Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau

Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau, Media/News Company, Zaria.

Mun bude wannan shafine dan hadin kai, sada zumunci, yada kyawawan al'adunmu, Tunawa da iyayanmu da kakanninmu, se kuma kare mutuncin Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau.

***MUNYI RASHIN MAZAN JIYA***Idan kai dogon tinani sai kaga Nageriya bata kamo hanyar gyaruwaba, abinda ze nunamaka hk s...
15/01/2025

***MUNYI RASHIN MAZAN JIYA***

Idan kai dogon tinani sai kaga Nageriya bata kamo hanyar gyaruwaba, abinda ze nunamaka hk shine, mazan jiya ba naira bane ko dala a gabansu, kishin kasarne sukeyi, yanzu cin hanci yasama gindin Zama a Nageriya, an lalata tarbiyyan matasanmu, babu kasarda zataci gaba da gurbatattun matasa,

NB: Talakan Nageriya kaji tsoron Allah, kabi Allah dai-dai gwargwado, kada yazo bakaji dadi a duniyaba Kuma kaje lahira bakada rabo, muna rokon Allah ya gyara zukatanmu, Allah ya shirya shuwagabanninmu, Allah ya daidaita matasanmu da Yan matanmu Amin.

Tsokaci: Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau.
#15/01/2025.

***MAKAMA JIKAN MAKAMA***Marigayi Mai girma MAKAMA BABBAN ZAZZAU Alh. Abdullahi Kwasau, jikan Makaman Zazzau tsoho jikan...
15/01/2025

***MAKAMA JIKAN MAKAMA***

Marigayi Mai girma MAKAMA BABBAN ZAZZAU Alh. Abdullahi Kwasau, jikan Makaman Zazzau tsoho jikan Mal. Sambo Sarkin Zazzau, jikan Mal. Abdulkarimu waliyyin Allah, muna rokon Allah ya jikanku da gafara Amin.

#15/01/2025.

***RAYUWANKA ABIN SHA'AWA NE***A duk yamma uwar haka, mukan sameka a kofar daki kana zaune, azo a gaisheka, kaima Jama'a...
14/01/2025

***RAYUWANKA ABIN SHA'AWA NE***

A duk yamma uwar haka, mukan sameka a kofar daki kana zaune, azo a gaisheka, kaima Jama'a alheri, ka saurara talakawanka, Amma yau baka, ka sadu da mahaliccinka, muna rokon Allah ya karamaka rahama da gafara a makwancinka Amin.

#14/01/2025.

***SARKIN MUSULMI ABUBAKAR***Bawan Allah Mai Alfarma SARKIN MUSULMI ABUBAKAR III, Hakika anmashi shaida da gaskiya, riko...
14/01/2025

***SARKIN MUSULMI ABUBAKAR***

Bawan Allah Mai Alfarma SARKIN MUSULMI ABUBAKAR III, Hakika anmashi shaida da gaskiya, rikon Amana, yaba Addinin Musulunci gagarinin gudunmuwa, yayi rayuwa Mai albarka, yayi Sarauta sama da shekara 50, muna rokon Allah ya jikanshi da gafara Amin.

#14/01/2025.

***DAN AMINU SHAKAKIN MAZA***Marigayi Mai girma IYAN ZAZZAU Alh. Bashari Aminu OON, Iya Dan Gwamma, Iya Bijimin Saraki, ...
13/01/2025

***DAN AMINU SHAKAKIN MAZA***

Marigayi Mai girma IYAN ZAZZAU Alh. Bashari Aminu OON, Iya Dan Gwamma, Iya Bijimin Saraki, Iya ka Iya ka hana wani ya Iya, Allah ya sadamu a Fadan masoyinka Manzon Allah S.A.W Amin.

#13/01/2025.

12/01/2025

Ya Allah! Kasan munada zunubai masu yawa, Kai kadaine zaka yafemanasu, Ya Allah! Ka shafe kura-kuranmu Amin.

