Aminu Abdullahi Danmagina Fan's

Aminu Abdullahi Danmagina Fan's My Name is Aminu Abdullahi Danmagina, I'm one of the followers of Sheikh Ibrahim Zakzaky (H), My nic

20/10/2022

A Cikin Aljannu Akwai Musulmai Masu Kyawun Ɗabi'u Akwai Kuma Azzalumai, Kamar Yanda Yake A Cikin Mutane Musulmai

20/10/2022

Duk Mai Neman Aibun Mutune To Ya Fara Da Kansa

__Imam Ali (A.S)
Allah Ya Tsarkake Mana Zukatanmu Ya Yafe Mana Zunnubanmu

20/10/2022

Karamci Shine Fifita Mutunci A Kan Dukiya, Ƙasƙanci Shine Fifita Dukiya A Kan Mutunci.

__Imam Ali (A.S)
🌹

20/10/2022

Babu Wata Rahama Da Ta Wuce Zuwan Manzon (S), Shine Haske Mai Maganin Duhu.
Assalamu Alaikha Ya Rasulillah

💞💞❤💞💞

20/10/2022

Addini Gaba Ɗayansa Kyakkyawar Mu'amalace, Duk Wanda Ya Fika Kyakkyawar Mu'amala Ya Fika Addini.
💞👌💞

20/10/2022

Kyakyawar Fuska Zata Tsufa, Kyakyawan Jiki Zai Rushe! Amma Kyakkyawar Zuciya Bata Taɓa Tsofewa Ko Rushewa!
🌹

"Ya k**ata ya zama mu masoya Manzon Allah (S), mu nuna wa masoya ƙasa da masoya ɗawagitan ƙasa da masoya jihohi da ƙabil...
19/10/2022

"Ya k**ata ya zama mu masoya Manzon Allah (S), mu nuna wa masoya ƙasa da masoya ɗawagitan ƙasa da masoya jihohi da ƙabilu cewa, mu mun fi son Manzon Allah fiye da ƙasar. Mu nuna ma maso son ƙabila cewa mun fi son addininmu fiye da yadda suke son waɗannan. Mu nuna wa masoya ƙasa cewa mu mun fi son addininmu fiye da ƙabila ɗin.

Wannan zai nuna ashe da gaske ne abin muna so ne, wato kenan kishinmu da wannan da yadda muke bada rayukanmu. Kuma fa kar a manta babu soyayya sai da biyayya wanda kake so fima labudda kana biyayya gare shi. Saboda haka sonmu da Manzon dole ne ya zamo wato mun ɗora shi bisa sunna tasa. Abin da ya ce mana mu yi, mu yi wanda yace mu bari, wannan shi ne yake nuna ainihin gwargwadon son da muke masa"

__Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).

AL'AMARIN ADDINI IMANI NE DA SADAUKARWA “Na ga k**ar wasu mutane sun dauka addini kasuwanci ne, har ma suke ganin cewa k...
19/10/2022

AL'AMARIN ADDINI IMANI NE DA SADAUKARWA

“Na ga k**ar wasu mutane sun dauka addini kasuwanci ne, har ma suke ganin cewa kowa ma in yace a yi addini shima kasuwancin yake yi.

“Amma na san wani abu guda, wanda duk ya dube mu yace muna yin (gwagwarmaya) ne saboda kudi ko saboda ana biyanmu, sai nace masa lallai ya fi sauki kace mana mahaukata akan kace mana ana biyanmu ne. In kace mu mahaukata ne (a wajenka) ya yi daidai. Domin babu yadda za a yi ace wasu mutane ana basu kudi ne, amma suke fuskantar bindiga da rayuwarsu. To meye amfanin kudin?

“Kuma in kai baka ji a jikinka ba, ka samu wanda aka kashe ubansa ko wanda aka kashe dansa, ka tambaye shi nawa za a bashi ya yarda a kashe masa da ko uba?

“Shi ya ji a jikinsa ai. In kace masa mahaukaci ya yi daidai, mahaukaci ka san bai san abin da yake yi ba. Amma kace mutum ana bashi kudi ne, kuma ya fuskanci bindiga, wanda zahiran ba wai an baku labari bane, kun ga yadda ake bude wuta, mutanenmu na nufan inda wutan yake, za a harbi wasu, wani ya je ya kare da kirjinsa ya kare wani shi a harbe shi, kyamarori sun daddauka.

“Wanda duk yace wannan kudi ake basu suke yin wannan. Si mu ce kai nawa za a baka ka fuskanci bindiga? Wannan in dai baka gane cewa imani ne da sadaukarwa ba, sai mu ce ka yi mana shiru kawai. Domin al’amarin addini imani ne da sadaukarwa saboda Allah.”

— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a ganawarsa da yan uwa ranar Laraba 16 ga Rabi'ul Auwal 1444 (12/10/2022) a gidansa da ke Abuja.

