Yobe A Yau

Yobe A Yau Wannan Shafi Dai Zai Kasance Wajen Kawo Muku Abubuwan Da Suke Gudana Kai Tsaye A Jihar Yobe.
(1)

28/12/2023

Har Yanzu Jam'iyyun Basu Ayyana Ƴan Takararsu Ba.

GUDAJI KAZAURE!Idan za'a iya tunawa, ƙasa da shekara ɗaya Hon Gudaji Kazaure, ya ce " tsohon Gwamnan babban Bankin Najer...
24/12/2023

GUDAJI KAZAURE!

Idan za'a iya tunawa, ƙasa da shekara ɗaya Hon Gudaji Kazaure, ya ce " tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya CBN, (Godwin Emeifele) yafi Gwamnatin Najeriya arziki.

A wancan lokacin, wasu da s**a ɗauki kansu 'Masana' s**ayi ta ƙaryata shi, wasu nayi mishi ba'a, wasu kuma s**a ɗauke shi ɗan wasan kwaikwayo.

Yanzu da shugaba Tinubu ya naɗa me bincike na musammam (Jim Obaze) yayi bincike akan irin badaƙalar da Emeifele yayi, ƙarshe dai Gaskiya ta fara bayyana.

Domin binciken da Jim Obaze yayi a ɗan kankani lokaci, ya gano wasu kuɗaɗe da Godwin Emeifele ya ajiye a wasu Bankunan dake UK, US da China su 593.

A UK kaɗai, an samu wani asusun da Emeifele ya ajiye kuɗaɗen da s**a haura Naira 6,226,817,019,71.64.

Wannan fa ɗaya ne daga asusu 593 da me binciken ya gano a ƙasashen UK, US da China.

NUJ YOBE COUNCIL JOINS COUNTERPARTS IN CELEBRATING THE 2023 WORLD PRESS FREEDOM DAY.The Nigeria Union of Journalists NUJ...
03/05/2023

NUJ YOBE COUNCIL JOINS COUNTERPARTS IN CELEBRATING THE 2023 WORLD PRESS FREEDOM DAY.

The Nigeria Union of Journalists NUJ Yobe Council today joined it's counterpart globally to celebrate the 2023 World Press Freedom Day which was proclaimed by the UN General Assembly in December 1993, following the recommendation of UNESCO's General Conference.

Since then, 3 May, the anniversary of the Declaration of Windhoek is celebrated worldwide as World Press Freedom Day.

After 30 years, the historic connection made between the freedom to seek, impart and receive information and the public good remains as relevant as it was at the time of its signing. Special commemorations of the 30th anniversary are planned to take place during World Press Freedom Day International Conference.

May 3 acts as a reminder to governments of the need to respect their commitment to press freedom. It is also a day of reflection among media professionals about issues of press freedom and professional ethics. It is an opportunity to:

celebrate the fundamental principles of press freedom;
assess the state of press freedom throughout the world;
defend the media from attacks on their independence;
and pay tribute to journalists who have lost their lives in the line of duty.

We commend our members for their hardwork, resilience and dedication to duty in informing, educating and entertaining the people.

We will continue to support in ensuring credible information dissemination as well as protecting our members.

Signed:
Comrade Rajab Mohammed
Chairman NUJ Yobe Council

25/04/2023
This is to Congratulate The Yobe State First Lady, Haj. Hafsat Kollere Buni for the massive victory of Her Husband Hon. ...
21/03/2023

This is to Congratulate The Yobe State First Lady, Haj. Hafsat Kollere Buni for the massive victory of Her Husband Hon. Mai Mala Buni, from the recent Gubernatorial Election.

Once Again Congratulations Yobe First Lady.

PRESS RELEASE. Gov. Buni Sues for Peaceful ElectionYobe state Governor, Hon. Mai Mala Buni CON, has advised the people o...
22/02/2023

PRESS RELEASE.

Gov. Buni Sues for Peaceful Election

Yobe state Governor, Hon. Mai Mala Buni CON, has advised the people of the state to conduct themselves peacefully before, during and after the elections.

The governor said, "Yobe state has a tradition of peaceful elections, this should be sustained to promote peace in the state.

Governor Buni said there is no election that is worth the blood of any citizen, while democracy and good governance can only thrive when there is peace and peaceful coexistence.

According to the governor, political differences must never cause hate and chaos among the good people of the state "We remain brothers and sisters in spite of our political differences.

"These differences should not be used to divide us, we should therefore play the game peacefully according to rules" Governor Buni advised.

He said as a state recovering from protracted security challenge, the citizens have a responsibility to promote peace and security across the state.

