa an hukunta likitan ne saboda abin kunyar da ya janyo wa Pakistan

Hukumar leken asirin ta CIA ta gudanar da rigakafi ne na bogi shekaru 10 da s**a gabata, karkashin jagorancin Doctor Afridi, da nufin gano Osama bin Laden.

INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI'UUN!Allah ya yi wa wannan baiwar Allah rasuwa a yau juma'a a wajen haihuwaKu sanya yar uw...
17/04/2021

INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI'UUN!

Allah ya yi wa wannan baiwar Allah rasuwa a yau juma'a a wajen haihuwa

Ku sanya yar uwa ta a cikin addu'a Allah ya karbi ranta a yau juma'a a wajen haihuwa.

Ubangiji Allah ya jikan ki da rahama sister.

Daga: Fatima Muhammad

Malamar makarantar da ta rasa rayuwar ta wajen ceto dalibai da gobara ta rutsa.
14/04/2021

Malamar makarantar da ta rasa rayuwar ta wajen ceto dalibai da gobara ta rutsa.

Wani dalibin jami'ar tarrayya dake Gusau yana cigiyar naira dubu biyunsa (₦2000 ) da ya yarda daga Sabon Gida Zuwa Feder...
14/04/2021

Wani dalibin jami'ar tarrayya dake Gusau yana cigiyar naira dubu biyunsa (₦2000 ) da ya yarda daga Sabon Gida Zuwa Federal University Gusau.

Wasu sun ce Dalibin Mutumen Kano ne.

Da Dumi-Dumi: An ga watan Ramadan a Nigeria Assalamu alikum fadar mai alfarma Sarkin Musulmi na Nigeria, Sa'ad Abubakar ...
12/04/2021

Da Dumi-Dumi: An ga watan Ramadan a Nigeria

Assalamu alikum fadar mai alfarma Sarkin Musulmi na Nigeria, Sa'ad Abubakar ta sanar da cewa an ga jinjirin watan Ramadan.

"Saboda haka muna sanar da Musulmin Nigeria cewa gobe Talata 13 ga watan April 2021 shine 1 ga watab Ramadan 1442 kowa ya tashi da Azumi"

Assalam yan uwa na bude sabuwar channel mai suna HAMID TECH TV don Allah kuyi mani subscribe don nuna goyon baya nagode
11/04/2021

Assalam yan uwa na bude sabuwar channel mai suna HAMID TECH TV don Allah kuyi mani subscribe don nuna goyon baya nagode

Muna kalubalantar Gwamna Tambuwal daya fito mana da sunayen matasa 10 kacal na kwarai daya taimaki rayuwar s**a ci gaba ...
11/04/2021

Muna kalubalantar Gwamna Tambuwal daya fito mana da sunayen matasa 10 kacal na kwarai daya taimaki rayuwar s**a ci gaba a yau~ Ibrahim Adam Kwankwasiyyya

'Yan Kwankwasiyya sun nemi Gwamna Tambuwal daya fito misu da sunayen matasa 10 kacal daya taimaki rayuwarsu s**a ci gaba a yau, a zamansa tsohon dan majalisar tarayya tsawon shekara 8, a zamansa tsohon Speaker tsawon shekara 4, a zamansa Gwamna mai ci tsawon shekara 6.

A cikin karamar hukumar Kwanbotso kadai Kwankwaso ya taimaki rayuwar matasa fiye da 40, kuma gasu k**ar haka;

1; Mansur Hassan MSc in Jordan (PhD IN VIEW Malaysia) working with Northwest University.

2. Rabiu Yunus MSc Malaysia working with Kano State University of Science and Technology.

3. Yusuf Shehu MSc Turkey working with Kano State University of Science and Technology.

4. Faruk M Aliyu MSc Turkey working with Federal University Kebbi.

5. Aliyu Isa Aliyu MSc Jordan PhD Turkey working with Federal University Dutse.

6. Munzali Musa MSc Turkey (PhD in view China) Working P***C Wudil.

7. Laja MSc India working with ABU Zaria

8. Engr. Salisu Isah MSc Turkey, Air Traffic Controller posted to Abuja Airport.

9. Shaibu Jafar MSc India working with CAS Tudun Wada.

10. Engr. Bashir MSc India working in one Federal Agency

12. Abdulrazaq Bature Pilot Jordan working with Dala orthopedic due to gov negligence.

13. Bello Coach MSc India (PhD in view Pakistan)

14. Dan Ali Pilot Jordan
15. Anas Habib BSc Biotechnology Bells University.

16. Engr Sadiq ibrahim MSC india working with National Space research and development agency.

17. Engr Yusuf Haruna MSC India working with national trade and investment.

18. Shamsu Haruna MSC Ukraine later transfer to India working with Abu Teaching hospital.

19. Engr Ahmad Sabo MSc Cyprus
20. Engr Bashir Umar MSC India

21. Pharm Murtala Suraj Bsc India Msc in view UK.

22. Mustapha Ibrahim Bsc Chemistry.

23. Suleiman sabo Bsc biology.

24. Bilya Bsc Biochemistry.

25. Engr. Najib Hamisu MSC India (PhD in view India).

26. Aminu Inuwa Darma Msc India working with buk (PhD in view Buk).

27. Abdulaziz Ahmad Muhd Msc India working with Rahma Radio.

28. Umar Garba working with BUK (MSC india Phd in view Thailand).

29. Mustapha Garba Msc Jordan working with Kano State Polytechnic.

30. Engr Adamu Yau MSc turkey (PhD in view Malaysia) working with KUST My mentor

31. Abdulazeez Muhd MSC india.

32. Abba Ibrahim M.tech India PhD in view

33- Farouk Umar (Msc Malaysia-Shagari quarters).