“Darajar Wannan Wata Daure Kayi Salatin Annabi (SAWW) Hadaya Zuwa Ga Jagoranmu Da Nufin Allah Ya ƙara masa Lafiya da Nis...
19/10/2022

“Darajar Wannan Wata Daure Kayi Salatin Annabi (SAWW) Hadaya Zuwa Ga Jagoranmu Da Nufin Allah Ya ƙara masa Lafiya da Nisan Kwana.🤲🏻❤️🌹

🌷Kazo🌷Kizo🌷Kuzo🌷Muzo  Muyiwa 💞Annabi💞💯 SalatiAllahumma Salli Ala Muhammad Wa Ali MuhammadHappy Maulud
19/10/2022

🌷Kazo
🌷Kizo
🌷Kuzo
🌷Muzo

Muyiwa 💞Annabi💞💯 Salati

Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ali Muhammad

Happy Maulud

BA WANDA YACE MAKA TABBATAR DA DAULA SHINE NASARA“Nasara Itace ku dage (ku dage) har yazuwa ƙarewar ajali, babban nasara...
19/10/2022

BA WANDA YACE MAKA TABBATAR DA DAULA SHINE NASARA

“Nasara Itace ku dage (ku dage) har yazuwa ƙarewar ajali, babban nasara kenan. kar kayi musu saranda yadda k**a Allah saranda ɗinnan ka tsaya ƙyam har ajali yazo. Saboda hakane ma muke ganin waɗanda s**a wuce da shahada mu tayasu murna mukeyi su sun wuce tsab tamu akeji.”

“Saboda bamusan inda zamu ƙarataba (Mune abin ji) s**an tsaf. Muna fatan Allahu ta'ala ya banu sabati. Muna ma shahidanmu addu'a akan cewa abinda ku rayu akai, kuka bada rayukanku akai. In Sha Allahu mun muku alƙawari baza mu tashi akan wannan ba.”

“Jinanan ku baza su tafi haka kawai ba‚ jinananku su zasu shayar da wannan al'almari in Sha Allahu. Kuma munanan a tafarkinku har mu cimmu ku‚ muna addu'ar Allah ya bayyana wanda daga bayyanan sane za'a samu numfasawa kuma Allah ya tabbatar da duga duginmu.”

—Sheikh Ibraheem Zakzaky [H] wani yanki cikin Jawabinsa yayin ganawa da iyalan Shahidai, a gidansa dake Abuja ranar 03-09-2022.

ALHAMDULILLAH 🥰Cikin Hikimar Allah Batula Adamu Sani Ta Kubuta Daga Hannun Yan Kidnapping, Amman Basu Bayar Da Abokiyar ...
19/10/2022

ALHAMDULILLAH 🥰

Cikin Hikimar Allah Batula Adamu Sani Ta Kubuta Daga Hannun Yan Kidnapping, Amman Basu Bayar Da Abokiyar Zamanta Ba.

Muna Barar Addu'a 🤲

SHARRI KARE NE 6HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMIWaziri Aku Wanzami ya matsa har ya zo kusa da ƙofar shagon, ya ja...
19/10/2022

SHARRI KARE NE 6

HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI

Waziri Aku

Wanzami ya matsa har ya zo kusa da ƙofar shagon, ya ja ya tsaya. Ya tabbata idan Marini ya gan shi, zai taso ya rungume shi cikin farin ciki, ya ja hannunsa ya zaunar da shi kusa gare shi, ya girmama shi, ya yi masa hidima.

Sa'adda idanu biyu s**a afku cikin idanu biyu, Abuƙir ya yi ido huɗu da Abusir, sai ya game girar sama da ta ƙasa k**ar wanda aka aiko wa da saƙon mutuwa. Da yake an ce mai kaza aljihu ba ya jimirin as, haka kuma mai mugun hali, gani yake k**ar kowa ma haka halinsa yake, sai Marini ya yi tsammani Abusir ya zo ne domin ya kware masa baya cikin mutane, ya tambayi kuɗinsa da ya ɗauke masa, saboda haka ya daka masa tsawa, "kai lalatacce! Ka biyo ni nan ne domin ka tozarta ni? Sau nawa na yi maka kashedi da zuwa nan? Ɓarawon banza mai kunnen ƙashi!" Ya dubi bayi ya ce, "ku k**a shi."

Masu fushi da fushin wani s**a zabura s**a yi cacukwi da Abusir. Abuƙir ya miƙe daga inda yake zaune, ya ɗauki tsumagiya ya ce wa bayi su kwantar da Wanzami. Ya yi ta tsala masa tsabga ga baya, sai da ya yi masa tsumagiya ɗari. Ya kuma ce a birkice shi. Ya yi masa wasu tsabgogi ɗari ga ciki, sa'annan ya ce a sake shi.

Abuƙir ya dubi Abusir ya ce, "idan na sake ganin ka kusa ga shagona, zan kai ka gun Sarki ya sa hauni ya sare maka wuya kowa ya huta da zambarka, ɓarawon banza, lalatacce! Tafi ka ba mu wuri, Allah ya tsine maka albarka!" Abusir ya juya ya tafi yana kukan zuci bisa ga tozarta shi da abokinsa ya yi. Da mutane s**a tambayi Abuƙir, "me wannan mutum ya yi maka?"

