30/12/2025
SPONSORED...
CBN ya gargaɗi ’yan Najeriya kan guje wa wulaƙanta naira a lokacin shagulgulan karshen shekara.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gargaɗi ga ’yan ƙasa da su guji duk wani aiki da zai haifar da wulaƙanta takardar kuɗin Naira, musamman a wannan lokaci na shagulgulan ƙarshen shekara.
CBN ya bayyana hakan ne yayin da ake shirin bukukuwa daban-daban da s**a haɗa da aure, suna, bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, inda wasu ke amfani da kuɗin Naira ta hanyoyin da s**a saɓa wa doka, k**ar jefawa, taka wa, yaga wa ko yayyafa kuɗi a fili.
Bankin ya jaddada cewa Naira alama ce ta martabar ƙasa, kuma duk wanda ya wulaƙanta ta yana keta dokokin kuɗi na Nijeriya.
CBN ya tunatar da jama’a cewa dokar ƙasa ta haramta duk wani abu da zai lalata ko rage mutuncin takardar kuɗi.
Haka kuma, CBN ya yi kira ga shugabannin al’umma, malamai, masu shirya bukukuwa da kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan illolin wulaƙanta Naira, tare da ƙarfafa amfani da hanyoyin biyan kuɗi na zamani k**ar canja wuri ta banki (transfer) da POS.
Bankin ya ƙara da cewa hukumomin tsaro za su ɗauki mataki kan duk wanda aka samu da laifin wulaƙanta Naira, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.
A ƙarshe, CBN ya buƙaci ’yan Nijeriya da su nuna kishin ƙasa ta hanyar kare mutuncin Naira, musamman a wannan lokaci na shagulgula, domin Naira mallakin kowa ce kuma alhakin kowa ne ya kare ta.