02/03/2025
TAFSEER NA RAMADAN RANA TA HUDU A ZARIYA!
Acigaba da gabatar da karatun Tafseer na Watan Ramadan da yan uwa Musulmai Almajiran Sheikh Zakzaky na garin Zariya keyi , yau Lahadi 2 gawatan Ramadan angabatar da zama na Hudu.
Kamar yadda aka tsara yau Lahadi na cikin ranaku da Za'ayi MUHADARA.
Farfesa Isa Hassan Mashelgaro shine yagabar da jawabi mai taken '' TSARABAN JANA'IZAR SIDI MAI NASARA.
tunda farko Farfesa Isa Hassan yataya yan uwa dasauran al umman Musulmai na sake ganin wannan watan mai Alfarma na Ramadan , inda yayi fata da addu'a na dacewa da dukkan rabo. Daya juya ga jawabin sa kuwa , ya godewa Allah dayasashi cikin wanda s**ayiwa Jagora (H) rakiya.
Yace katin gayyata guda uku akaba Jagora matsayin na Nigeria. Sai yazama Jagora daya haris daya sai shi kuma na uku da Jagora yayi masa izinin sutafi tare.
Farfesa yayi bayanin daki daki , yadda tafiyar ta kasance , harzuwa yadda akayi jana'izar da irin dunbin al umman das**a halarta . Yafadi Kasar Lebanon karamar kasace, mai yaruka daban daban kabilu daban daban , ga kiristoci , sannan ga Musulmai sunnah da shi'a.
Hakanan yayi bayanin yadda s**ayi fama da mutane daban daban daga kasashe suke tururuwa don suga Sheikh Zakzaky...
Yayi bayanin yadda s**aga karamci matuka , tun daga filin jirgi har zuwa masaukai , yace wasu wuraren ma ba'a masu bincike (checking)..
Ya misilta wannan jana'izar a matsayin gagarabadau , wanda ba'a taba ganin irin sa ba .Yace hatta kwamitoci sai da aka samar da kwamiti 11 , kowane kwamiti yanada mambobi dubu 20 kuma duka kwararu adukkan fagage wanda s**a sanya ido da lura gamida da tsari na yadda za'a gabatar da jana'izar.
Zatan makiya sun kashe Syd mai Nasara ne zatansu sunkawo Karshen yan gwagwarmaya sai abin yajuye ..
Ya karkare dacewa '' dukda kokarin makiya da munafukai na kawo cikas basu samu nasaraba anyi cikin nasara...
Bayan kammalawar na Farfesa , Sheikh Abdulhamid Bello yayi ta'aliki . Inda yafadi muhimman darassa da yakamata yan uwa su dauka. ..
Akarshe akayi addu'a aka salami jama'a.
2Ramadan 1446 /2-3-2025.