Sai ya amsa musu da cewa, "ɓarawo ne mai sace kayan mutane. Yakan lallaɓo nan ya faki idona, idan ya ga hankalina ya ɗauku ya yi mini sata. Ya jawo mini asara mai yawa wajen biyan mutane kuɗin kayan da ya sace mini. Duk sadda na k**a shi, sai na ji tausayinsa in ƙyale shi, nakan ce a raina wataƙila talauci ne ke damunsa, nakan ja masa kunne in sake shi. Amma tunda na ga kunnen ƙashi gare shi, lallai idan na sake k**a shi in kai shi ga Sarki ya sa a kashe shi kowa ya huta." Da mutane s**a ji haka sai s**a yi ta tsine wa Wanzami, suna la'antar shi. Kun ji kaɗan daga halayen Abuƙir.

Shi kuwa Abusir sai ya koma gidan baƙi, ya shige ɗakinsa ya zauna yana jinjina wulaƙancin da Marini ya yi masa, ga kuma jikinsa na yi masa raɗaɗi saboda bulala. Can zuwa wani lokaci bayan ya ɗan sarara, sai ya sake ɗaukar zabirarsa ya nufi cikin gari wajen sana'arsa. Da ya ji jikinsa dai ya dame shi da zogi, sai ya yanke shawarar zuwa gidan wanka, ya samu ruwan ɗumi ya watsa ko ya ji 'yar dama-dama. Yana cikin tafiya sai ya haɗu da wani mutum, ya tambaye shi hanyar gidan wanka. Mutumin ya ce, "menene gidan wanka kuma?"

Abusir ya ce, "wurin da aka keɓe domin mutane su je su cire dauɗar da ke jikinsu, fatarsu ta yi wasai su ji daɗin rayuwarsu."

Mutumin ya ce, "af, ka ce hanyar rafi kake nema. Ai mu duka nan garin rafi muke zuwa mu gurje dauɗar jikinmu. Hatta Sarki idan ya yi nufin watsa ruwa can yakan je. Mu ba mu san wani abu gidan wanka ba."

Wanzami ya yi ta yawo har Allah ya gajishe shi, amma bai samu gidan wanka ba, bai kuma samu wanda ya san abin da ake kira da haka ba. Ya yi mamaki matuƙar mamaki. Ya ce a ransa gari k**ar wannan bai k**ata a ce babu gidan wanka ba. Ya tuna an taɓa gaya masa Sarkin garin wayayye ne mai son abubuwan ci gaba a garinsa. Don haka sai ya shura takalmansa ya nufi gidan Sarki.

Da zuwa ya faɗi ya ɗauki ƙasa gaban Sarki, ya gayar da shi cikin ladabi da girmamawa, sannan ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni baƙo ne, sana'ata wanzanci da kuma aikin gidan wanka. Na zagaya duka garin nan kaf ban samu gidan wanka ko ɗaya ba. Abin da na tabbata kuwa shi ne, duk garin da babu gidan wanka a cikinsa to tamkar abinci ne da babu gishiri."

Sarki ya dube shi ya ce, "menene muhimmancin gidan wankan nan da kake faɗi?"

Abusir ya nutsu ya yi ta bayyana wa Sarki alfanun gidan wanka, har sai da ya ga Sarki ya gamsu da bayaninsa sarai. Daga ƙarshe ya ce, "birni duka ba ya cika birni sai in akwai gidan wanka a cikinsa, ya Sarki."

Sarki ya yi farin ciki da zuwan Abusir, ya ce, "maraba da kai baƙo. Wallahi irin ku muke so, masu kawo mana ci gaba a gari, baƙo da gashi ai ya fi ɗan gida figagge." Ya kawo tufafi na alfarma ya ba shi. Ya ba shi ingarman doki da dukiya mai yawa. Ya kuma ba shi ƙayataccen gida cike da kayan alatu. Aka ba shi bayi biyu baƙaƙe da kuyangi huɗu da fararen bayi masu yawa. Sarki dai ya karrama shi fiye da yadda ya karrama Marini.

Washegari Sarki ya kira magina ya haɗa su da Abusir ya ce su zagaya da shi cikin gari, ya gwada musu duk inda yake so, su gina masa gidan wanka. Kada kuwa su kuskura su saɓa wa umurninsa. Haka kuwa aka yi, Abusir ya nuna wa magina wurin da yake so a yi gidan wankan. Masu gini s**a duƙufa ga aiki, Abusir na gwada musu yadda yake son ginin ya kasance. Cikin 'yan kwanaki kaɗan aka gama ginin gidan wanka wanda babu k**arsa. Aka shafe bangayen da launuka masu ɗaukar ido.

Bayan an gama komai na gini, Abusir ya je gun Sarki ya durƙusa gabansa ya ce, "Allah ya taimake ka an gama gini, yanzu kayan aiki kurum s**a rage a sanya."