The governor urged politicians and political parties, opinion leaders, traditional rulers and parents to caution their wards and youth to shun violence and thuggery before, during and after the elections.

He directed security operatives to watch out for black spots for a proactive approach.

Governor Buni said the law will take its full wrath on all election offenders, persons or groups who go against the laws.

"I also call on our religious leaders and everyone to pray for a peaceful and successful election in our State and Nigeria generally" Governor Buni said.

Signed
Mamman Mohammed,
DG, Press and Media Affairs.

10/01/2023
09/01/2023
30/12/2022

APC Constitute State Campaign Council.

06/04/2022

Sabuwar Tafiya Ta Matasa Ƙarƙashin Gwamna Buni.

27/08/2021

YAU JIHAR YOBE TA CIKA SHEKARU 30 DA KAFUWA. MAIYE RA'AYOYINKU?. ANA IYA CEWA KWALLIYA TA BIYA KUDIN SABULU?

13/06/2020

Ustaz Mallam Babagana Kyari.

His Excellency the Executive Governor of Yobe State Hon. Maimala Buni.Yayi Kira ga Dukkan Imaman Juma'a na faɗin Jihar d...
12/06/2020

His Excellency the Executive Governor of Yobe State Hon. Maimala Buni.

Yayi Kira ga Dukkan Imaman Juma'a na faɗin Jihar da sauran Al-Umma Musulmai da su gudanar da addu'o'i na musamman. A dukkannin Masallatan Juma'a na fadin Jihar da Makarantu da Tsangayoyi baki daya.

A maimakon Kade-kade da raye-raye, da sauransu, don bikin zagayowar Ranan Demokraɗiyya "DOMOCRACY DAY".

Mai girma Gov. yace "Yau mu Najeriya babu abinda muke bukata k**ar Addu'ar Zaman lafiya da Kwanciyar Hankali, Idan mukayi la'akari da irin Halin da Al-ummarmu suke ciki, da kuma irin Halin tausayi da Alhini wajen Rasa Rayuka da Zubarda Jinni da Salwantar Dukiyoyi da Annoba iri-iri da Talauci da Rashin tabbacin Rayuwar.

Mai girma Gwamnan ya ƙara da cewa "Mu dubi irin abinda yake faruwa a jihohin Borno,Yobe, Taraba, Sokoto, Katsina, Zamfar, Kaduna da Nigerian kanta. Toh a irin wannan Hali babu wata Mafita ko Hanyar Tsira sai Addu'a,
da Tuba don komawa ga Allah (SWT) k**ar yadda ya umurcemu mu Koma Gareshi don shine mai yaye mana irin wannan Halin da muke ciki".
Allah SWT ya amsa mana Addu'o'in mu ya share mana Hawayen mu. Amin.!!!

Sakon HE Governor M.M.Buni daga Offishin Special Adviser on Religious Affairs to His Excellency Governor of Yobe,Ustaz B.G Kyari.

GWAMNA MAI MALA BUNI YA KIRAYI AL'UMMA DA SU YIWA JIHA DA KASA ADDUA A YAU RANAR DEMOCRADIYA Mai Girma Gwamna Mai Mala B...
12/06/2020

GWAMNA MAI MALA BUNI YA KIRAYI AL'UMMA DA SU YIWA JIHA DA KASA ADDUA A YAU RANAR DEMOCRADIYA

Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni, yayi wa jama'ar Yobe da Nigeria fatar alkhairi da wannan rana ta democradiya a Nijeriya.

Gwamna ya kuma kirayi al'umma da su yiwa jiha da kasa addua a Masallatai da Mujami'u na karin samun zaman lafiya, cigaba da wadata.

Gwamna Buni yace tabbas abin yabawa ne da samun cigaba da aka yi a jihar Yobe karkashin gwamnatoci daban- daban indan aka lura da shekarun da aka kwashe karkashin mulkin democradiya.

Ya kuma ce yanzu an sami lokaci da kasar Nijeriya ta samu zama karkashin mulkin democradiya mai tsawon lokaci saboda haka abin godiya ne kuma wajibine al'umma su dukufa wajen karfafa mulkin democradiya.

"Al'umma a karkashin democradiya suna da daman fadin albarkacin bakinsu kuma ana damawa dasu a mulki ta wajan wakilansu a jiha ko kasa.

" Gwamnatinmu zata cigaba da karfafa democradiya, gasa a siyasa mai tsabta, tsare dokoki da kuma baiwa kowa hakinsa" inji Gwamna Mai Mala Buni.

