BARKA DAYAU

BARKA DAYAU Domun samun labaren duniya

SHAHARARRUN BARAYIN DUNIYA 01                        ADAM WORTH Adam Worth Babban Barawon Kasa Da Kasa , Wanda Ana Lissa...
20/05/2022

SHAHARARRUN BARAYIN DUNIYA 01
ADAM WORTH
Adam Worth Babban Barawon Kasa Da Kasa , Wanda Ana Lissafa Shi Na Farko A Shahararrun Barayin Da S**a Yi Fiche A Duniya .
Adam Worth Bayahude ne Talaka ,An Haife Shi A Kasar Germany A Sheakarar 1844 , A Shekarar 1854 Baban Adam Worth Ya Koma Da Iyalansa Kasar Amurka , Yayin Da Baban Na Worth Ya K**a Sana'ar Dinki. Adam Worth Ya Gudu Daga Wurin Iyayensa Ya Shiga Gari , Tare Da Fara Aiki A Wani Babban Shago Dake A Newyork Na Tsawon Wata Guda ( Ana Tunanin Yayi Musu Ta'adi Ne Shi ya saka Ya bar Shagon).
Adam Worth Yayi Aiki Da Sojin Hada Ka Na kasar Amurka , Yayin Da Akayi Rikichin Farar Hula , Yana Dan Shekara Sha Bakwai Lokachin , A Yaki Na Biyu Da Akayi Aka Ji Masa Chiwo , A Shekarar 30 August 1862 , Sai Ya Gudu Asibitin Georgetown Dake Washington DC , Don Neman Lafiya.
Adam Worth Ya Fara Da Yankan Aljihu A Birnin Newyork Na Kasar Amurka, Har Yakai Ga Ya Hada Dabarsa Ta Kansa Ta Yankan Aljihu, Daga Nan Fa Sai Ya Fara Fashi Da Damfara , An K**a Adam worth Yana Satar Kudin A Akwatin Ajjiye Kudi Na ADAM EXPRESS , Aka Yanke Masa Hukunchin Zaman Gidan Yari Na Shekara Uku A Gidan Yari Na SING SING , Amma Duk Da Haka Ya Samu Hanyar Daya Gudu Ya chigaba Da Sache Sachensa .
Adam Worth Yayi Fashi A Bankuna Da Dama Na Kasar Ta Amurka , Musamman Shekarun 1866 Zuwa 1869.
Ana Bayar Da labarin Chewa , Ya Taba Yiwa Ma'aikacin Banki Dabara cikin Hikima , Ya Karbe Bindigarsa Yayi Fashi Da Ita .

Daga Nan Adam Worth Da Bullard S**a Yanke Shawarar Komawa Yankin Turai Don Chi Gaba Da Sata , Haka S**a Nufi Birnin Liverpool Dake Kasar England , Bayan sun Yi Sache Sachen Su Achikin Dabara Sai Kuma S**a Koma Birnin London .

A Shekarar 1875 Adam Worth Ya Tafka Babbar Sata A Abirnin London .

Don Kada Rubutun Ya Tsawaita, A Rubutu Na Gaba Zamu Ji Karashen Labarin Adam Worth.

BARKA DAYAU

★BIRNIN LONDON KAZO NAZO ★1— London Dake Kasar England Shine Birni Na Biyu A Duniya Bayan Birnin New York Na Amurka Da Y...
20/05/2022

★BIRNIN LONDON KAZO NAZO ★

1— London Dake Kasar England Shine Birni Na Biyu A Duniya Bayan Birnin New York Na Amurka Da Yafi Yawan Yan Kazo Nazo , Wanda Asalinsu Duk Ba A London Aka Haifesu Ba, An Haifesu A Kasashe Daban Daban Ne.

2— Kididdigar Shekarar 2011 Da Akayi A birnin na London Ya Bayyana Fiye Da Kaso Uku Na Mutanen London Duk Yan Kasar Waje Ne , Wanda Ta na Da Kimanin Mutane Kazo Nazo Milyan Biyu Da Dubu Dari Tara Da Chasa'in Da Takwas Da Dari Biyu Da Sittin Da Hudu ( 2,998,264 million ).

KO KUNA SHA'AWAR ZUWA BIRNIN NA LONDON ?

Ahmad Quraishi

29/08/2021

Tabbas! wllh tausayi suke bani.
* Mace ta kasance Kullum tana gida, idanun iyayenta yana kanta. A haka zatayi fama da rashin # kudi babu mai bata, domin ita ba fita zatayi ta nema ba k**ar . Ya kakeji a ranka idan aka wayi gari bakada ko sisi na rana daya ? to a haka wata sai tayi wata a cikin wannan mawuyacin halin, kai kuma saurayinta ka kasa lura da hakan. idan kuma ta cire kunya ta tambayeka a matsayinka na wanda take tunanin zai iya rufa mata asiri a rywa, sai kaji wani yanata Korafi yana cewa "Wance Mayyar kudi ce, ta mayar dani sai kace nine Ubanta " Mtsss! kuji shirme*
A matsayinka na Namiji kuma a gurin Kanwarka, Sau nawa kata6a daukar Naira ( 100 ko 200 ) haka kawai ka baiwa kanwarka kace ta kashe ?
Ina mai shawartarmu mu akan mu dinga kyautatawa Kannenmu Mata, Domin ko nawa ka baiwa kanwarka komai kankantarsa ita mai yawane a gurinta zataji dadi sosai. **Amma a hakan ma wasu dayawa basuda yayyen ma wayyoo!
**Tabbas a Tunanina kuma a ganina, ba mayun kudi bane k**ar yanda wasu suke tunani, dolece ta sakasu hakan. Yak**ata muyi musu Uzuri kuma mu fahimcesu.
** Sannan Mace Tun tana karama Batada kuzari, ta yanda Qaninta Namiji zai iya sakata Kuka. Ta taso tafara girma idanuwa su dawo kanta, tun daga 'yan unguwa har iyayenta
**Sannan Mace ta k**a kanta ace girman kai
**Tayi Faran-faran ace batada kamun kai
**Tayi kwalliya ta fito tana kwarkwasa ace 'yar iska ce
** Ta Qiyi ace shegiya Qazama
Ya Salam! wai dame zasuji ne ?
** A huro musu wuta agida akan duk hankalinsu ya tashi, kullum burinsu shine su samu Miji nagari, wanda zai basu cikakkiyar kulawa, Amma ahaka mazan suzo su yaudaresu suci Amanarsu
** Sunyi auren k**ar sun huta amma sai wacce ta dace, kaga mace tana kokarin farantawa mijinta amma shi baya gani.
Kuyi hkri Mata, wata rana sai labari.
Ina Kaunarku mata, ina tausayinku kannena, yayyuna, kuma iyayena. ALLAH yayi muku Albarka.

Address

Zaria

Telephone

+2348067912214

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when BARKA DAYAU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category


Other Magazines in Zaria

Show All

You may also like