***KADA DAMA RUWA DAN SHEHU***
12/01/2025

***KADA DAMA RUWA DAN SHEHU***

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***Allah yayima Matar Mai Martaba Sarkin Keffi Alh. Dr. Shehu Chindo Yamusa lll rasu...
11/01/2025

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Allah yayima Matar Mai Martaba Sarkin Keffi Alh. Dr. Shehu Chindo Yamusa lll rasuwa yanzu, Za'ayi Janazanta gobe da Karfe 12pm a kofar Fadar Sarkin Keffi Nasarawa State, muna rokon Allah ya jikanta da gafara Amin.

#11/01/2025.

11/01/2025
***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***Allah yayima Alh. Bashir Babajo rasuwa, Za'ayi Jana'izansa anjima da Karfe 5:30pm...
11/01/2025

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Allah yayima Alh. Bashir Babajo rasuwa, Za'ayi Jana'izansa anjima da Karfe 5:30pm a nan Zaria, muna rokon Allah ya jikanshi da gafara Amin.

11/01/2025.

11/01/2025

Allah yayima Hajiya Jummai na gidan Sarkin Doka rasuwa, Za'ayi janazanta da Karfe 2pm a mangoron babajo Zaria Allah yasa ta huta Amin

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***Allah yayima Fatima Muhammad rasuwa, Za'ayi janazanta gobe Asabar a gidan Baban f...
10/01/2025

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Allah yayima Fatima Muhammad rasuwa, Za'ayi janazanta gobe Asabar a gidan Baban fulane kusa da makarantar Dandada dake Kwarbai Zaria, muna rokon Allah ya jikanta da gafara Amin.

#10/01/2025.

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***Allah yayima Baba Lawal rasuwa, Za'ayi Jana'izansa anjima Bayan Sallan Isha'i a G...
10/01/2025

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Allah yayima Baba Lawal rasuwa, Za'ayi Jana'izansa anjima Bayan Sallan Isha'i a Gidan Marigayi Galadiman Zazzau Tukur dake Kwarbai Zaria, Muna rokon Allah ya jikanshi da gafara Amin.

#10/01/2025.

10/01/2025

Muna maku Barka da Juma'ah, Muna rokon Allah ta'ala ya amshi ibadunmu ya jikan iyayanmu da kakanninmu Amin.

10/01/2025

Allah yayima Hajiya Azumi Mai allura rasuwa, wacce take layin barebari T/wada Zaria, Allah ya jikanta Amin.

***GIWA DA "YA"YANTA JIKAN SAMBO***Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris CFR da "ya"yansa Mata, Allah...
10/01/2025

***GIWA DA "YA"YANTA JIKAN SAMBO***

Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris CFR da "ya"yansa Mata, Allah ya jikan Zaliha, gasunan da jajayan sahunsu, Allah ya jikan dukkan Musulmi baki daya Amin.

#10/01/2025.

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***Allah yayima Hajiya Hadiza Tajo (Hajiya Umma) Shugaban Yan agajin Fitiyanu rasuwa...
09/01/2025

***INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Allah yayima Hajiya Hadiza Tajo (Hajiya Umma) Shugaban Yan agajin Fitiyanu rasuwa, Za'ayi janazanta anjima da karfe 4:30pm a Fadan Zazzau, Muna rokon Allah ya jikanta da gafara Amin.

#09/01/2025.

***WALIN ZAZZAU UMMARU DALHATU***Marigayi Mai girma WALIN ZAZZAU Mal. Ummaru Dan Sarkin Zazzau Mallam Dalhatu,Yayi zaman...
09/01/2025

***WALIN ZAZZAU UMMARU DALHATU***

Marigayi Mai girma WALIN ZAZZAU Mal. Ummaru Dan Sarkin Zazzau Mallam Dalhatu,

Yayi zamani da Sarakunan Zazzau Biyar (5) anfara nadashi Sarauta tin a zamanin mulkin Mahaifinsa yanada shekara kasa da goma (10),

Yayanshi Sarkin Zazzau Mallam Ibrahim Dan kwasau ya nadashi Sarautar Wali,

Walin Zazzau Ummaru Sirikine wurun Mai Girma Madakin Zazzau Mallam Munir Ja'afaru Kuma Aminine a wurun Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. Muhammadul Aminu CFR, WALIN ZAZZAU ya rasu a cikin shekarar 1984, Muna rokon Allah ya jikanshi da gafara Amin.

#09/01/2025.

Address

Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau:

Videos

Share