Ya ja hankalin al'umma su zama masu bin doka, karfafa zaman lafiya da lura da sa ido akan abubuwan da zasu iya kawo rashin zaman lafiya domin magancewa cikin lokaci.

Gwamna Buni yace, yana da yakini cewar duk da halin da Nijeriya ta sami kanta ciki a yanzu, kasar zata fito lafiya da karin zaman lafiya da kuma tattalin arziki mai karfi Insha Allahu.

Ya godewa dukkan mutanen jihar Yobe da irin goyon baya da ake baiwa gwamnatinshi da tabbacin cewar gwamnati zata cigaba da kokarin ingata rayuwar al'ummar jiha baki daya.

Daga
Mamman Mohammed
DG Press and Media Affairs na Mai Girma Gwamna.

30/05/2020
Godiya Ta Musamman Ga Gwamnan Jihar Yobe, A Gaskiya Saƙonka yana Isa Ga Talakawa Kao Tsaye. Al'ummar Bade, Yusufari da K...
20/05/2020

Godiya Ta Musamman Ga Gwamnan Jihar Yobe, A Gaskiya Saƙonka yana Isa Ga Talakawa Kao Tsaye.
Al'ummar Bade, Yusufari da Karasuwa sun yabawa salon mulkin ka. Fatan Mu Shine Allah Yayi Maka Jagora.

Jinjina ta musamman ga haziƙin matashi Dr. Ali Ibrahim Abbas, me tinkahon ganin an taimakawa Talakawa, Jagoran Matasa Na Gwamna Buni ikon Allah.

Mu ganau ne, saƙon Gwamna Buni Ya Isa Ga Duk Inda Akeso, Da Hakane Muke Godewa Gwamna Buni da ya zabi Nagartaccen Matashi Ya Bashi Wannan Matsayi. Dr. Ali Abbas Talawaka Sunce A Yaba Maka.

18/05/2020

Za'ayi Sallar Eid_El-Fitr A Jahar Yobe. Insha Allah.

His Excellency the Executive Governor of Yobe State Hon. Mai Mala Buni has approved the appointment of IBRAHIM MAMMAN as...
13/05/2020

His Excellency the Executive Governor of Yobe State Hon. Mai Mala Buni has approved the appointment of IBRAHIM MAMMAN as Director of Protocol, Government House.
The appointment takes immediate effect.

13/05/2020

SAKON TAYA MURNA

A madadin Gwamnati da al'ummar jihar Yobe, ina taya Prof. Ibrahim Gambari, murnar nadin shi a matsayin sabon Shugaban ma'aikatan fadar Shugaban kasa.

Prof. Gambari Kwararen jami'in diplomaciya kuma gogegen malamin Jami'a ne wadda yayiwa kasa hidima a fanoni daban daban.

Ina da yakinin Cewar zaiyi anfani da kwarewarsa wajen taimakawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Muna adduar Allah Ya bashi basira, lafiya da kariya wajen cima burin aikin shi.

Muna kuma taya Shugaba Buhari murnar samun Kwararen ma'aikaici wadda zai daffawa gwamnatin shi.

A madadin ni kaina, gwamnati da al'ummar jihar Yobe, muna maka fatan Allah Ya shige maka gaba, a gama lafiya, Amin.

Sa Hanu
Mai Girma
Hon. Mai Mala Buni
(Ciroman Gujba)
Gwamnan
Jihar Yobe

Ta'aziyaA yau Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni , yayi ta'aziyar rasuwar tsohon Gwamnan tsohon jihar Borno Marigayi Alh. Mo...
03/05/2020

Ta'aziya

A yau Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni , yayi ta'aziyar rasuwar tsohon Gwamnan tsohon jihar Borno Marigayi Alh. Mohammed Goni da Marigayi Shehun Bama Alh. Kyari Umar El-kanemi.

Gwamna Buni yace rasuwar wayanan shugabanin baban rashi ne wa jama'an Borno da Yobe.

Gwamna ya jajantawa iyalan marigayun, gwamnati da jamaar jihar Borno.

Daga
Mamman Mohammed
DG Press and Media Affairs

02/05/2020

Deeply Touched My Heart.

GWAMNA MAI MALA BUNI YA GANA DA SHUGABA BUHARIMai Girma Gwamna Mai Mala Buni  ya gana yau Alhamis da Shugaba Muhammadu B...
30/04/2020

GWAMNA MAI MALA BUNI YA GANA DA SHUGABA BUHARI

Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni ya gana yau Alhamis da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa dake Abuja.

Gwamna ya nemi ganawar ne domin jadada harkar tsaro a duk fadin jihar Yobe.