Sarki ya kawo dinari dubu goma ya ba shi ya ce ya sayi duk abin da ake bukata. Abusir ya tafi kasuwa ya sayi komai da komai, ya zo ya shirya su a gidan wankan. Ya rarrataye mayafai na goge jiki a kan igiya, ga sabulu iri-iri, wasu na magani wasu masu sa ƙamahin jiki, an jejjera ko'ina. Mutanen da ke wucewa ta kan hanyar sai s**a tsaya s**a saki baki suna kallon irin kwalliya da tsarin da aka yi wa gidan wanda ba su taɓa gani ba, s**a riƙa tambayar Abusir, "menene wannan?" Abusir ya amsa musu, "gidan wanka ne." S**a yi mamaki, mamaki mai yawa.

Daga nan Abusir ya fara aiki. Ya kunna turaren wuta, ƙamshi ya gauraye ciki da wajen gidan. Ya dafa ruwan zafi, ya kuma shirya ruwan yana ɓuɓɓuga ta cikin wata babbar kwatarniya wadda mutum zai iya shiga ciki ya kwanta. Duk wanda ya ga yadda ruwan nan ke fitowa daga cikin kwatarniyar, k**ar dai yadda ruwa ke keto jikin dutse ya fito, sai abin ya ba shi sha'awa ya tsaya kurum yana kallon ikon Allah. Mutane s**a riƙa tafa hannuwa cikin mamaki, suna faɗin aikin wani sai kallo.

Abusir ya tafi ga Sarki ya samo 'yan yara ƙanana guda goma, daga cikin fararen bayi, yaran nan kuwa sai ka ce watanni don kyau. Ya koya musu yadda za su yi wa mutane hidima, da yadda za su taje musu gashin kai idan sun fito daga wanka. Daga nan ya aika mai shela cikin gari yana cewa, "ya ku bayin Allah, ku zo maza ku yi wanka a wurin da aka keɓe, wanda ake kira Gidan Wankan Sarki."

Mutane s**a yi ta tururuwa suna zuwa don yin wanka. Yaran nan s**a himmatu wajen hidimta musu. Duk wanda ya yi wanka sai su taje masa kansa k**ar yadda Abusir ya koya musu. Mutane s**a yi ta zuwa suna yin wanka, tsawon kwana uku ba a karɓi dirhami ko ɗaya daga hannun kowa ba.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, insha Allah.

Bukar Mada
19/10/2022

Ga Irin Sisters Din Da Muke Kishi Akansu Nan, Kuma Muke Kare Muradansu, Duk Halin Daza'a Shiga Muna Tare Dasu.Tayaya Zan...
18/10/2022

Ga Irin Sisters Din Da Muke Kishi Akansu Nan, Kuma Muke Kare Muradansu, Duk Halin Daza'a Shiga Muna Tare Dasu.

Tayaya Zan Iya Auren Daya Daga Cikin Ma'abota Gyale!!!, Alhalin Ga Waɗanda S**a San Kimar Hijabi.🌹

Duk Iskancin Dan Iska Saiyayi Shakkar Tunkarar Mace Acikin Wannan Suturar.

Duk Mai So Murabu Da Sisters Dinmu, To Ya Kawo Mana Wanda S**a Fisu Ko Kamarsu Mugani.

Allah Ya Karawa Rayuwarku Albarka Sisters Abin Alfaharinmu.🌹🌹🌹

Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'unDangane da halin da ake ciki na kidnapping din Sister Fatima Adamu Sani, ana da bukat...
18/10/2022

Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un

Dangane da halin da ake ciki na kidnapping din Sister Fatima Adamu Sani, ana da bukatar addu'ar 'yan uwa sosai don Allah a wannan daren, kowa yayi bakin kokari.

Sannan an samu magana dasu Sheikh Yakubu Yahayya sun bada addu'ar *Jaushan Kabeer* da *Saukar Qur'ani*

Duk da wannan lokaci ya tafi, don Allah wadanda s**a ga sakon Nan a daure a karanta Jaushan din koda daya ce da wani adadi na suratu Yaseen.

Muna addu'a Allah ya nuna karfin ikonsa akan wannan al'amari.

-Academic Forum Katsina.
😢😢😢

BABU WANI KARFI KO ZALUNCIN DA YA ISA YA RABAMU DA SHAIKH ZAKZAKY (H)"Muna tare da Malam, ba ma maganar takalmin kaza ba...
18/10/2022

BABU WANI KARFI KO ZALUNCIN DA YA ISA YA RABAMU DA SHAIKH ZAKZAKY (H)

"Muna tare da Malam, ba ma maganar takalmin kaza ba tsakaninmu da malam ba, don takalmin kaza idan an gasa kafar ana zare shi. To lahira komin bakin cikin mutum tare da Malam zai ganmu insha Allah".

Shaikh Yaqoub Yahya wajen rufe Muzaharar Free Zakzaky (H) Ranar lahadi 18th, Feb, 2018.