34- Munzali MusaMsc Physics Turkey, PhD in view China

35- Abdullahi Namama Bsc IT Uganda

36- Ahmad Adamu Bello (Bsc Igbenidion

37- Farouk Musa Aliyu Msc Turkey

38- Akibu Isa Murtala Turkey

39- Ahmad A Bello Ignenidion University

40- Masud Abdulkarim Ignenidion University

41- Maryam musa Gwadabe Ignenidion University

42- Yusuf danladi Ignenidion University

43- Zarau Ibrahim Muhd (Uganda

Don haka Gwamna Tambuwal ka tsaya matsayinka, idan ba haka ba zamu ci gaba da tonawa duniya assirin kai waye.

Wallahi muna sane da cewa duk cikin Gwamnonin Arewacin Najeriya kowane Gwamna ya fi ka amfani ga jiharsa.

Kyakykyawar macce da mummunar macce duk abu daya ne, babu wani banbanci, yadda idan ka sadu da kyakykyawa zaka samu gams...
11/04/2021

Kyakykyawar macce da mummunar macce duk abu daya ne, babu wani banbanci, yadda idan ka sadu da kyakykyawa zaka samu gamsuwa hak**a marar kyau.

Don haka a maimakon neman kyakykyawar macce zai fi kyau ka nemi mai tarbiyya,mai addini.

Ra'ayin: Habiba Yusuf

Duk wanda ya kara farashin kaya lokacin azumi zan soke lasisinsa: Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Ish...
10/04/2021

Duk wanda ya kara farashin kaya lokacin azumi zan soke lasisinsa: Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Ishiyaka Rabiu, ya gargadi masu sayan kaya a kamfaninsa, da kada su kuskura su kara farashin kayan don shigowar azumin watan Ramadan. Inda yace a bara ya yi masu rangwame amma s**a tsauwala farashin kayan, don haka a bana duk wani dan kasuwa da ya yi haka to za'a soke lasisin sayar masa kaya. Muna jiran martaninku?

Arna Sun Fi Musulmi Tausayi, Inji Zee-Zee DAGA IRO MAMMAN, Mujallar FimFITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayya...
08/04/2021

Arna Sun Fi Musulmi Tausayi, Inji Zee-Zee
DAGA IRO MAMMAN, Mujallar Fim

FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya waɗanda ba Musulmi ba sun fi takwarorin su waɗanda ba Musulmi ba jinƙai.

Ta ce ta gane haka ne daga abin da ya faru a gare ta a makon jiya lokacin da ta yi barazanar za ta kashe kan ta saboda damfarar da aka yi mata ta kuɗi naira miliyan 450.

Zee-Zee ta ce lokacin da abin ya faru, yawancin Hausawa ko ‘yan Arewa Musulmi daga masu ƙaryata ta sai masu zagin ta, amma su kuwa ‘yan Kudu waɗanda ba Musulmi ba, waɗanda ta kira “arna”, su ne masu tausaya mata da jajanta mata.

Daga nan ta yi tir da waɗanda su ka zage ta ko su ka ƙaryata ta a kan wannan lamari.

A makon jiya ne dai jarumar ta Kannywood ta bayyana cewa wani Inyamiri ya zambace ta zunzurutun kuɗi har naira miliyan 450, kuma faruwar hakan ya sanya ta yanke hukuncin gara ma ta kashe kan ta ta huta.

Labarin da ta bayar da muguwar shawarar da ta yanke wa kan ta sun jawo ce-ce-ku-ce sosai a soshiyal midiya.

A sabon saƙon da ta tura ɗazu domin yi wa masu tausaya mata godiya, Zee-Zee ta ce: “Salam ‘to Nigerians’, ina son ku ban dama in gode muku a bisa jaje da ku ka min ta hanyar kira na a waya da aiko min da ‘text’ dangane da damfara na da aka yi na kuɗi masu yawa naira ‘million’ ɗari huɗu da hamsin a kan wani ‘business’ da za mu yi na saye da sayarwa na ƊANYEN MAI da wani Inyamuri da ke Lagos.

“Ya damfare ni a kan ‘business’ da za mu yi da shi, amma maƙiya na saboda jahilci da hassada sai su ke cewa ba wani damfara na da aka yi, ƙarya ne. To Aljanna za a sa ni a ciki ko ko zunubai na za a yafe min da zan yi ƙarya in ce an damfare ni bayan kuma ba a damfare ni ba?

“To ya k**ata mu Hausawa mu koyi son junan mu domin duk Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne.