Mai Girma Gwamna yace hakan ya zama tilas ganin cewa ana daf da damina lokacin da jama'a zasu soma harkar noma.

Gwamna Buni ya nemi alfarma da Shugaba Buhari ya umurci dakarun tsaro da su cigaba da himma wajen tabatar da zaman lafiya domin jama'a su sami walwalar aikin gona.

Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa a shirye take domin hada kai da jamian tsaro a koda yaushe.

Shugaba Buhari ya bada tabacin cewar Jami'an tsaro zasu cigaba da kare lafiyar mutanen jihar dama ko ina a Nijeriya.

Ya bukaci gwamnatocin da jama'a dasu hada kai a yakar ta"adanci a Nijeriya.

Mamman Mohammed
DG Press na Mai Girma Gwamna.

Watarana ina cikin zama na, sai nayi tunanin cewa mu matasa mune ƙashin bayan kowacce ƙasa. Cikin ikon Allah kuma sai ka...
25/04/2020

Watarana ina cikin zama na, sai nayi tunanin cewa mu matasa mune ƙashin bayan kowacce ƙasa. Cikin ikon Allah kuma sai kaga ragamar tafiyar da ƙasar ma ta shigo hannun mu.

Daga nan ne fa tunani na ya fara canzawa, domin tayaya zamuja ragamar ƙasar alhalin bamu aza irin tubalin da ya dace mu aza ba.

Sai naje wajen magabata, nayi musu shimfiɗar abin da na zayyano a sama, nace dasu shawara nake nema game da yadda tunani na zai zamo gaskiya.

Sai s**a bani shawarar;

1. Naje nayi karatu.
2. Na kasance me girmama manya.
3. Kada na kasance me hargaga.
4. Na kasance me hakuri.
5. Kada na kasance me girman kai.
6. Na kasance me ladabi da biyayya.
7. Na kasance me kawaici da juriya
8. Idan zanyi magana na tauna ta.
9. Na guji yin kage akan abinda bani da sani akai.
10. Idan an fadi magana kuma nayi bincike, domin gudun yaɗa ƙarya.

Nan take na amshi wannan shawarwari. Godiya ta musamman ga wanna dattijai da s**a bani wannan shawarwari k**ar su; Mal. Abdullah Bego, Mamman Mohammed da Dr. Ali Ibrahim Abbas domin a kullum suna ce mun ka kasance me ladabi da biyayya, kada kayi rashin ɗa'a, kayi gaskiya, idan kuma wasu suna suki burutsu, kada kayi raddi akan suki-burutsun su.

Daga nan na gane cewa shi me ilimi komai nasa idan yanayi, to akwai hikima. Mohammed Baba Aji Allah Yayi maka jagora, tafiyar da shugabancin ka cikin ilimi yana isar da saƙo.

23/04/2020

SANARWA

Ana sanar da jama'a da suyi watsi da wani Facebook account na bogi me dauke da sunan Mai Girma Gwamna Jihar Yobe Mai Mala Buni da ke neman mutane su tura lambar asusun su na banki da kuma lambar waya.

Babu wani abu mai k**a da haka kuma ana bin didigin wadda ke bayan wannan account na bogi.
Mun gode.

Daga
Mamman Mohammed
DG Press na Mai Girma Gwamna

Mai girma Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) a yau yayi wa mataimakinsa Hon. Idi Barde Gubana (Wazir...
16/04/2020

Mai girma Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) a yau yayi wa mataimakinsa Hon. Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ta'aziyar rasuwar yayansa Alhaji Abdulkadir Barde Gubana wadda Allah Ya yi masa rasuwa a jiya kuma aka yi jana'izarsa yau.

Mai girma Gwamna yayi addu'ar Allah Ya gafartawa marigayi, Ya kuma bawa iyalansa juriyar rashi da akayi musu. Allah gafarta mishi da rahama, amin.

A ranar Lahadi Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni ya karbi baƙoncin Jami'in bankin duniya. Sun tattauna muhimman abubuwa da ...
22/03/2020

A ranar Lahadi Mai Girma Gwamna Mai Mala Buni ya karbi baƙoncin Jami'in bankin duniya. Sun tattauna muhimman abubuwa da dama da s**a shafi jihar Yobe.

Gaba dai Gaba dai Yobe: Mai girma Gwamna Mai Mala Buni da Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan sun gana da Shug...
20/03/2020

Gaba dai Gaba dai Yobe: Mai girma Gwamna Mai Mala Buni da Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan sun gana da Shugaban Buhari a yau Alhamis.

Mamman Mohammed
DGPA YBGH.

Address

Yakubu Gowon Street
Maitama Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yobe A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Videos
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share