“In da za ka ce akwai wani mutum wanda shi ne ‘kamil’, ‘perpect’ (cikakke), to shi ne Annabi (S). Saboda duk wata ɗabi’a...
18/10/2022

“In da za ka ce akwai wani mutum wanda shi ne ‘kamil’, ‘perpect’ (cikakke), to shi ne Annabi (S). Saboda duk wata ɗabi’a kyakkyawa ya kai maƙurarta; gaskiya, riƙon amana, tausayi, taimako, murmushi da sakin fuska, sauƙin kai, ka ɗauki dukkanin kyawawan siffofi za ka ga shi yana da k**alarsu ne. Waɗannan kuma sune za mu ɗauka a matsayin abin da za mu kwaikwaya.”

—Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a ganawarsa da ba’adin ƴan uwa a gidansa da ke Abuja, a cikin munasabar Mauludin Manzon Allah Muhammad (S) 16/03/1444AH daidai da (14/10/2022 Miladiyya).

“(Shugaban ƙasa na mulkin soja), Janar Ibraheem Badamasi Babangida, ya shahara da rufe bakin Malamai da kuɗin rashawa, w...
18/10/2022

“(Shugaban ƙasa na mulkin soja), Janar Ibraheem Badamasi Babangida, ya shahara da rufe bakin Malamai da kuɗin rashawa, wata rana sai ya tura wa Shaikh Ibraheem Zakzaky Saƙon magudan kuɗi, amma sai Shaikh Zakzaky (H) ya yi musu gatse irin yadda Annabawa da Mujaddadai suke wa Ɗagutai.

Ya dubi kuɗin ya cewa wanda ya kawo saƙon; “Ai kuɗin ba su kai yadda s**a ambata ba”, wanda ya kawo saƙon jiki na rawa ya ce; “Wallahi Malam ba a taɓa komai a ciki ba”, sai Shaikh (H) ya ce; “Na duba ne ban ga Aljannar Allah a cikin abin da ka kawo ba”.

Nan take ɗan saƙo ya gane abin da Shaikh (H) ke nufi, sai ya ce; “Allah gafarta Malam, wannan kam babu”, sai Shaikh (H) ya ce; “To, a maida masa abinsa tunda babu Rahamar Allah a ciki, dama ni ita nake nema”.

Ɗan saƙo ya kwashi saƙon Ubangidansa cikin kunya da ƙasƙanci, yana tambayar kansa ashe akwai Malamin da zai ƙi kuɗi irin wannan?”.

©Ibn Muhd Alawi

HARKA BA  BAYAR DA UMARNI BANE.Duk wanda yace maka yanzu safiya ne kasan ba safiya bane, za kace, A'a... Yanzu in ba hak...
18/10/2022

HARKA BA BAYAR DA UMARNI BANE.

Duk wanda yace maka yanzu safiya ne kasan ba safiya bane, za kace, A'a... Yanzu in ba haka ba sai ka tashi kayi, haka muke addinin mu? In shugaba yace yanzun a yi Magriba sai kayi? Mu a ko mene ne yana da ka'ida, kuma ya k**ata ace kana da hankali ne.

"Duk tarbiyan da muke yi mu muna yi ma hankali ne. Muna kokari mu tarbiyantar da mutane ne akan in wani abu ya taso, me ya k**ata ka yi?

Ya zama kai ka sani ba sai an gaya maka ba. Ba Malam ya ce ba.

*"Na san na sha fadin wannan; 'Ni kullum ina tarbiyar mutane su yi tunani, amma sai wasu suna bata mana da *Malam yace. Wasu suna kokarin su tarbiyantar da mutane da cewa ana ba da umurni ne. A wani nizamin haka ne

amma namu ba haka bane Giving situation' me ya k**ata kayi?

Kana da hankali, an koyar da kai, an saka maka tunani da sanin abu da ka'idoji ba sai an koya, an ce maka kaza ba

"Hatta in aka ce maka Malam yace kaza, za ka ce karyane, saboda ba zai ce haka nan ba, tunda ya saba. Ina fadin wannan ne dangane da k**an su (Jahiliyya) tun da irin tarbiyarsu daban ne, irin namu daban ne, su kuma sun dauka namu irin nasu ne... "

— Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin da yake magana da Harisawa a lokacin bikin Nisfu Sha'aban 1436.

18/10/2022

"Ko Janar ne aka ce masa Zakzaky zai Saranda, zaice ƙarya ne".

-Sheikh Zakzaky (H)

Ko Kasan Da Wannan Shafin ???Ma'asumah Nigerian News UpdateShafin 'Ma'asumah Nigerian News Update', shafi ne wanda a sam...
18/10/2022

Ko Kasan Da Wannan Shafin ???

Ma'asumah Nigerian News Update

Shafin 'Ma'asumah Nigerian News Update', shafi ne wanda a samar dashi domin amfanuwar al'umma, ta hanyar isar da ingantattun labarai, rahotanni da mukaloli gami da sauran shirye-shiryen dasu ka shafi al'umma. Shafi ne wanda yake gudanar da ayyukanshi karkashin kulawar wasu yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) suke tafiyar da wannan Shafin. (Ba lalle bane duk abinda shafin ke wallafawa ya zamo ra'ayin Harka.

