23/02/2023
Ga wata dama ta samu.
Akwai Jami'ar da Gwamnatin tarayya ta turo jihar Katsina (Federal University Of Health Sciences) da ta ke reto a saman iska wato ba a kai ga samar mata da matsugunni ba. Wadda har an fara ba da appointments na operational staff, k**ar yadda za ku iya gani a takardar da ke kasa.
Zaben wajen aje ita wannan Jami'ar yanzu hurumi ne na gwamnatin jihar Katsina.
A wannan gabar, ya zama wajibi ga shugabannin mu, tun daga kan Yan majalisu, Sanata, Hon Muhammad D Muntari Dan majalisar Tarayya, Dan majalisar jiha, Hon Abubakar Muhammed Shugabancin Karamar hukuma, Sarkin Maska da yan majalisar sa, Malamai, limamai, Yan siyasa, Yan boko, Yan kasuwa, da dukkan wani mai kishin garin Funtua da ya yi iya kokarin sa, a kuma hada hannu waje guda don ganin an kawo wannan Jami'a garin Funtua domin a mahanga ta adalci da cancanta, babu inda ya fi nan din dacewa a wannan gaba.
Allah ya tabbatar mana da wannan alkhairi.
Wannan kira ne daga:
Kungiyar (FUNTUA PATRIOTIC FRONT)