20/10/2023
TARIHIN TA’ADDANCIN ISRA’ILA AKAN ASIBITOCIN DA CIBIYOYIN FARAREN HULA. 20/10/2023
Ibrahim Alkatibi Daurawa
'The Evil is one and only means to attain the end. Therefore, We must not stop at bribery, deceit, and treachery when they should Serve toward the attainmment of our end.
In Politics one must know how to seize the Property of others without hestation if by it we secure the Submission and Sovereinghty. it is enough for them to know that we are mercilees for all disobedient to cease'-- Protocol of the Learned Elders of Zion.
Harin akan Asibitin Baptist a Gaza da Sojojin Isra’ila s**a kai akan fararen hula Majinyata Mata da Kananan Yara da Tsofaffi da sauran wadanda s**a samu munanan raunika a sakamakon hare-haren ta’addanci da Isra’ila take kaiwa akan Gidaje da Masana’antun Falasdinawa ba kakakkautawa. Abin da ya yi sanadiyar Mutuwar Mutane sama da dari biyar nan take.
Duniya ta girgiza da ganin sassan Mutane a warwatse hannuwa da Kafafuwa da sauran curi-curen bangarorin Jikin Mutane sun kaca-kaca, lamarin ya firgila Mutane a fadin Duniya, abin da ya jawo Zanga Zanga,Gangami da tarurrukan Allah wadai da Isra’ila. Mutane sun matukar fusata wasu, su yi kiran dole a dakatar da wannan Yakin na zalunci da rashin Imani da nuna tsantsar kekashewar Zukatan Yahudawan Sahyona akan Falasdinawan Gaza.
Isra’ila ta harin a asibitin ne bayan kai harin ramuwar gayya da Hamas ta yi a 07/10/23, a ranar cikar Shekaru 50, da Kasashen Larabawa s**a kaiwa Isra’ila harin ba zato, wanda tayi nasarar akansu a cikin kwanaki shida. Wato a Yakin da ake kiransa da Yakin kwana shida. Isra’ila ta yi amfani da wannan Harin da Hamas ta kai mata shi ta kaddamar da Farfaganda akan Hamas, sun sharara Karerayi don su boye gazarwarsu sun nuna Hamas a matsayin yan ta’adda masu Kisan Kananan Yara da Mata. Sun yi nasarar da farko na juya tausayawar Mutane zuwa garesu da Mayar da Hamas Azzalumai yan ta’adda duk da babu Shedai ko Hujjar abin da suke zargin Hamas da aikatawa na fille kawunan Jararai