Shafin MA'ASUMAH shafi ne wanda ya tattara wakilai daga kusan dukkanin sassan wannan kasa dama wajen ta, tun daga lunguna da sakuna na birane da kauyukan Najeriya, har da ma wasu kasashen ƙetare. Inda ya tattara zakakurai kuma kwararru masana mak**ar aiki dai-dai gwargwado. Shafin yana da kyakkyawan tsari wajan gabatar da ayyuka, inda ya hada da fannoni daban-daban a ayyukansa.

Ga wasu daga cikin fannonin da shafin ke gabatar da ayyuakansa

1-KOYARWA
Shafin MA'ASUMAH shafi ne da ya yaye dalibai fiye 300 a cikin shekaru Uku, ta hanyar koyar dasu fannoni daban-daban a kafar sada zumunta (Social Media). Ta yadda za su taimakawa Harka da kuma yadda za su dogara da kansu musamman a Social Media, k**ar koyar da, Blogging, Photograpy, Applications, Vedio editing da sauran fannoni.

Sannan yayi shura wajan kawo labarai da rahotannin das**a shafi harkar musulumci da wajen harka, al'amuran yau da kullum, tunatarwa, fadakarwa, ilimantarwa, Nishadantarwa, da Wa'azantarwa.

An sanyawa shafin suna MA'ASUMAH ne domin tawasulli da neman tabarrukin Sayyada Fatima Azzahra(A.S) domin samun dacewa a cikin ayyukan shafin da samun tsira a ranar Lahira.

Ya ku al'umma, masu bibiyan wannan shafi tsawon lokaci daya gabata, Muna masu bada hakuri sak**akon jinmu da kukayi shiru na wani lokaci zuwa yanzu. Hakan ya faru ne sak**akon wasu gyare-gyare da muka yi domin inganta tsarin shafin, domin samar da ababen da zasu amfanar daku. Shafin a shirye yake domin cigaba da amfanar daku ta kowane janibi. Sannan muna neman gudummawa da taimakonku ta kowace fuska, k**ar yadda ku saba a baya, ta hanyar addu'o'inku da shawarwari da cikakkiyar gudummawarku wajan cigaban wannan shafi mai albarka.

Mun gode!

Sa hannu; C.E.O; Mas'udu Dan-Masani Shinkafi, a madadin daukacin wakilan wannan shafi mai albarka na 'Ma'asumah Nigerian News Update'.

— Ma'asumah Nig. News. Update
18/10/2022

Wannan mutum-mutumin na wasu iyalai ne da s**a zo Iran daga arewacin ƙasar Afganistan , sunyi Tattaki da ƙafarsu domin z...
17/10/2022

Wannan mutum-mutumin na wasu iyalai ne da s**a zo Iran daga arewacin ƙasar Afganistan , sunyi Tattaki da ƙafarsu domin ziyartar Imam Ali Ridha (a.s.) , tun sama da shekaru 200 da s**a gabata, a lokacin da s**a isa wannan wuri saboda sanyi da dusar ƙanƙara da nisan tafiya da s**a sha , sai Allah ya karɓi ransu a wannan wuri , kafin su karasa shiga Haramin.

Nisan wurin da s**a rasu da Haramin Imam Ridha (a s.) fiye da mita 500 daga gefen Babuɗdusi , kan titin Shirazi .
Domin dawwamar da tunawa dasu aka yi mutum mutuminsu a wurin .

Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

A DAINA KALLON WASU ANA ZARGIN WASU."Har ma wasu suna cewa Hope ɗin su duk gare mu ne (Fatan su duk gare mu ne). Masha A...
17/10/2022

A DAINA KALLON WASU ANA ZARGIN WASU.

"Har ma wasu suna cewa Hope ɗin su duk gare mu ne (Fatan su duk gare mu ne). Masha Allah wannan kyakkyawan zato ne, amma mu a ƙashin kan mu, mu muna ganin komai lafiya lau? Yawwa, mu kuma a ganin mu bamu kai yanda ya k**ata mu kai ba, saboda haka ya k**ata kowanen mu ya yi ta hanƙoro, mu yi ta hanƙoro, shine dai maganar ƙwara daya kenan. Bugawa za ayi ta tayi ne! Ai ta ƙoƙari ne! Kowane ya gwada kan sa ya dinga sa kan sa a ma'auni, ya daina kallon wasu yana zargin wasu, ya zargi kan sa yayi ƙoƙari ya ga cewa lafiya lau shi daidai gwargwado Insha Allahul azim".

– Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a cikin jawabin sa wajen rufe Mu'utamar a garin Bida shekarar 2013.

Ibrahim Almustapha Saminaka ya rubuto muku.

Da mata sun san yadda Hijabi yake musu kyau, da kun mai da shi sutura dai'man gida da waje ....Da mata sun san yadda maz...
17/10/2022

Da mata sun san yadda Hijabi yake musu kyau, da kun mai da shi sutura dai'man gida da waje ....

Da mata sun san yadda maza ke kallonsu yayin da s**a fito babu Hijabi, masu kishin kansu sai sunyi fatan ina ma ana sanya Hijabin Karfe su sa, don tseratar da mutumcin su.

