Muhammed Yunusa Malinta

Muhammed Yunusa Malinta Muhammed Alhaji Yunusa Malinta

09/01/2024
MATASA NASON ZAMA Y'AN DABAR SIYASA. Y'AN SIYASA BASU K'AUNAR ZAMA DA MATSA MASU ILMI.A wannan Lokaci ko yanayin da muke...
10/22/2023

MATASA NASON ZAMA Y'AN DABAR SIYASA. Y'AN SIYASA BASU K'AUNAR ZAMA DA MATSA MASU ILMI.

A wannan Lokaci ko yanayin da muke ciki mafiya yawa daga cikin y'an siyasar mu na Arewacin Nigeria sunfi son y'ayan talakawa su kasance marasa ilmi y'an dabar siyasa maimakon su kasance masu ilmi masu ƙyamatar dabar siyasa.

Hakan yasa a koda yaushe y'an siyasa kan jin tsoro da shayin duk matashin dake da ilmin zamani kuma mai harkar siyasa, domin a nasu tunanin matasa masu ilmi sun san y'ancin su sannan zasu taso suyi gogayya dasu koma su ɗara su.

Idan kayi tuba da siyasar matashi mai ilmi za kaga tasha bamban da wanda baida ilmi ko a wajen mu'amular tsakankanin gama garin al'umma da y'an siyasa. Domin duk inda mai Ilmi yake ba yadda za'ai y'an siyasa su bashi kayan maye da y'an kuɗaɗen da basu taka kara sun karya don yaci zarafin waɗanda basa jam'iyyar daya ba.

Amma y'an siyasar wannan lokacin s**an so su kasance da matasa marasa ilmi waɗanda basu san y'ancin su ba, don su maida su y'an dabar siyasa, su musu duk abun da s**a gadama a harkokin siyasa da sunan neman Ƙuri'u ko haɗin kan al'umma masu katin zaɓe ta hanyar Ƙarfa-k'arfa da zubda jinene.

Hakan yasa a duk lokacin da naji wani dan siyasa mai mutuƙar son matasa suyi karatu ko yake ɗaukar nauyin karatun su ko kuma tallafa musu a harkar karatun ina masa kallon uba na Ƙwarai kuma mai kishin k'asa na gaskiya.

Domin duk wanda ya taimakawa matasa har s**ayi karatu zahiri ya cika mutum wanda yake da burin ginuwar sabuwar al'umma mai tasowa ta kasance cikin haske da zaman lafiya da samun dauwamammen y'anci na ha abada.

Don haka mu matasa kada mu sake bambancin ra'ayin siyasa ya rabamu da duk wani dan siyasa ko dan kasuwar da suke bawa y'an uwan mu matasa ilmi a duk inda suke. Domin ba abun da dan siyasa zai baka daya wuce ilmi.

Idan mukayi magana ta gaskiya duk halin Ƙunci da matsin rayuwa da rashin ilmin da kuma cigaba da samun nakaso a cikin rayuwar talakawa duk ya samo asali ne daga rashin adalcin da shugabannin mu y'an siyasa suke mana.

Kuma basu k'aunar mu samu Ilmi, domin idan mun samu ilmi zamu waye, idan mun waye mun san ciyon kanmu tabbas zamu kawo sauyi wa al'ummar mu.

Muyi hakuri wataran zamu sha alawa Insha'allahu.

Muhammed Alhaji Yunusa Malinta
Kirikasamma, Jigawa State
22/10/20222.
✍️

Address

Malinta, OH

Telephone

+2349039233421

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammed Yunusa Malinta posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muhammed Yunusa Malinta:

Share


Other Digital creator in Malinta

Show All