“Da aka damfare ni, akwai wani ‘page’ mai suna , su ma sun yi ‘posting’ damfara na da aka yi, amma wallahi da na shiga ‘page’ ɗin ban ga ana zagi na ba, sai addu’a kawai da ake min da kuma ban haƙuri a kan damfara na da aka yi. Wasu ma ‘direct’ su ka dinga kira na su na jajanta min.

“Kuma fa shi mai ‘page’ ɗin instablog9ja ɗin wallahi da shi da ‘followers’ ɗin nasa duk yawanci arna ne ‘yan Kudu.

“Amma a nan Arewa kuma duk wani ‘page’ da aka yi ‘posting’ damfara na da aka yi to zagi na kawai ake yi. Abin ya ban haushi.

“Ba zagi na da aka yi ba ne ya ban haushi; abin da ya ban haushi shi ne a ce ina Musulma ƙaddara ya same ni amma sai arna ne wanda addinin mu ba ɗaya ba su ne za su nuna alhinin su a kan damfara na da aka yi?

“Sai yanzu na fahimci arnan Nijeriya wallahi sun fi Musulman Nijeriya tausayi. Don haka Allah wadaran Musulmai masu irin wannan mummunar zuciyar!”

Zee-Zee ta miƙa godiyar ta ga ƙanwar ta, Hasina Ɗan-chaina, “da ta zo Kano ta taka min birki ta hana ni aikata SU***DE da na ce zan yi.”

Tsohuwar jarumar ta faɗi dalilai uku da su ka sa ta ƙudiri aniyar kashe kan ta ɗin. Ta ce: “Tabbas, na so na kashe kai na ɗin domin abu 3 su na damu na. Na 1, mutuwan baba na; na 2, ina son wani namiji da ya mutu; na 3, damfaran da aka min.”

Bugu da ƙari, ta gode wa wasu da ta kira “manyan mutane iyayen gida na da su ka dinga aiko min kuɗi ta ‘account number’ na domin in rage asaran damfaran da aka min.”

Daga nan ta yi tuba ga Allah kan muguwar niyyar da ta ɗaura.

Ta ce, “Sai magana ta ƙarshe kuma, ina tuba ga Allah dangane da kai na da na ce zan kashe. Astagfirillah ya Allah!”

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito cewa a cikin ‘yan watannin nan Zee-Zee ta riƙa wallafa hotunan shahararren mawaƙin nan Michael Jackson a kai a kai, tare da kalamai masu bayyana shauƙin so game da shi.

Akwai yiwuwar kila shi ne namijin da ya mutu wanda ta kamu da ciwon son shi, kuma da ta haɗa da rasuwar baban ta da damfarar da ta ce an mata sai abin ya haifar da tunanin ɗaukar ran ta shi ne mafita daga ƙuncin da ruhin ta ke ciki.

Zamu Kawo Karshen Aliko Dangote tunda   Ya kare - IPOBDangote Yana Siyar da Siminti Kan Naira 1,150 A Kasar Zambiya.Dang...
08/04/2021

Zamu Kawo Karshen Aliko Dangote tunda Ya kare - IPOB

Dangote Yana Siyar da Siminti Kan Naira 1,150 A Kasar Zambiya.

Dangote yana sayar da siminti a kan Kwatcha 55 (Naira 1150) a Zambiya. Amma a Najeriya, siminti daya yake tafiya akan naira 3,000 zuwa 5,000. Dangote shine babbar matsalar Najeriya.

Ban taɓa ganin irin wannan mummunan zalumci ba a rayuwata. ya kare Lokaci yayi da zamu kawo KARSHEN DANGOTE - Cewar Masu Rajin kafa Biafara.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Ministan Noma Sabo Nanono Ya Angonce Da Amaryar Sa Rakiya Mai Shekaru 18.Daga Aliyu Adamu TsigaMinistan aikin gona mai s...
08/04/2021

Ministan Noma Sabo Nanono Ya Angonce Da Amaryar Sa Rakiya Mai Shekaru 18.

Daga Aliyu Adamu Tsiga

Ministan aikin gona mai shekaru 74 Nanono ya auri mai shekaru 18 a cikin sirri.

Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono, ya auri yarinya 'yar shekaru 18 da ta bar makaranta a cikin wani bikin sirri. Mista Nanono, mai shekara 74, ya daura auren tare da kyakkyawar matar a wani bikin sirrin da ya samu halartar wakilai uku na ango da ke garin Jere na jihar Kaduna.

Ministan ya sanya mutane uku ne kawai kuma ya gargade su game da bayyana dalla-dalla game da auren ga mutane, ”in ji wata majiya daga dangin da ta fi son a sakaya sunanta.

Don Allah kuyi mani subscribe wannan channel mai suna HAMID TECH TV
07/04/2021

Don Allah kuyi mani subscribe wannan channel mai suna HAMID TECH TV

Assalamu akaikum yan'uwa muna maku Barka da ziyartar wannan channel ta HAMID TECH TV 📺 kudanna muna subscribe da kwaraurawar domin samun sabbin Darussanmu m...

Address


Telephone

08167515363

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al Hamid TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share