Sista, wallahi summa tallahi Hijabi sutura ne, bayan cika Umarnin Allah da samun gwaggwaban lada, Shaidan da manajojinsa na shakkar wannan Hijabin naku.

Saboda sanin tasirin sa, da yadda yake makami mai karya lagon makiya, Imam Hussain (As) ya karfafi Sayyida Zainab duk bala'i kar ta rabu da Hijabi.

Duk sadda na ganku da wannan Hijabin, lalle na kanji cewar akwai Hope, ko kun san shine dalili mai karfi wajan yunkurawar Imam Khomeini yayin tunbuke Shah Pehlavi?

Shah Pehlavi yace ya haramta sanya Hijabi, Imam yace bai lamunta ba, daga wannan gabar ya fara kalubalantar Shah har ta Allah ta kasance gashi Daula ta kafu a Iran.

Yake Sista, Namijin kwarai yana son yaga abar da yake so killace a lullube cikin Hijabi, hatta mutumin banza, yana sha'awar yaga na sa cikin Hijabi, Shine mutumcinki shine kimar ki, Ko kun san Meyasa a Shi'a muka muhimmatar da bakin Hijabi?

Wataran zanyi rubutu akai Insha-Allah.

Allah ta'ala ya muku Albarka Sistotinmu, ya baku mazaje yan gwagwarmaya na gari, masu sadaukarwa.

Muhammad Bala Afuwa

KUSA-KURAI DA MUKE AIKATAWA WAJEN FURUCI KO RUBUTU AMMA BAMU DAMUWA.A ko wane yare na duniya, ana samun wata baƙuwar kal...
17/10/2022

KUSA-KURAI DA MUKE AIKATAWA WAJEN FURUCI KO RUBUTU AMMA BAMU DAMUWA.

A ko wane yare na duniya, ana samun wata baƙuwar kalma amma saboda wucewar zamani da kuma amfanin da ake da wannan kalmar a kan harsuna, wannan kalmar takan zamanto wacce ake sabawa da ita har ta zamanto wani ɓangare na wannan yaren.

Saboda yawan amfani da wannan kalmar, ta kan yaɗu a cikin ƙwaƙwale sannan ma’abota tunani ba su keɓanta da ita, sai ya zamanto kuskuren ya yaɗu a kunnuwan mai saurare da mai ji, za mu bijiro da wasu daga waɗannan kusa-kuran waɗanda suke yaɗuwa muke kuma amfani da su, mun kuma saba da su duk da ba mu san hakan kusa-kurai ba ne ba.

Akwai abubuwan da larabawa suke kira “Akɗa Sha’i’a” wanda a turance suke ce ma “Common Mistakes”, wasu kusa-kurai ne da bamu damu ba idan mun aikata su, sun zamar mana jiki. So da yawa kuskuren yana faruwa ne idan mun ari wata kalma da ba yaren mu ba. Misali k**ar: رب العالمين wajen furta wannan kalmar maimakon mutum yana nufin Ubangijin talikai, sai ma’anar ta koma Ubangijin raɗaɗi. رب الآلمين kun ga idan ya ce haka ya yi kuskure. Ire-iren waɗannan kusa-kuran bama damuwa wajen furta su ko kaɗan sun zamar mana jiki.

Akwai kalmar Ajjil عجل da wasu suke furta اجل a ya yin furuci. Kuma hakan kuskure ne. Maimakon gaggautawa kun ga ya koma jinkirtawa. Sannan akwai kalmar فَرَجَهُمْ da wasu idan sun tashi furuci suke faɗin فَرْجَهُمْ to kun ga ma’anar yadda ta canza zuwa ɗaya. Ka nufi Allah da nufin ya gaggauta bayyanar sa. Amma a lokaci guda ya yin furuci sai ka kuskure kace Allah ya jinkirta bayyanar sa.

Akwai wasu misalan ma k**ar: Labbaika Ya Rasulallah. Sai kaga wasu sun rubuta “Labbaika Ya Rasulullah” ko kuma “Labbaika Ya Rasulillah”, waɗannan duk wasu kuskure ne da muke yi wajen furuci ko rubutu, amma sam bamu damu ba. tunda Ya harafin Nida ne da ya yi nasaba ga Rasula, to kunga kenan Rasulallah zai zama ba Rasulullah ko Rasulillah ba. Akwai wani misali k**ar haka: Yaushe za mu gan ka Abush-Shuhada’i ne zai zama ba Abush-Shuhada’u ba idan kun lura. Idan Ya ta zo kafin Abu ɗin, kun ga kenan ya zama ‘Aba’ kenan, idan harafin jarra ya zo sai ya zama ‘Abi’ kenan. To idan kace Abush-Shuhada’u a ƙa’idar larabci zai zama su Shuhada ɗin basu da alaƙa da shi “Abu” ɗin, ko kuma shi “Abu” ɗin bai da alaƙa da su Shuhada ɗin. Idan misali sunan nan suna ne zaka kira Ma’alumi kuma mufrad, shi ne zai iya zama ‘Ya Rasulu’.

Akwai misalin haɗa Ma’arifa da tanwini, rashin yiwuwar haka ko kuma yiwuwar yin hakan, wajen haɗa ma’arifa da tanwin k**ar misalin:

Assalamu Alaiki Hirzina.
Salamu Alaiki Ramzina.

Tunda farko an sanya Ma'arifa a sallama, kun ga kenan idan an lura ƙasan zai zama “Salamun” ne ba “Salamu” ba. Amma ba zai yiwu a haɗa su a Jumla ɗaya ba ta wannan fuskacin idan an lura, da fatan an fahimta.

Wata rana Abu Hanifa tare da Sibawaihi, Abu hanifa ya cewa sibawaihi kun zo kuna cewa bil kaza ku tafi kuje ku karanci Ilimin fiƙihu ku san shari’a, sai sibawaihi ya cewa Abu hanifa ina zuwa yanzu kai idan aka kawo maka shari'a aka ce maka “Haza ƙatilu Ibnaka” da kuma “Haza ƙatilun ibnaka”, ya za ka yi da su.?

Sai Abu hanifa ya ce duk zan kashe su, sai sibawaihi ya cewa Abu hanifa za a kashe ka kai ma. sai ya ce “Haza ƙatilu ibnaka” idan ka kashe shi kayi daidai. Amma “Ƙatilun” ya yi shirin kashe ɗan ka idan ka kashe shi za a kashe ka. Saboda ya yi shirin kashe ɗanka ne.

Na kawo wannan labarin ne domin bayanin da nake yi ya sake fito mana fili sosai. Akwai misalai kala-kala amma ba tsawaita wa zan yi ba. Bari na rufe da wannan “Innallaha wamala’ikatahu” ake cewa, ba “Innalllaha wamala’ikatuhu ba” a lura da kyau abokai.

Imam Sadiƙ (a.s) yana cewa, za ka iya samun mutum bai iya ta’abirin sunan shi ba, amma zuciyar shi tafi ‘Misbahu’ haske. Akwai kuma wanda baya kuskuren nahawu, ma’ana baya kuskuren marfu’atu, la mansubatu, la majruratu, la maskunatu, amma kuma zuciyarshi diɗin take. To abin da muke son nunawa shi ne ba wai dole sai ka zama ‘Kamil’ ba (Perfect) a matakin kiyaye kusa-kurai, amma daidai gwargwado mutum ya yi iya iyawarshi ya kiyaye wasu kuskuren da zai iya.

Kuma hanya mafi sauƙi da za ka iya kiyaye waɗannan kusa-kuran shi ne makaranta, mu daure mu taimaki kanmu da kanmu mu tsaya mu yi karatu daidai gwargwado iyawarmu.

Wasu ta yiwu su ce naga k**ar ka kawo wasu abubuwa ne, amma baka gamsar damu ba domin mu samu tabbaci ta hanyar dalili mai ƙarfi sosai. Ko kuma dalilin daka kawo bai kai ya tabbatar mana da kuskure ake furta wa ba ko kuma idan an tashi yin rubuta ake rubuta wa ba. Sai na ce musu nan ba muhallin gyara waɗannan kusa-kuran bane. Hanya mafi sauƙin da za mu gyara waɗannan kusa-kuran shi ne mu tafi makaranta mu zauna a aji mu yi karatu. Rubutun da na yi na haskaka mana ne kawai, domin mu gane wasu abubuwan sosai.

Ayi min afuwa.

-Aba Sajjadi.

17/10/2022

Har Yanzu Wasu Suna Cewa Hope Dinsu (Fatansu) Gare Mu Ne.

-Syd Zakzaky (H)

17/10/2022

Dirka:
Ana rubuta dirka (ne ko ce) ita kaɗai ba tare da an haɗe ta da wani abu ba. Misali:

Mu ne✅ *mune❌
Shi ne ✅ *shine❌
Ita ce ✅ * itace ❌
Ke ce ✅ *kece ❌
Kai ne ✅ *kaine ❌

Idan har ka cika Bahaushe kai ma ka kawo naka misali a cikin jimla.

Hassan Sa'ad Kaura

17/10/2022

A tsari na dokokin rubutun Hausa, haramun ne nuna dogon wasali ta hanyar ruɓanya shi a rubutun Hausa na yau da kullum, Misali:

Sameera❌
Samira✔️

Haleema❌
Halima✔️

Zaenab❌
Zainab✔️

Baqeer❌
Baƙir ✔️

Zoomoo❌
Zomo✔️

Don haka kuskure ne rubuta wasu sunaye mak**antan waɗannan da ake ruɓanya wasali a cikinsu, darasin yau babu yawa, idan mun gane sai mu haɗu a kwamen tare da kawo wasu misalan. 👇

— HHassan Sa'ad KauraSHassan Sa'ad KauraKHassan Sa'ad Kaura17 October, 2022

Address

Zaria

Telephone

+2349067166776

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminu Abdullahi Danmagina Fan's posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Aminu Abdullahi Danmagina Fan's:

Videos

Share

Category


Other Media in Zaria

Show All